Maganin Girman Nono Na Budurwa Idan Ɗaya Yafi Ɗaya Girma

 Assalamu Alaikum 'yan uwa dafatar kowa yana lafiya, ya fama da tsadar rayuwa Allah ubangiji ya sassauta mana yasa mudace, ameen.

Dan Allah inada tambaya ne shin akwai wanda suka yi experiencing lokacin yaye mama daya yafi daya? Dan Allah me ke kawo haka kuma mene ne mafita shin zai daidaita ko a haka zai zauna? Nagode. 

Maganin girman nono


Amsa

Mene ne Girman Nono Ɗaya Yafi Ɗaya (Anisomastia)?

Girman nono ɗaya yafi ɗaya ana kiran sa "anisomastia" a likitance. A turance kuwa ana kiran sa "breast asymmetry". Yanayi ne wanda yakan sanya nono ɗaya yafi ɗaya girma (unequal breast size), ko siffar nono ɗaya ta bambanta da ɗaya (different breast shape), ko mazaunin nono ɗaya ya bambanta da ɗaya (different breast position). 

Rashin daidaito a girman nono anfi ganinsa a jikin mata saboda su ne halittar nonon su take yin girma. Amma ana samun kaɗan daga cikin maza masu wannan yanayin. 

Asali Allah Subhanahu wata'ala ya kaddara cewa nonon mace ɗaya yana fin ɗaya girma, saidai ba'a cika ganewa ba domin bambancin ba shi da yawa. Kuma mafi yawanci nonon hagu ne yakan fi girman, duk da cewa ana samu kadan daga cikin mata wadanda nonon su na dama shine yafi na hagu girma. 

Wannan yana nufin cewa a mafi yawan lokuta girman nono ɗaya yafi ɗaya ba matsala bane, abinda aka sani ne. Saidai idan bambancin yayi yawa, to, yana taba ƙwarjinin mace (self-esteem) ta yadda ba za ta so ko 'yan-uwanta mata su gani ba, sai idan ya zama dole.

Rabe-Raben Girman Nono Ɗaya Yafi Ɗaya (Types Of Breast Asymmetry)

Yanayin bambancin girman nono daya yafi daya ya rabu kamar haka:

1. Bambancin girman nono a lokacin kuruciya (developmental asymmetry)

Wannan yana faruwa ne ga yan mata budare a lokacin da nonon su ya fara girma, sai aga bambanci sosai a nonuwan ta fuskar girma (size), ko siffa (shape), ko mazauni (position). Hakan halitta ne ba wata rashin lafiya take haddasa shi ba.

2. Bambancin girman nono sakamakon sauye-sauyen zubar ruwan sinadarai a cikin jini (hormonal asymmetry)

Wannan yana faruwa ne a lokacin al'ada (menstruation), ko sake ƙwan haihuwa (ovulation), ko juna biyu (pregnancy), ko shayarwa (breastfeeding), ko yaye (weaning), ko ɗaukewar al'ada (menopause). A wannan lokacin, nono daya zai iya rike ruwa fiye da daya, don haka sai girman su ya bambanta.

3. Bambancin girman nono sakamakon rauni (traumatic asymmetry)

Wannan yana faruwa ne idan mace ta sami rauni ko bugewa a nono (trauma), ko akayi mata tiyata a nono (surgery), ko akayi mata aikin kara girman nono (breast implants).

4. Bambancin girman nono sakamakon gado (congenital asymmetry): 

Wasu matan sukan tashi da nonuwa masu bambancin girma saboda sunyi gado ne daga iyaye ko kakanni.

5. Bambancin girman nono sakamakon yadda mace take gudanar da rayuwarta (postural or lifestyle asymmetry)

Wannan ya shafi yadda mace take tafiyar da rayuwarta, kamar kwanciya ruf-da-ciki akan nono daya (lopsided sleeping on breast), ko sanya matsattsiyar rigar nono (wearing of tight fitting brezia), daukar kaya mai nauyi a kan kafada guda (heavy load carrying on one shoulder), ko yin ayyukan motsa jiki da hannu daya (one-handed physical exercises).

Maganin girman nono

A duk cikin wadannan da muka ambata, bambancin girman nonon da akafi samun sa a cikin matan mu a yau shi ne wanda shayarwa ko kuma yaye suke haddasawa.

A lokacin shayarwa, bambancin girman nono yana faruwa ne sakamakon taruwar ruwan nono a bangare daya fiye da daya, musamman idan mace tafi yin shayarwa da nono daya. To, wanda tafi shayarwa dashi, shine yake yin girma.

A lokacin yaye kuma, nonuwan zasu rage girma sakamakon ɗaukewar ruwan nono, don haka zasu koma girman su na asali. Toh, idan dama mace can tana da yanayin girman nono daya yafi daya, yanayin zai iya bayyana ƙarara. 

Idan hakan ya faru, to, mawuyaci ne a iya daidaita su. Amma idan mace ta sake haihuwa, sai tayi kokarin daidaita su ta hanyar yin shayarwa da karamin nonon fiye da mai girman. Wannan zai sanya shi ma ƙaramin nonon ya ciko. Daga nan sai ta daidaita shayarwar.

Idan kuwa bambancin girman nonon ya faru ne saboda wasu dalilai na daban, to, hanyar magance shi ya danganta da abinda ya haifar dashi. Ma'ana, mai yiwuwa ne sai anyi tiyata, ko shan magani, ko yawaita motsawar nono wajen mu'amala, ko yin atisaye.

Bambancin Girman Nono Ɗaya Yafi Ɗaya Ga Maza (Breast Asymmetry In Men)

Wannan yanayin zai iya faruwa ga maza, duk da kasancewar ba'a cika samun sa ba.

Abubuwan da suke haddasa shi su ne sauye-sauyen zubar ruwan sinadarai a cikin jiki (hormonal changes), ƙiba (obesity), cuta gynecomastia wacce take haifar da girman nono ga maza, da dai sauransu. Magance shi ya danganta da abinda ya haddasa shi.

Post a Comment

0 Comments