Zubar Farin Ruwa Da Jini A Gaban Jarirai Mata

Aslm ina yiwa kowa fatan alkhairi, please Dr me ke sa gaban jarire mata ke fidda wani farin ruwa mai yauqi kamar madara wani lokaci ma harda jini

Zubar Farin Ruwa Ko Jini A Gaban Jarirai Mata


Amsa

Fitar farin ruwa mai yauƙi kamar madara daga gaban jaririyar ki mace a karon farko ba lallai bane ya zamo alamun kamuwa da kwayoyin cuta a gabanta ba, musamman idan bata nuna alamun rashin lafiya kamar yawan kuka, kin shan nono, yawan mutsu-mutsu, da rashin bacci.

Wannan yana faruwa ne saboda janyewar sinadaran estrogen da progesterone daga jikin ta wanda take samu daga jikin uwarta kafin a haife ta (maternal hormone withdrawal). 

Shi kuwa jini-jini da yake fitowa shine ake kira "pseudo-menstruation", kuma duk yana da alaka da janyewar wadannan sinadaran. Wannan yanayin yakan warkar da kansa bayan 'yan kwanaki kadan, ba tare da anyi amfani da magunguna ba. 

Amma idan ya cigaba har na tsawon lokaci, ko kuma ya hadu da alamun rashin lafiya, to, ki kai yarinyar a asibiti domin ayi bincike a tabbatar da abinda yake faruwa da ita.

Wani lokaci kuma irin wannan yanayin yana faruwa ne sakamakon kamuwa da kwayoyin cuta, kamar kumburin farjin (neonatal vaginitis), ko yeast infection wanda kwayoyin fungi suke haddasawa (candida), ko rashin canza mata pampers akai-akai tareda rashin tsabtace mata gabanta (diaper rash-associated infections), ko kamuwa da cututtukan farji wanda uwar take iya yaÉ—awa yaro a lokacin haihuwa (congenital infections).

Sai dai yana da kyau mu fahimci cewa dukkan wadannan cututtukan da muka ambata suna sanya jaririya ta nuna alamun kamuwa da rashin lafiya in addition to fitar jini ko farin ruwa a gaban ta. Don haka sai a kaita asibiti domin likita ya duba ta.

Post a Comment

0 Comments