Jarababben Namiji: Fadakarwa Akan Alamomin Rashin Lafiyar Namiji

Jarababben namiji


Matukar mazajen yanzu zasu riƙa amfani da maganganun abokai, magungunan masu sayar da magani da kallace kallacen hotuna da bidiyon turawa ba zasu taɓa zama lafiya ba a gidajen auren su.

Sai kaga wani jarababben namiji ko aure bai yi ba amma ya fassara kansa a matsayin maras lafiya. Haka kuma sai kaga wani jarababben namiji gashi yayi aure malan hadda haihuwa amma ya koma gefe yana zargin wai gabansa baida tsawo ko girma, ko yana saurin kawowa, ko kuma wai baya iya daÉ—ewa.

Bata lokaci ne da rashin aikin yi saurayi wanda bai da ko mata ya tsaya yana bin mu a inbox ko yana bibiyar masu magani yana iƙirarin wai baida lafiya ta gaban sa, alhali ko aure bai yi ba.

Mazaje maimakon dagewa da kashe kuÉ—aÉ—e a banza wajen neman magungunan da basu da amfani gwara ku saya wa 'yan matan ku sarkar sallah, ko a sai ma iyalai taliya da shinkafa yar gwamnati ka da a sai bahausa don Allah a dafa iyalai kowa ya anfana yafi neme-nemen magungunan da basu da amfani a cikin wannan tsadar rayuwa.

Babu wata hanya da É—a namiji zai fahimci baya da lafiya alhali ko aure bai yi ba, in kau kaga namiji ya dage da tambayar ka baya da lafiya Kuma tazuru ne yi masa wa'azi yaji tsoron Allah.

Babbar matsalar da ya dace mazaje su damu da ita shi ne rashin tashin gaba da kuma rashin ruwan maniyyi gaba É—aya.

Wadannan alamomin su ne manyan alamomin da suka dace a fara la'akari dasu a É“angaren rashin haihuwar É—a namiji.

Idan maigida ya fahimci kwata kwata baya fitar da maniyyi a lokacin inzali ko kuma maigida ya fahimci sam gabansa baya tashi duk da cewa yana cikin sha'awa yin haka, toh akwai matsala. Duka Wadannan ga ma'aurata nake magana, ba wai namijin da bai da mata ko baiyi Aure ba.

Bata lokaci da rashin aikin yi saurayi wanda bai da ko mata ya tsaya yana bin mu a inbox ko yana bibiyar masu magani yana iƙirarin wai baida lafiya ta gaban sa, alhali ko aure bai yi ba.

Ku daina neman mata, kuji tsoron Allah, komai zaman mutum jarababben namiji bazai fahimci lallai cikar lafiyar sa ba ko akasin hakan ta hanyar anfani da mace a waje ko wacce ba matar sa ba ta yau da kullum. 

Wannan shi yasa sai an kwashe watanni 12 ana zaune tare da mace ba a samu juna biyu ba za a fara tuhumar matsala ta rashin haihuwa. Toh ina ga wanda bai yi auren ba ko wanda yake tarayya da mace cikin tsoro da fargaba, minti 5 ya tashi ya kakkabe wandonsa kuma ace ana zargin matsala ta rashin lafiyar Gaba.

Alamomin Rashin Lafiyar Namiji

Akwai wasu alamun da masana suka gano ga mazan da suke fama da cututtuka a fannin al'aurar su. Ga wasu alamun kamar haka.

1. Jin zafi

Idan kana yawan jin ciwo ko zafi a kan azzakarin ka, ko kana jin zafi yayin fitsari, ko kuma a lokacin da kake inzali (Ejaculation) ko ma kana jin zafi a lokacin da kake saduwar aure, toh waÉ—annan duk alamomi ne dake nuna cewa akwai matsala a tare dake. Nan take kayi maza ka garzaya kaga likita domin neman magani.

2. Sauyin Kalar Fitsari 

Idan kaga fitsarinka ya sauya, ko ka fara samun zubar farin ruwa ba ayan ka kammala fitsari, ko fitsarin ka ya rikiÉ—a ya zama kamar madara. Toh wannan ma alamu  ne dake nuna cewa akwai matsala a azzakarin ka. Ka kula da yanayin fitsarinka, domin gano idan ya sauya hakan zai sa kayi maza kaga likita.

3. Rashin Kuzari 

Da zarar kaga mazakutarka babu kuzari kaman yadda ka saba gani, alamu ne dake nuna cewa azzakarin ka ya kamu da rashin lafiya.

Yana da kyau kaga azzakarin ka mike gal, tana harbawa a duk lokacin da sha'awar ka ta motsa. Idan har kana samun wahala wajen miÆ™ewar azzakarin ka duk da kana cikin sha'awa, toh wannan alama ce ta rashin lafiya. 

Namiji mai lafiya idan azzakarin sa ya miƙe yana iya huda gaban mace da karfin azzakarinsa ba tare da ya rike shi da hannu ya zura ba. Wannan shi ne lafiyayyen karfin gaban namiji. Muddin ka fahimci gaban ka da rauni, to kayi maza ka ga likita domin samun taimako.

4. Kumburi Ko Ƙuraje 

Wasu alamomi ne da suke nuna gaban namiji akwai matsala. Daga zarar kaga gabanka ya kumbura ko wasu ƙuraje sun feso maka. Kada ka dauki wannan abun da wasa maza garzaya wajen likita domin neman magani.

5. Zubar Ruwa Mai Wari

Idan gaban ka na dauke da wasu cututtuka, zaka ga gabanka na fitar da wani ruwa mai wari. Da zaran ka ga hakan a tare da kai, to ka maza garzaya wajen likita.

6. Kaikayi

Gaban namiji idan yana kaikayi tabbas akwai matsala. Kaikayi alamomi ne na rashin lafiya ko da kuwa a jiki ne bare kuma akan azzakari.

Kammalawa 

Wadannan su ne wasu daga cikin alamomin cutukan dake iya shafan azzakari. Wanda ya kamata duk wani É—a namiji yayi hankali da su. Mafi yawancin maza masu neman magungunan karfin gaba ko kuzari ko dadewa ana jima'i kuma basu da ko É—aya daga cikin alamomin da muka lissafa, toh lafiyar su kalau, jarraba ce kawai ke damun su.

Post a Comment

0 Comments