Illolin Istimna'i Da Yadda Mutum Zai Daina Istimna'i (Masturbation )

Gabatarwa:

Maganin istimna'i na gargajiya

Yau abin da zamu tattauna shi ne yin amfani da hannu don biyan bukatar sha'awa, abin da ake kira istimna'i (masturbation). Rubutun mu zai yi tsokaci akan waÉ—annan maudu'ai

  • Da farko, zamu tattauna ko istimna'i zai iya zama jaraba? Da kuma yadda yake da alaÆ™a da kallon fina-finan batsa.
  • Na biyu, zamu tattauna game da kimiyyar kwakwalwa da ke bayan wannan É—abi'ar ta istimna'i 
  • Na uku, zamu tattauna yadda masturbation yake tasiri a Æ™waÆ™walwa, tunani, damuwa, da lafiyar hankali.
  • Bayan haka, zamu koma a kan istimna'i da lafiyar jiki, kuma mu tattauna game da rashin Æ™arfin gaba lokacin jima'i (erectile dysfunction).
  • Zamu tattauna dangantakar istimna'i (masturbation) da sinadarin hormone na testosterone.
  • Zamu kuma tattauna yadda masturbation ke shafar rayuwar jima'i.
  • A Æ™arshe, zamu tattauna a kan hanyoyin da zaku daina wannan É—abi'a. 

Shin Istimna'i (Masturbation) Zai Iya Zama Jaraba?

Bari mu zurfafa, shin istimna'i ko masturbation zai iya zama jaraba kuma ta yaya yake da alaÆ™a da batsa? Zamu tsallaka kai tsaye cikin kimiyyar kwakwalwa idan muna so mu yiwa wannan maudu'i wadataccen bayani mai adalci. Hakika, amfani da hannu a kowane lokaci don biyan buÆ™atar sha'awa yana da alaÆ™a da jaraba.

Na san cewa yawancin matasa maza da mata suna so su ji cewa istimna'i ko masturbation ba shi da wani illa, ba ya shafar lafiyar kowa. Saboda mafiyawancin matasa a yanzu, maza har da mata su na daukar istimna'i ko masturbation a matsayin hanya mara illa don rage damuwa da samun gamsuwar sha'awa ba tare da yin jima'i ba.

Na ji wannan duka a gurin matasa, amma gaskiyar magana ita ce, idan an haÉ—a istimna'i , watau masturbation da kallon batsa ko tunanin batsa, ba ya da kyau ga lafiyar kwakwalwar mutum. Saboda hakan, zai shafi lafiyar hankali da na jiki, wanda har zai iya bayyana a rayuwar mutum.

Don haka, istimna'i (masturbation) na iya zama jaraba, kuma muna da masaniya cewa wasu mutane mata da maza su na fama da matsanancin yawan aikata istimna'i (masturbation) don biyan buÆ™atar sha'awa a kowane lokaci. 

Lokacin da wasu masana ke magana akan cewa istimna'i  ko masturbation ba shi da illa ko ma yana da amfani, ba su na magana ne akan mutanen da suka É—auki masturbation abin yi kullum ba, ma'ana mutane masu fama da jarabar masturbation, wanda su ne mafi yawan mutanen da ke aikata istimna'i. Masana su na magana ne a kan masu yin istimna'i (masturbation) jefi-jefi.

Kimiyyar Kwakwalwa Akan Istimna'i (Masturbation)

Za mu tattauna game da yadda kwakwalwa ke aiki yayin da mutum ke masturbation. Lokacin da kake matashi, ka fara kallon batsa da yin masturbation a cikin wannan yanayi da rayuwa take da wahala. Kana samu jin daɗi a kwakwalwarka ta hanyar kallon batsa da yin istimna'i (masturbation). Wannan ya sa ka ji daɗi na ɗan lokaci. Wannan jin daɗin yana ƙarfafa kwakwalwa don ta nemi wannan jin daɗin a duk lokacin da kake cikin damuwa.

Wannan yana haifar da yawaitar sinadarin dopamine a jinin mutum, wanda yake kawo jin daɗi sosai. Lokacin da wannan ya faru, kwakwalwar mutum tana koyan cewa hanya mafi sauƙi don gujewa matsaloli da samun gamsuwar sha'awa ita ce ta hanyar aikata istimna'i da kallon batsa. Wannan sinadarin dopamine yana sa ka ci gaba da komawa wannan ɗabi'ar ba tare da ka lura cewa tana dagula rayuwarka ba.

Lokacin da mutum yake cikin wannan hali, kwakwalwar sa tana jin cewa babu wani farin ciki a duniya da kuma jin daÉ—i da ya wuce wanda yake samu ta hanyar kallon batsa da aikata istimna'i. Don haka, sai mutum ya koma kallon batsa da masturbation don samun wannan jin daÉ—in, ba tare da la'akari da cewa wannan na ci gaba da haifar da matsala mai zurfi wajen tunanin sa da yadda yake gudanar da rayuwar sa ba.

Tasirin Istimna'i Akan Ƙwaƙwalwa

Idan kana yawan yin istimna'i, yana shafar gaɓoɓin ƙwaƙwalwa da ke kula da hankali, tunani da sarrafa kai. Saboda haka, yana haifar da rashin kaifin ƙwaƙwalwa, wahalar tunani da rashin nutsuwa. Ana ganin haka musamman idan mutum yana yawan aikata istimna'i akai-akai, saboda yana rage ikon kwakwalwa wajen aikin da ta saba yi da kyau.

Dangantakar Istimna'i Da Rashin Ƙarfin Gaba Lokacin Jima'i (Erectile Dysfunction)

Yin istimna'i tare da kallon batsa yana iya sa mutum ya kasa samun kuzari lokacin da yake tare da abokin jima'i. Wannan na faruwa ne saboda Æ™waÆ™walwar mai kallon batsa da aikata istimna'i tana buÆ™atar irin matsanancin kallo da ta saba da shi ta hanyar batsa da yin istimna'i kamin ya samu cikakkiyar motsawar sha'awa. Wannan na sa mutum ya kasa jin daÉ—i yayin jima'i da abokin tarayya idan bai yi abin da ya saba dashi ba. 

Wannan yana É—aya daga cikin dalilan da za ka ga mutum yana da aure amma yana kallon finafinan batsa ko yana aikata istimna'i. Wani ma idan bai yi haka ba ba zai ji sha'awar matar sa ba, balle har ya zo mata. Wani kuma ko yazo ga matarsa ba zai samu cikakkiyar motsawar sha'awa ba sai dole ya kunna finafinan batsa.

Su kuma mata masu aikata istimna'i suna da wahalar gamsarwa a lokacin jima'i, saboda sun saba da aikata istimna'i, kuma idan sun fara suna É—aukar lokaci mai tsawo suna yi har sai sun gama gamsuwa. Toh inda matsalar take shi ne, idan sunyi aure kuma mijin su baya iya É—aukar lokaci mai tsawo yana saduwa dasu kamar yadda suka saba a lokacin istimna'i, wannan yana haifar musu da rashin gamsuwa da fitina tsakanin ta da mijin.

Illolin Istimna'i na lafiya


Dangantakar Masturbation Da Sinadarin Testosterone

Bincike ya nuna cewa dakatar da yin istimna'i ko masturbation na iya ƙara yawan sinadarin hormone na testosterone a jiki. Wani bincike ya nuna cewa yawan testosterone ya ƙaru da kashi 146% a rana ta bakwai bayan mutum ya daina masturbation. Haka kuma, dakatar da wannan dabi'ar na iya taimakawa wajen inganta lafiyar jima'i da ƙarfin mazakuta.

Hanyoyin Daina Istimna'i 

Idan kana son daina yin istimna'i ko masturbation, abu na farko da zaka yi shi ne ka daina kallon batsa. Idan har ka daina kallon batsa, zaka ga cewa zaka iya rage wannan É—abi'ar cikin sauÆ™i. 

Amma muddin mutum yana kallon batsa ba ranar da zai daina wannan ɗabi'ar ta istimna'i, ko ya sha alwashin yin haka da ya kalli wannan batsar zai ji cewa, toh dole sai yayi istimna'i sannan zai samu sauƙin abin da yake ji.

Hakanan, ana so ka nemi hanyoyin da za ka rage damuwa da cike lokutan shagala ta hanyar yin abubuwan da kake so kamar wasanni ko ayyukan nishaÉ—i.

Shin Akwai Maganin Istimna'i Na Gargajiya Ko Na Asibiti?

Babu maganin istimna'i da za'a baka na turawa domin daina yin istimna'i ko masturbation, su ma masu maganin istimna'i na gargajiya yaudara É—ai ce ba komi ba. Shawara a nan itace kaji tsoron Allah, kamar yadda kasan cewa ba zaka iya aikata zina ba saboda zina haramun ce haka ma istimna'i haramun ne. 

Haka kuma kamar yadda kasan zina na da illoli, haka ma istimna'i yana da illoli har ma da illolin lafiya masu É—imbin yawa. Akwai hanyoyi da dama da zaka bi domin controlling sha'awar ka, kamar;

  1. Yawaita yin azumi
  2. Tsare idanun ka daga kallon mata, batsa ko duk wani haramun, mafi yawancin masu aikata istimna'i ko masturbation suna aikata shi tare da kallon finafinan batsa, toh dole gaskiya sai ka daina kallon batsa ko wace iri.
  3. Nisantar duk wata macen da ba muharramar ka ba, ko namijin da ba muharramin ki ba.
  4. Yawaita karatun Alkur'ani da kuma zikirori.
  5. Kiyaye sallolin ka duk a cikin lokacin su.
  6. Ka daina zama a É—aki kai kaÉ—ai, saboda hakan yana iya sa sheÉ—an ya turaka zuwa yin istimna'i.
  7. Ka nemi wani aikin da zai sanya ka zama busy, kamar karatu ko maida hankalinka akan wata sana'a.

Post a Comment

0 Comments