Matsayar Ilmin Likitanci Na Zamani Dangane Da Cututtukan Shafar Aljanu

Assalam Alaikum Dr ina wunee. Doctor nayi fama da matsalar aljanin dare (Namijin dare). Har Nakai Lokacin da dade zai iya kwanciya dani, ina mafarkinsa. Alhamdulillah an nemaman magani na warke sede, haryanzu banajin sha'awa,  haihuwata 2.

Wani zubin sai in mijina ne ya siyomun maganin ƙarin sha'awa Sannan nake jin sha'awar koshi ba kowane lokaci ba. Wani zubin idan ma nasha banajin sha'awar.



Amsa

A likitancin zamani, ana yarda da matsalolin rashin lafiya ne kawai idan za'a iya gane su ta hanyar yin binciken kimiyya na asibiti (medical diagnosis). Hakan yana nufin cututtukan da suke da dangantaka da shafar aljanu, waɗanda ba za'a iya ganewa ba ta hanyar binciken dakin kimiyya (laboratory investigations), toh, ba'a iya yarda dasu.

Amma likitoci musulmai sun yarda da cewa akwai cututtukan da shafar aljanu take haddasawa, bisa la'akari da Ayoyin Qur'ani da Hadithan Annabi Muhammad SAW.

Misali, Suratul-Baqarah, Aya ta 275 tace:

ٱلَّذِينَ يَأْكُلُونَ ٱلرِّبَوٰا۟ لَا يَقُومُونَ إِلَّا كَمَا يَقُومُ ٱلَّذِى يَتَخَبَّطُهُ ٱلشَّيْطَٰنُ مِنَ ٱلْمَسِّۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمْ قَالُوٓا۟ إِنَّمَا ٱلْبَيْعُ مِثْلُ ٱلرِّبَوٰا۟ۗ وَأَحَلَّ ٱللَّهُ ٱلْبَيْعَ وَحَرَّمَ ٱلرِّبَوٰا۟ۚ فَمَن جَآءَهُۥ مَوْعِظَةٌ مِّن رَّبِّهِۦ فَٱنتَهَىٰ فَلَهُۥ مَا سَلَفَ وَأَمْرُهُۥٓ إِلَى ٱللَّهِۖ وَمَنْ عَادَ فَأُو۟لَـٰٓئِكَ أَصْحَـٰبُ ٱلنَّارِۖ هُمْ فِيهَا خَـٰلِدُونَ.

Ma'ana, wadanda suke cin riba, zasu tashi ranar lahira kamar wadanda suka sami shafar aljanu...... Har zuwa ƙarshen ayar.

Suratul-Hijr, Aya ta 27 Allah yace:

وَٱلْجَآنَّ خَلَقْنَـٰهُ مِن قَبْلُ مِن نَّارِ ٱلسَّمُومِ.

Ma'ana, tun farko mu (Allah) mun halicci aljanu daga wuta mai tsananin zafi.

Suratun-Nas, Aya ta 1 - 6 tace:

قُلْ أَعُوذُ بِرَبِّ ٱلنَّاسِ. مَلِكِ ٱلنَّاسِ. إِلَـٰهِ ٱلنَّاسِ. مِن شَرِّ ٱلْوَسْوَاسِ ٱلْخَنَّاسِ. ٱلَّذِى يُوَسْوِسُ فِى صُدُورِ ٱلنَّاسِ. مِنَ ٱلْجِنَّةِ وَٱلنَّاسِ.

Ma'ana, ka nemi tsarin Allah SWT daga aljani wanda yake da tasirin sanyawa mutum shakku a cikin zuciya.

Sahihul-Bukhari (Mujalladi na 7, Hadith na 71) yace:

سُحِرَ النبي صلى الله عليه وسلم حتى إنه ليخيل إليه أنه يفعل الشيء وما فعله.

Ma'ana, anyiwa Annabi Muhammad SAW sihiri, kuma yayi tasiri har ya rika ganin kamar yayi wani abu, alhalin baiyi ba.

Sahih Muslim (Hadith na 2187) yace:

إِنَّ الشَّيْطَانَ يَجْرِي مِنَ الإِنْسَانِ مَجْرَى الدَّمِ.

Ma'ana, aljani yanada tasirin shiga cikin jikin mutum ya rika yawo kamar yadda jini yake gudana a cikin jijiyoyin jiki.

Sahih Muslim (Hadith na 2188) yace:

لَا بَأْسَ بِالرُّقَى مَا لَمْ يَكُنْ فِيهِ شِرْكٌ.

Ma'ana, babu laifi ayi addu'ar neman samun warakar shafar aljanu, matukar ba'a yi shirka da Allah SwT ba.

Duk wadannan jerin gwanon hujjojin suna tabbatar da tasirin aljani a jikin mutum ne, amma sai idan Allah SwT ya yarda. Don haka tunda kin ce an tabbatar kina da matsalar shafar aljanu, toh, abinda ya kamata kiyi shine ki dage da yin zikirori da ingantattun Hadithan Annabi Muhammad SAW suka tabbatar, ba tare da kinyi shirka ba. Zaki iya samunsu a cikin littafin Hisnul Muslim In-sha-Allah.

Sa'annan ki hada da magungunan asibiti na daukewar sha'awa. Akwai bayanai masu yawa akan matsalar daukewar sha'awa a cikin group dinnan. Kiyi searching, zaki sami cikakken bayani in-sha-Allah.

WalLahu A'lam. 

Ainihin wanda ya amsa tambayar Dr. Usman Shehu Hassan 

Post a Comment

0 Comments