Dangantakar Sakin Ƙwan Haihuwa Na Mata (Yin Ovulation) Da Jinin Al'ada

Dan Allah mene gaskiyar cewa Wai mace idan bata al'ada duk wata bata sakin kwai. 

Yadda ake gane ovulation

 Amsa

Wannan gaskiya ne, duk watan da mace ta tsallake ba tayi al'ada ba, toh, lallai wannan watan bata yi ovulation ba. Yin al'ada yana faruwa ne a lokacin da mace ta gama ovulation har ƙwan ya mutu bai samu ya haɗu da sperm ba. 

Toh daga zarar ƙwan ya mutu, sinadaran hormones ɗin da yake samar wa zasu yi ƙaranci, bayan haka ya faru, mahaifa za ta cire ranta da samun ciki a wannan wata, wannan zai sa duk wani shiri da mahaifa tayi domin samun ciki a wannan wata zai wanke ya fito a matsayin jinin al'ada.

Don haka, a duk watan da mace tayi ovulation toh dole za tayi al'ada a wannan watan, sai dai kuma in ta samu saduwa da namiji kuma ta dace maniyyin sa ya haɗu da ƙwan da ta saki, toh a nan ba za ta yi al'ada ba, za ta ɗauki ciki.

Rashin yin al'ada a duk wata, mafiyawanci yana faruwa ne sakamakon cutar polycystic ovarian syndrome. Munyi bayani akan wannan cuta a cikin wannan rubutun "Cututtukan da ke sanya mata gashin fuska, rikicin al'ada da kuma rashin yin ovulation".

Post a Comment

0 Comments