Aslm barkanmu da safiya pls tambayace Dani. Shin mace zata iya daukar ciki da datti a mararta kokuma sai Ammata wanki ciki kokuma maganin gargajiya zata sha na flushing.
Ba wani datti a mara mai hanawa mace daukar ciki. Shin idan ma ance dattin mara, me ake nufi da dattin mara? Mara shi dake cikin ciki yana yin datti ne?
Amsa
Maganar gaskiya ba wani datti dake shiga a cikin mara, hasalima duka alauran mata, tun daga mahaifa har zuwa waje yana wanke kanshi da kanshi. Ba'a bukatar amfani da sabulu, turare ko wani abun flushing domin wankewa.
Mafi akasari infection ne ke damun wasu matan wanda ke sanya su fitar da wani datti ko discharge kala daban daban, wasu masu wari da ƙarni. Wannan shi ke sa wasu mata suna ganin kamar marar su ne ke da datti. Kuma irin waɗannan infections suna iya hanawa mace samun ciki da kuma rikita mata al'ada. Amma idan an je asibiti anyi maganin infection din toh komai zai koma norma kuma mace za ta iya samun ciki.
Haka zalika maza, wasu suna fama da cututtukan magudanan fitsari, ko cutar sanyin gonorrhea ko sanyin clamydia, sai suzo suna fitsari mai kauri, watarana kamar madara, ko kuma su kama ganin farin ruwa nayi musu zuba bayan sun kammala fitsari. Wannan duk sharrin infections ne da kuma wadannan cututtukan dana ambata amma ba dattin mara ba. Shin da wane dalili ma namiji zai yi dattin mara?
A lura cewa wankin marar da ake yi a asibiti ba ana yin shi ne akan dattin mara ba, ana yin shi ne akan dattin mara ba, ana yin sa ne a lokacin da hoton ultrasound ya tabbatar da cewa akwai wani abu a cikin mahaifar mace. Misali;
1. Macen da ta samu ɓarin ciki amma sauran ciki ya maƙale bai zube a baki daya ba.
2. Macen da ta haihu amma wani abu ya makale a cikin mahaifa.
3. Macen da ta samu cikin da yayi kwancii
4. Cikin da ya rasu kamin yakai watanni uku.
0 Comments