Tambaya
SalamDr. Barka da warahaka1. Dan Allah Dr. Mike saka idan mace ta haehu Ruwan nono ya Kae kwana 2 zuwa 3 bae kawo? Sannan ya ake magani hakan?2. Miya ya kamata abaewa yaron kafin Ruwan nono ya kawo?3. Wane lokaci yafi dacewa ayi family planing idan mace ta haehu?
Amsa
Jinkirin zuwan ruwan nono musamman a haihuwar fari, ba baƙon matsala bane, mafi yawancin mata suna samun haka a haihuwar fari. Jinkirin yana faruwa ne saboda normally nono baya samar da madara sai da dalilin shayar wa. Shi yasa tun a lokacin da mace ta ɗauki ciki, hauhawar sinadaran wasu hormones sukan fara shirya nononta zuwa ga samar da madara da kuma shayar wa, za ta fara ganin wasu canje-canje a nononta tun farkon samun ciki har zuwa haihuwa.Ku Karanta: Amfanin Shayar Da Jariri Ruwan Nono Zallah Har Na Tsawon Wata Shida
- Rashin fitowar kan nono bayan haihuwa
- Rashin zuwan madarar nono
Rubutu Mai Alaka: Matsalolin Shan Nono Ga Jariri Yayin Da Mahaifiya Ke Kwance
Rubutu Mai Alaka: Bayani Game Da Ruwan Nono Mai Maiƙo Ga Mai Shayarwa
Ku karanta: Fitar Ruwan Nono Ga Mace Ba Tare Da Ciki Ko Shayarwa Ba (Galactorrhea)
Kamin mace ta samu wadataccen ruwan nono ba za'a bar yaro haka kawai yana kuka ba, za'a dora shi akan madarar jarirai da ake kira BMS (Breast Milk Supplement), wadannan su za'a baiwa jariri duk bayan awa 2 har zuwa lokacin da uwa take iya samar da wadataccen ruwan nono.
Tsaraba: Yadda Jarirai Ke Shan Nono Har Na Tsawon Watanni Shida
A asibiti ana sa mace ta fara family planning sati 6 bayan haihuwa. Wannan shi ne mafi ƙarancin lokacin da mace zata dauka kamin normal cycle dinta ya dawo bayan ta haihu yadda zata iya samun wani ciki. Wasu matan sukan iya ɗaukar har tsawon wata 6 normal cycle dinsu bai dawo ba, kuma a irin wannan lokacin bazasu iya samun ciki ba, amma wannan bayada guarantee. Saboda haka the earlier the better.
No comments:
Post a Comment