Ad Code

Ticker

6/recent/ticker-posts

Illolin Maganin Karfin Maza Da Dadewa Ana Jima'i

Gabatarwa:

Kwayoyin inganta jima'i, wandanda aka fi sani da maganin karfin maza, wasu nau'o'in magunguna ne da ake da'awar suna kara sha'awar jima'i, sanya dadewa ana yin jima'i, karawa namiji kuzari da kuma samun mikewar azzakari tsattsaura.

Maganin karfin maza

A cewar Hukumar Kula da Abinci da Magunguna ta Amurka (FDA), mafi yawan magungunan karfin maza suna haifar da wasu illoli a jikin namiji musamman wanda ya lazimci amfani dasu ko da yaushe.

Rashin karfin mazakuta, wanda kuma ake kira rashin kuzari ko kuma rashin karfin maza, na iya shafar ingancin rayuwar namiji ta hanyar rage jin daɗin jima'i, rage masa walwala, har ma da kawo fitinar aure.

Akwai abubuwa da yawa masu iya kawowa namiji rashin kuzari, tun daga halittar namiji (wasu a haka Allah ya halicce su basu da kuzari), yanayin rayuwar namiji, matsananciyar damuwa da kuma wasu cututtuka irinsu ciwon sugar da kuma hawan jini. 

Haka kuma karfin maza da karfin sha'awa da juriyar jima'i duk suna raguwa a yayin da namiji yake tsufa. Masana sun ƙiyasta cewa karfin yana fara raguwa ne daga bakin shekaru hamsin zuwa sama.

Magungunan karfin maza suna da inganci sosai wajen kara kaimin jima'i da sha'awa ga masu amfani dasu, haka kuma, suna da nasu illoli. Sai dai hanzari ba gudu ba, ba'a amfani da maganin karfin maza haka kawai, saki ba kaidi ga lafiyayyen namiji, sai namiji wanda ya fara fuskantar matsaloli a wajen saduwa da iyalansa. 

Domin gujewa wadannan illolin anso lafiyayyen namiji yayi hakuri da ainihin kuzarinsa da Allah ya hore masa ba tare da amfani da maganin karfin maza ba.

Bugu da kari idan lafiyayyen namiji ya fara afkawa maganin karfin maza tun yana saurayinsa toh, ainihin kuzarinsa na halitta zai fara raguwa, har sai yakai lokacin da idan bai yi amfani da maganin karfin maza ba toh bazai iya saduwa da iyalansa ba.


Illolin maganin karfin maza

1. Ciwon kai 

Ciwon kai shi ne illar da ta zama ruwan dare cikin illolin da magungunan karfin maza ke kawowa. Maganin karfin maza yana kawo ciwon kai ne ta hanyar chanja yadda jini ke gudana a cikin magudanan jini kai tsaye. Ana maganin irin wannan ciwon kai ta hanyar shan magungunan rage radadi masu dauke da sinadarin caffeine kama Panadol Xtra.

2. Ciwon jiki da gaɓɓai 

Wasu mutane suna fama da ciwon gaɓɓai da jijiyoyi da zafi a cikin jikinsu yayin da duk sukayi amfani da maganin karfin maza. Wasu mutane kuma suna samun ciwon baya ne wanda zai rike musu gadon baya da tsara.

3. Ciwon ciki da matsalolin tsarin narkewar abinci

Maganin karfin maza na iya haifar da lahani da gurbata tsarin narkewar abinci a ciki. Mafi akasari abinda maganin karfin maza yake haifarwa a ciki su ne, ciwon ciki, kumburin ciki saboda rashin narkewar abinci da kuma gudawa.

Don taimakawa irin wadannan matsaloli na ciwon ciki, yi la'akari da yin canje-canjen abinci.

4. Jiri da ganin juwa

Ƙaruwar sinadarin nitric oxide da maganin karfin maza yake kawowa a cikin jini na iya sa wasu maza ganin juwa ko kuma jin jiri. Juwar da magungunan karfin mazakuta ke haifarwa mafi akasari ba mai tsanani ba ce, amma wani sa'ilin yana iya yin tsanani har ya sa mutum ya suma. Idan kuna fuskantar juwa yayin amfani da maganin karfin maza toh ku daina amfani dashi kuma ku garzaya a asibiti domin ganin likita.

5. Matsalar idanu

Maganin karfin maza na iya canza yadda kuke ganin abubuwa a zahiri.  Yana iya ragewa namiji hangen nesa na ɗan wani lokaci ko kuma yasa mutum ya kama gani bishi - bishi ko kuma garaye - garaye. Ba'a ba da shawarar namiji yayi amfani da maganin karfin maza idan yana da matsalar idanu, domin yakan iya kara tsananta matsalar. 

6. Mikewar gaba da baya kwantawa

Wannan wani mummunan illah ne da maganin karfin maza ko karfin mazakuta ke haifarwa. Idan ansha wannan maganin karfin maza fiye da kima yakan iya haifar da mikewar azzakari da baya kwantawa ko bayan sha'awar namiji ta yanke. Wannan yanayi ne mai matukar ciwo, haka kuma, yana bukatar kulawa ta gaggawa musamman idan azzakari yakai akalla sa'a huɗu a miƙe. 

Namiji ya hanzarta zuwa asibiti idan ya yi amfani da maganin karfin maza kuma azzakarin sa yaki kwantawa bayan sha'awarsa ta dauke.

A asibiti za'a yiwa mutum wasu 'yan dubaru domin gabansa ya kwanta. Idan kuwa yaki kwantawa to ya wajaba ayi masa aikin tiyata da zai sa abin ya kwanta. A lura cewa, idan har aka kai ga yiwa mutum wannan aikin tiyata toh azzakarinsa bazai kara tashi ba har abada.

7. Sauran illolin da mutum zai iya fuskanta yayin da yake ya lazimci amfani da maganin karfin maza sun hada da toshewar hanci, jan fuska watarana har da ƙananan ƙurajen jiki.

Kammalawa

Idan mutum yana da ɗaya daga cikin waɗannan mahimman illolin, ya kamata ya tuntuɓi likita nan da nan. Wasu sun fi samun waɗannan illolin fiye da wasu. Wannan na iya kasancewa da alaƙa da wasu al'amurran kiwon lafiya ko magungunan da suke sha.

 Yayin shan waɗannan magunguna, yana da mahimmanci don sanar da likita game da duk wani magungunan yau da kullun da ake sha da sauran batutuwan likitanci da mutum zai iya fuskanta. 


NassoshiPrint this post

Post a Comment

0 Comments