Tambaya
SLM meke kawo zubewar ciki INA da yaro mai wata 15 zan iya yaye shi sabo da na samu wani ciki. Sann Don Allah mene ne maganin ciwon nono da ke zuwa bayan yaye yaro daga shan nono.
Amsa
Abubuwan da ke iya kawo zubewar ciki basuda adadi. Ko a asibiti sai da bincike za'a gane, mene ne ainihin ya kawo zubewar ciki.
Ba matsala ki yaye yaron idan har kin samar masa da wani abinci mai gina jiki da zai maye masa gurbi kuma kin tabbatar yaron zai iya cigaba da chi da sha har ya ƙoshi. In kuma baki iya samar masa da abincin mai gina jiki da zai maye masa gurbi da zai isheshi. To wajibi ne ki cigaba da shayar da shi yadda ya kamata har sai yakai lokacin da zai iya chin komai, in ba haka ba tamowa zata iya sallama masa.
Akwai wani chanfi da ake cewa idan mace ta cigaba da shayar da yaronta lokacin da take da ciki, toh yaron da aka shayar zai tashi wawa ko marar wayau. Wannan magana ce marar toshe, irin ta mutanen dori, batada wani inganci.
Duk da haka, madarar nono takan iya samun wasu chanje-chanje bayan mace ta samu ciki sakamakon hauhawar sinadaran hormones na mata da samun ciki yake kawowa, amma cigaba da shayar da yaro da ciki ba ya haifar da wata matsala ta lafiya ga yaro ko ga uwar ko ga cikin.
A lura cewa, yara masu shan mama suna gane chanje-chanjen da madarar nono ke samu yayin da uwarsu ta samu ciki, shi yasa wasu yara zasu daina karbar mama, da kuma fara kukan yunwa idan mamar su ta samu ciki. Wannan shi yasa wasu ke ganin yaye yafi idan za'a iya samar da ingantaccen abinci, idan kuwa ba'a iya samarwa yaron ingantaccen abinci to acigaba da shayar dashi yafi.
Ciwon nono bayan yaye ba cuta ba ce ko wani babban matsala, yana faruwa ne daga zarar mace ta yaye yaron ta saboda samar da madarar da nonon ke yi kuma babu yaron da zai sha. Wannan yakan sa madarar ta taru ta cika nonon ya bunƙasa sosai ya kama ciwo.
Gaskiya al'amari ne ma ciwon gaske, amma yakan daina cikin yan kwanaki kadan bayan yaye, saboda nonon zai daina samar da madarar tunda babu yaron da zai sha. Sai dai idan har ya dade bai daina ba ko kuma mace ta kasa jurewa ana bada maganin da zai hana nonon samar da madara.
Tabs Bromocriptine 5mg dly x 5/7.
Print this post
0 Comments