"Aslm dan allah doctor ni budurwa ce nake fama da ciwan nono. Yanzu shekara ta 20 tun farkon halittar fitowar mama a jikina yake mun ciwo kana nonon idan aka bugeni a tsakiyar bayana nake jin zafin".
Amsa
Ciwon nono ga budurwa ko 'yan-mata masu kananan shekaru yawanci baya nuna cewa suna da wata babbar matsala a nonon su. Yakan zamo yana da alaƙa ne da canje-canjen hauhawar sinadaran mata watau estrogen da progesterone a cikin jininsu (hormonal imbalances).
Wadannan sinadaran suna shafar balaga, jinin haila, ko girman nonon mace. Yawancin yan mata matasa ko budurwa tana jin ciwon nono ko zafin nono ko rashin jin daÉ—i a matsayin wani É“angare na tsarin girman halittar jikinta.
Ana kiran wannan da ciwon nono na lokaci-lokaci (cyclical breast pain), kuma yawanci wannan ciwon nono yana warkar da kansa bayan wani lokaci, ko kuma mace taji sauƙin sa bayan ta sami sauyin rayuwa idan tayi aure.
Amma, idan ciwon nono ya zamo mai tsanani kuma bai daina ba na tsawon lokaci, ko ya hadu da kumburin nono ko wasu canje-canje marasa kyau a nono, ko nono guda daya ya shafa na tsawon lokaci, ko ba yana faruwa bane a lokacin jinin al'ada, to, ya kamata mace taje asibiti domin likita ya duba ta domin tabbatar da abin da ke damun ta.
Sa'annan kuma, ya kamata ki san cewa ciwon nono a daidai shekarun ki na yanzu, zai iya zamowa sakamakon abubuwa ne kamar haka:
1. Sauye-sauyen zubar ruwan sinadaran estrogen da progesterone a cikin jikin ki (hormonal changes), kuma shine ake kira "cyclical mastalgia". Wannan ba matsala bane In-sha-Allah.
2. Budewar fatar kirjin ki, da kuma habakar girman tsokar nonon ki (developmental stretching of skin and tissues as the breasts grow).
3. Tasirantuwar fata da tsokar nonon ki idan aka taba su (breast sensitivity), domin wasu matan ko an taba nonuwan su basu jin komai, amma wasu ko yaya aka taba su, to , suna tasirantuwa sosai. Wannan yanayin halittar mace ne.
4. Rashin samun halittar kasusuwan baya, kirji, da kafaɗu masu kyau (poor posture). Wannan yana nufin idan halittar ƙasusuwan kirjin ki, da kafaɗun ki, da bayan ki sun sunkuya basu tsaya a tsaye kyam ba, to hakan zai sanya tsokoki da fatar nonon ki su takure, daga nan sai nonon ki ya rika yi miki ciwo akai-akai, har zuwa bayanki.
Idan haka halittar kasusuwan kirjin ki suke, to, zaki iya samun saukin ciwon nono ne ta hanyar yawan yin atisayen bankare ƙirjin ki da bayan ki (postural exercises), tare da zama ko kwanciya a wuraren da bayan ki da kafaɗun ki ba za su takura ba.
5. Canje-canjen nono sakamakon kullutun nono (fibrocystic breast changes), wanda yake faruwa saboda cutar fibroadenoma. Fibroadenoma shi ne kullutun nono wanda yake sanya jin wani ƙullutu ko kumburi mai ƙarfi ko laushi a cikin nono. Wani lokacin nono yakan kumbura ko ya gunɗi ruwa, ya haddasa jin zafin nono idan aka taba ko ba'a taba ba.
0 Comments