Assalamu Alaikum tareda Fatar Antashi Lpy Doctor.
Don Allah minene Mai Fama da Matsalar fitar bayan Gida yadace Yarinka Amfani Dashi Domin Samun saukin fitarsa batareda wahala ba.
Kuma miyakesa Wani Lokaci idan Mutum yajin bayan Gida Sai shikama jin kamar Zai biyo ta makoshinsa yafito baki ?
Sannan Don Allah wane Irin shawarwari Zakaba Masu Fama da Wannan Matsalar. Sannan Miyake Haifarda Wayannan Abubuwan ?
*Nagode*
Amsa
Matsalar wahalar fitar bayan gida yana samo asali ne mostly sakamakon irin abincin da mutum yake chi sa kuma matsalar dankanoma mai tsiro.
Domin samun saukin fitar bayan gida dole mutum ya dinga chin abinci mai ɗauke da sinadarin fiber da kuma ya'yan itace. An bukatar mutum ya dinga shan lemun ɓawo da kankana da ayba a kullum idan akwai hali domin sauƙin yin bayan gida, saboda wadannan abubuwa na lausasa bayan gida.
Mutum ya daina barin bayan gida a cikin sa, a lokacin da duk yaji shi, to ya tabbatar da yaje yayi shi. Saboda a duk lokacin da bayan gida ya jima a cikin ciki to hanji zai cigaba da tsotse ruwan bayan gidan sai yasa yayi ƙarfi wanda hakan zai sa yayi wahalar fita.
Dole mai fama da wannan lalurar ya kauracewa wasu kalolin abinci da basu da sinadaran fiber kamar garin kwaki da dankalin hausawa, saboda wadannan suna sanya bayan gidan mutum yayi ƙarfi.
Haka zalika ana bukatar mai wannan lalurar ya yawaita shan ruwa domin ƙara lausasa bayan gidan shi.
0 Comments