Ad Code

Ticker

6/recent/ticker-posts

Bayani Game Da Ƙurajen Cutar Ƙaranbau

Gabatarwa

Ƙurajen Karinbau

Ƙaranbau cuta ce mai saurin yaɗuwa wadda ƙwayar cutar virus ta varicella-zoster (VZV) ke haifar wa. A turance ana kiran cutar karinbau da cutar Varicella ko kuma Chickenpox. Cutar karinbau na yaɗuwa ne tsakanin mutane ta hanyar shaƙar gurɓataccen iskar da mai cutar ke fitarwa ko kuma ta hanyar cuɗanyar jiki. Wannan cutar ta fi addabar yara ƙanana amma har manya ma suna iya kamuwa.

Alamomin Karinbau

Karinbau ba cuta ce wadda ke yin illah kai tsaye ga wanda ta kama ba, sai dai idan ba'a an dade ba'a ɗauki matakin da ya dace ba. Karanbau na iya zama mai tsanani, musamman a jarirai, matasa, manya, mata masu juna biyu, da kuma mutanen da garkuwar jikinsu ta yi ƙasa. Manyan alamomin cutar karinbau sun haɗa da:

  1. Zazzabi ko masassara (Jiki kan iya zafi sosai)
  2. Rashin jindadin jiki
  3. Rashin cin abinci 
  4. Kasala da rashin karfin jiki
  5. Ciwon kai
  6. Karinbau yana haifar da ƙaiƙayin jiki
  7. Ƙuraje
  8. Kananan yara sukan samu rashin walwala da kuma kukan banza
  9. Ƙaiƙayin jiki mai hana bacci.

Ƙurajen Karinbau 

Kurajen karinbau suna fitowa kamar kananan ƙolalai, bororo ko borin jini a jikin wanda ya kamu da cutar. Kurajen na iya fara bayyana akan ƙirji, baya, da fuska, sa'an nan kuma su bazu a dukkanin jiki, gami da cikin baki, fatar ido, ko yankin al'aura. Suna haifar da bororo tsakanin 250 zuwa 500. Haka zalika ƙurajen karinbau bau suna da matuƙar ƙaiƙayi.

Ƙuraje masu ƙaiƙayi da kamuwa da cutar karanbau ke haifarwa suna bayyana kwanaki 10 zuwa 21 bayan kamuwa da cutar kuma yawanci suna ɗaukar kwanaki 5 zuwa 10 sannan su fara ɓacewa.

Da zarar kurjin ƙaranbau ya bayyana, yana tafiya a matakai uku: Ƙunƙarar ruwan hoda ko ja (papules), wanda ke fitowa cikin kwanaki da yawa sananan su zama bororo masu cike da ruwa (vesicles), waɗanda ke fitowa nan da kwana ɗaya sannan su karye su zama bawo da bambaroki, waɗanda ke rufe bororo da suka karye kuma suna ɗaukar ƙarin kwanaki don warkewa.

Yadda Ake Maganin Ƙurajen Karinbau 

Abu na farko da ya kamata ayi idan yaro ya fara nuna alamomin cutar karinbau shi ne a kai shi a asibiti domin tabbatar wa, sannan a tsare yaro gida tare da hanashi cudanya da sauran yara domin rage yaɗuwar cutar. 

Yadda ake maganin cutar karinbau ya danganta da irin alamomin da ta sakawa mutum. Ana bada magungunan rage zazzaɓi, ciwon kai, ƙaiƙayi da kuma creams masu maganin ƙuraje.

Idan har cutar ta yi tsanani akwai magungunan antivirals da ake iya amfani dasu.

Yadda Ake Kariya Daga Kamuwa Da Cutar Ƙurajen Karinbau 

1. Matakin farko na kariya da wannan cutar shi ne tabbatar da yaro ya samu alluran riga-kafin da ake yi tun daga haihuwa har na tsawon shekaru biyu. Waɗannan alluran riga-kafi suna inganta garkuwar jiki da hana yara da manya kamuwa da ƙananan cututtuka. Yaron da ke da cikakken alluran riga-kafi yana da wahala ya kamu da irin wannan cutar, ko ya kamu ba zata yi tsanani ba.

2. Rage cudanya cikin mutane da kuma tsare wanda ya kamu da cutar sai ya warke.

3. Yaro ko babba mai ɗauke da cutar anaso ya kama amfani da takunkumin baki da hanci a koyaushe domin kare makusantan sa da kamuwa.

4. Kange yaron da ya kamu daga zuwa makaranta ko wuraren wasan yara.

5. Anayin cutar karinbau bau ne sau ɗaya a rayuwa. Wanda ya kamu da cutar ya warke zai samu ƙarfin garkuwar jikin da zai bashi damar faɗa da cutar, haka zai sa ba zai sake kamuwa da cutar ba.

Print this post

Post a Comment

0 Comments