Yadda ake Kula da Gaban Mace Bayan Haihuwa: Abubuwan da Kowace Mai Jego Ya Kamata Ta Sani

Gabatarwa

Haihuwa wani muhimmin abu ne a rayuwar kowace mace. Sanin yadda ake kula da gaban mace bayan haihuwa abu ne mai matukar muhimmanci, saboda bayan mace ta haihu, jikinta yana bukatar kulawa ta musamman domin dawo da martabar jikin da kuma karfin da ta rasa, musamman yankin gabanta (farji da perineum).

Yankin Perineum wani É—an sarari (space) ne da ke tsakanin kofar farjin mace da duburar ta. Wannan shi ne Ć™aramin tazara da ke raba Ć™ofar farji da Ć™ofar duburar mace. 

Yadda ake kula da gaban mace bayan haihuwa

Wannan yankin yana taka muhimmiyar rawa yayin haihuwa, saboda shi ke samun matsin lamba, raunuka da tsagewa a lokacin fitowar jariri, don haka yana bukatar tsaftacewa, kariya, da kulawa yadda ya kamata.

Rubutu Mai Alaka: Budewar Gaban Mace Da Kuma Yadda Yake Samun Kari Yayin Haihuwa

A cikin wannan rubutun, za mu tattauna dalla-dalla yadda ake kula da gaban mace bayan haihuwa, abin da ya kamata a guje masa, da hanyoyin taimakawa wajen murmurewa da kare mace kamuwa da cututtuka. 

Wannan rubutu zai taimaka wa kowace mace da ta haihu ko masu shirin haihuwa su san yadda za su kula da lafiyarsu ta gaba bayan haihuwa (private part health after delivery).

Me Yasa Sanin Yadda Ake Kula Da Gaban Mace Bayan Haihuwa Ya Ke Da Muhimmanci?

Bayan haihuwa, musamman idan mace ta haihu ta hanyar farji (vaginal delivery), yankin perineum (tsakanin farji da dubura) yana iya fuskantar wasu sauye-sauye na halitta. Wasu daga cikin sauye-sauyen ba matsala ba ne, yayin da wasu kuma na iya zama alamun matsala da ke bukatar kulawa. Sauye sauyen da ba matsala bane sun hada da:

  • Zai iya yiwuwa yankin ya dan kumbura, ya yi ja, ko kuma yana yi miki ciwo.
  • Idan an yanka wajen a lokacin haihuwa (episiotomy) ko kin samu Ć™ari, jami’an lafiya zasu yi miki dinki.
  • Jijiyoyin wajen na iya É—aukar lokaci kafin su dawo daidai, wannan zai sa yankin yin jaa da kumburi.
  • Zaki iya jin rashin jin dadi yayin zama ko tafiya ko tsuguno — musamman a kwanaki na farko-farko bayan haihuwa.
  • Zaki iya jin Ć™aiĆ™ayi yayin da dinkin ke kokarin warkewa.

Hanyoyin Kula da Gaban Mace Bayan Haihuwa 

Gaban mace yawanci yana fara warkewa cikin mako 1 zuwa 2, amma cikakkiyar warkewa na iya É—aukar makonni 6 ko fiye da haka, gwargwadon irin raunin da mace ta samu. Kulawa da wannan yanki yana taimakawa wajen:

  • Rage zafi da kumburi.
  • Hana kamuwa da cututtuka.
  • Hanzarta warkar da raunuka.
  • Kare lafiyar gabanta gaba É—aya.
  • Inganta jin daÉ—in jima’i a nan gaba.

1. Kula da Tsabtace Gaban Mace Bayan Haihuwa

Tsabta ita ce ginshiƙin farko a kulawar mace bayan haihuwa. Mace mai jinin bayan haihuwa (lochia) na bukatar kulawa sosai domin hana kamuwa da cutar infection na farji ko warin gaba. Hanyoyin tsabtace gaban mace bayan haihuwa sun hada da:

  • A rika wanke gaba da ruwa mai tsabta da ruwan dumi akai-akai, musamman bayan gama bayan gida.
  • A guji amfani da sabulu mai Ć™amshi ko sinadarai masu Ć™arfi domin suna iya haifar da Ć™aiĆ™ayi ko Ć™onewa a gaban mace.
  • A yi amfani da tissue mai laushi ko tawul mai tsabta wajen goge wurin daga gaba zuwa baya (ba daga baya zuwa gaba ba), don kauce wa yada Ć™wayoyin cuta daga dubura zuwa farji.
  • A canza pad ko zanin tariyar jini sau da yawa — aĆ™alla kowane awa 3–4.
  • Kada a yi amfani da tampon ko duk wani abu da za a saka cikin farji har sai an nemi shawarar likita.

2. Yadda Ake Rage Zafi da Kumburi a Gaban Mace Bayan Haihuwa 

Bayan haihuwa, yawanci mace tana jin zafi, ƙaiƙayi, ko kumburi a gabanta, musamman idan an yi mata dinki (episiotomy). Abubuwan da zasu taimaka a irin wannan yanayi sun haɗa da:

Sanya Ć™anĆ™arar ruwan sanyi (ice pack) a cikin kyalle sannan a dan sa a yankin na mintuna 10–15 domin rage kumburi.

Rubutu Mai Muhimmanci: Maganin Matsi Na Asibiti: Tiyatar Tsukewar Gaban Mace 

Yin zama a cikin ruwa mai dumi (sitz bath) sau biyu a rana yana taimakawa wajen rage ciwo da kara saurin warkewa.

Guji zama na dogon lokaci a wuri daya – a tsaya, a yi motsi kadan kadan.

Zama akan matashi: Ki dinga zama a kan matashi ko filo mai laushi domin rage matsin lamba da ciwo a wajen.

Guji saka fatari (pant) mai matse jiki sosai, sai a yi amfani da fatari mai laushi da iska ke shiga.

Ki samu isasshen hutu kuma ki guji É—aukar kaya masu nauyi. Kada ki dinga tsayuwa na dogon lokaci.

Rubutu Mai Muhimmanci: Bayani Game Da Zubar Jini Dayawa Bayan Haihuwa 

3. Abinci da abubuwan sha da ke taimakawa gaban mace saurin warkewa

Abinci mai kyau yana taka babbar rawa wajen saurin murmurewar jikin mace bayan haihuwa. Kalar abinci da ake ba da shawarar ci sun hada da:

  • Abinci mai gina jiki kamar kifi, naman sa, kwai, madara, da wake.
  • ’Ya’yan itatuwa da kayan marmari masu sinadarai na vitamin C don taimakawa wajen gyaran fata da raunuka.
  • Ruwa mai yawa, domin taimakawa wajen fitsari mai laushi da hana kwayoyin cuta kama mafitsari.
  • Zuma da nono ko kunun aya don karfafa jiki da samar da isasshen madara.

4. Yin Aiki da Atisayen Kegel (Kegel Exercise)

Kegel exercise wata hanya ce ta motsa tsokokin da ke rike da farji da mafitsara domin su dawo da ƙarfin su bayan haihuwa. Yadda ake yin Kegel exercise shi ne:
  • Ki zauna ko ki kwanta cikin natsuwa.
  • Ki matse tsokar da ke hana fitsari ya fito na daĆ™iĆ™a 5–10 (zaki matse jikin ki kamar kina yin fitsari, amma kinason ki tsayar da fitsarin kamin ki gama).
  • Ki sake jikin ki bayan daĆ™iĆ™u 5-10
  • Ki maimaita haka sau 10 zuwa 15 
  • Shikenan kin gama kegel exercise 
  • Ana so kiyi wannan aĆ™alla sau uku a rana.
Kegel exercise na taimakawa wajen:

Hana fitsari ya zubo ba tare da niyya ba (urinary incontinence).
Inganta jin daÉ—in jima’i bayan haihuwa.
Dawo da ƙarfin gaban mace.

Lokacin Da Ya Kamata Aga Likita

Koda mace na yin duk wadannan matakai, akwai lokuta da ya zama dole ta ga likita.

Ki garzaya asibiti, ki gaggauta tuntubar likita idan kika lura da É—aya daga cikin waÉ—annan alamomin:
  1. Kin ga zubar jini mai yawa ko jini ya tsaya daga baya sai ya sake fitowa sosai.
  2. Idan ciwon wajen yana ƙaruwa maimakon raguwa.
  3. Idan wajen yana wari ko kina ganin É—igon kurji, ko fitar ruwa mai warin gaske.
  4. Kumburin wajen ya tsananta ko ya yi ja sosai fiye da da.
  5. Jin zazzabi, kasala ko sanyi a jiki.
  6. Idan kina zubar da jini mai yawa — har pad É—in ki ya jike Ć™asa da awa É—aya.
  7. Dinkin wajen ya kumbura ko yana wari.
  8. Dinkin ya buÉ—e.
  9. Wahalar yin fitsari ko bayan gida
  10. Rashin iya riĆ™e fitsari da kyau ko yoyon fitsari 
Likita zai duba ko akwai cututtukan infection, rauni ko tsagewar perineum, ko matsalar episiotomy domin a ba ki magani yadda ya dace.

Ku Karanta: Fitar Farin Ruwa Mai Kauri Daga Gaban Mace Mai Ciki 

Abubuwan Da Ya Kamata A Guje Musu Bayan Haihuwa

Kada a yi saurin fara yin jima’i sai bayan aĆ™alla makonni 6 ko likita ya tabbatar da wurin ya warke sarai.

A guji wanke farji da sinadarai ko sabulu mai ƙamshi, domin yana iya lalata ƙwayoyin bakteriya masu kariya a ciki.

Guji tura magunguna ko ganyayyaki a farji, domin wasu na iya jawo ƙaiƙayi ko infection.

Guji nauyi ko motsi mai yawa cikin kwanaki na farko bayan haihuwa.

Shawarwari na Musamman ga Mata Masu Dinki Wajen  Haihuwa (Episiotomy Care)

Idan an yi miki dinki bayan haihuwa:
  1. A tabbatar ana gashi (sitz bath) sau biyu zuwa sau uku a rana.
  2. A ci abinci mai sauƙin narkewa don guje wa jinkirin bayan gida (constipation).
  3. A yi amfani da maganin da likita ya rubuta kawai, kada a ƙara wani.
  4. Idan wurin ya kumbura ko yana zubar da ruwa, a tafi asibiti nan da nan.

Tambayoyi da Amsoshi (FAQ Section)

Q1: Yaushe mace zata iya komawa yin jima’i bayan haihuwa?

A: Ana ba da shawarar mace ta jira akalla makonni 6 bayan haihuwa kafin yin jima’i, sai idan likita ya tabbatar da cewa wurin ya warke gaba É—aya.

Q2: Shin yana da kyau mace ta wanke farji da sabulu mai ƙamshi bayan haihuwa?

A: A’a. Sabulu mai Ć™amshi yana iya lalata sinadarin kariya na cikin farji, wanda zai iya jawo Ć™aiĆ™ayi da infection.

Q3: Me yasa gabana yake da laushi ko sanyi bayan haihuwa?

A: Wannan yana da alaka da canjin hormone (estrogen) bayan haihuwa, wanda ke rage danshi da laushi na fata. Ana iya amfani da lubricant lokacin jima’i idan an fara.

Q4: Yaya zan hana kamuwa da infection bayan haihuwa?

A: Ki kula da tsafta, ki canza pad akai-akai, ki guji amfani da sabulu mai ƙamshi, kuma ki sha ruwa mai yawa.

Kammalawa

Kulawa da gaban mace bayan haihuwa ba kawai don jin daÉ—i ba ne, amma don kare lafiyar jiki gaba É—aya. Tsabtacewa, cin abinci mai gina jiki, yin atisaye kamar Kegel exercise, da bin shawarwarin likita suna taimakawa mace ta dawo da lafiyarta cikin kankanin lokaci. Mace mai kula da kanta bayan haihuwa tana kare lafiyarta, jin daÉ—inta, da kuma ingancin rayuwar iyalinta.

No comments: