Alamomin Cutar Kansar Mama (Breast Cancer): Abubuwan da Kowace Mace Ya Kamata Ta Sani

Gabatarwa

Alamomin kansar mama


Cutar kansar mama (Breast Cancer) na ɗaya daga cikin cututtuka da sukafi kamari da ke shafar mata a duniya, ciki har da Najeriya da sauran ƙasashen Afirka. Abin bakin ciki shi ne, yawancin mata suna gano cutar ne a makare, bayan lokacin da ake iya yin wani abu ya riga ya ƙure, wanda hakan ke rage damar samun cikakkiyar warkewa.

Sanin alamomin kansar mama da wuri na da matuƙar muhimmanci, domin yana taimakawa wajen gano cutar tun tana matakin farko, inda magani ke da sauƙi kuma sakamako yafi kyau.

A wannan rubutu, za mu yi bayani dalla-dalla kan alamomin kansar mama, dalilan da ke haddasa ta, da kuma lokacin da ya dace mace ta ga likita.

Rubutu Mai Alaka: Wayar da Kan Jama’a Kan Cutar Kansar Nono (Breast Cancer Awareness in Hausa)

Menene Kansar Mama?

Kansar mama cuta ce da ke faruwa idan ƙwayoyin halittar mama suka fara girma ba tare da tsari ba, suna rarrabuwa fiye da kima. Waɗannan ƙwayoyin na iya taruwa su zama ƙumburi (lump) ko su bazu zuwa wasu sassan jiki idan ba a gano su da wuri ba.

Kansar mama na iya shafar:

  • Mata 
  • Maza (amma da wuya)

Manyan Alamomin Kansar Mama

1. Kumburi a Mama

Samuwar Ƙumburi a Mama ko Ƙasan Hannu ko Cikin Hamata: Wannan ita ce babbar alamar da aka fi sani. Ƙumburin kan kasance:

  • Ba ya ciwo
  • Yana da tauri
  • Ba ya motsi da hannu
  • Zai iya bayyana: A mama, a Æ™arÆ™ashin hannu (Æ™asan hannu) ko a cikin hamata.

⚠️ A lura sosai, ba kowane kumburi ba ne kansa, amma duk kumburin da ya daÉ—e yana bukatar dubawar likita.

2. Sauyin Girma ko Siffar Mama

Idan mace ta lura da:

  • Mama É—aya ta fi É—aya girma
  • Canjin siffa ba tare da dalili ba
  • Kumburin da bata saba gani ba

Wannan na iya zama alamar matsala a cikin mama.

Cikakken Bayani: Yadda Mace Zata Dinga Yin Binciken Nono Ko Gwajin Nono A Gida Domin Gano Matsalar Nono Da Wuri

3. Sauyin Fatar Mama

Cutar kansar mama na iya shafar fatar mama ta hanyoyi kamar:

  • Fatar ta yi kamar bawon lemu
  • Fatar ta yi ja ko duhu
  • Fatar ta fara kauri ko ta bushe
  • Fatar ta fara yin Æ™aiÆ™ayi ba tare da dalili ba

4. Sauyin Kan Nono (Nipple Changes)

Wasu alamomin cutar kansar mama da ke da alaƙa da kan nono sun haɗa da:

Kan nono ya shiga ciki (inverted nipple)

Jin zafi ko kaikayi a kan nono

Fitar ruwa daga kan nono ba tare da matsawa ba

Musamman idan ruwan yana launin ja (jini) ko launin rawaya mai duhu.

Ku karanta: Zubar Ruwan Nono Ga Budurwa Wanda Bayada Alaqa Da Shan Nono Ko Shayarwa - Galactorrhoea

5. Jin Ciwo ko Zafi a Mama

Ko da yake yawanci kansar mama ba ya haifar da ciwo a matakin farko, amma:

  • Idan zafin ya daÉ—e
  • Ba ya da alaÆ™a da lokacin zuwan jinin haila
  • Yana faruwa a wuri É—aya kullum
Toh yana da kyau mace ta je asibiti.

6. Kumburin Hannu ko Kafadar Gefen Mama

Idan kansar ta fara bazuwa:

  • Ƙasan hannu na iya kumbura
  • Ana iya jin nauyi ko zafi a kafada

Wannan na iya nuna cewa ƙwayoyin cutar sun shiga hanyoyin lymph.

7. Canjin Yanayin Mama Lokacin Taɓawa

Idan maman mace:

  • Ya yi tauri fiye da yadda aka saba
  • Ya yi sanyi ko zafi ba tare da dalili ba
  • Ya rasa laushinta na al’ada

Duk waÉ—annan na iya zama alamomin cutar kansar mama.

Alamomin Kansar Mama a Matakin Farko

A matakin farko:

Alamomi na iya zama kaÉ—an, wani lokaci babu alama kwata-kwata.

Saboda haka ne ake bada shawarar:

Duba mama da kai (Self breast examination)

Yin gwajin asibiti lokaci-lokaci

WaÉ—anne Mata Ne Suka Fi Fuskantar Hadarin Kamuwa Da Cutar Kansar Mama?

Duk mace na iya kamuwa, amma haɗarin yafi ƙaruwa idan:

  • Akwai tarihin kansar mama a iyali
  • Mace ta haura shekaru 40
  • Tayi saurin fara haila tun kamin ta shekara 13
  • Ta jinkirta haihuwa ko ba ta taÉ“a haihuwa ba
  • Ta yi amfani da wasu magungunan sinadaran hormones na dogon lokaci.

Muhimmancin Gano Kansar Mama Da Wuri

Fa’idodin gano cutar da wuri sun haÉ—a da:

  • SauÆ™in magani
  • Rage kashe kuÉ—i
  • Karin damar warkewa gaba É—aya
  • Rage saurin mutuwa

A Najeriya, matsalar ba rashin magani ba ce kawai, rashin sani ne ke jawo matsala.

Yaushe Ya Kamata Mace Ta Ga Likita?

Ki je asibiti nan da nan idan:

  • Kin lura da kumburi
  • Kin ga sauyin fata ko kan nono
  • Kina jin zafi da bai saba ba
  • Kina ganin fitar ruwa daga nono ba tare da shayarwa ba

Yadda Mace Za Ta Kare Kanta Daga Kamuwa Da Kansar Mama (Rigakafi)

Ko da ba a iya hana kamuwa da kansar mama gaba É—aya, akwai abubuwan da ke rage haÉ—arin kamuwa da cutar kamar haka:

  • Yin motsa jiki akai-akai
  • Cin abinci mai gina jiki
  • Rage kiba
  • Gujewa shan taba
  • Yin duba mama da kai duk wata

Kammalawa

Cutar kansar mama ba kabari kusa ba ce idan aka gano ta da wuri. Sanin alamomin kansar mama na iya ceton rai, ba wai naki kaÉ—ai ba, har da na ‘yan’uwa da abokai baki daya.

Ki kasance mai lura da jikinki, ki É—auki duk wani canji da muhimmanci, kuma ki nemi shawarar likita ba tare da jinkiri ba. Lafiyar mama, lafiyar rayuwa ce.

Tambayoyi da Amsoshi (FAQ) Akan Alamomin Kansar Mama

1. Menene kansar mama?

Kansar mama cuta ce da ke faruwa idan Æ™wayoyin halittar mama suka fara girma ba bisa ka’ida ba, suna haifar da Æ™umburi ko canje-canje a mama.

2. Mene ne alamomin farko na kansar mama?

Alamomin farko sun haÉ—a da:

  • Ƙumburi a mama ko Æ™asan hannu
  • Sauyin girma ko siffar mama
  • Sauyin fatar mama ko kan nono

3. Shin duk kumburin mama kansa ne?

A’a. Ba duk Æ™umburi ba ne kansa, amma duk Æ™umburin da ya daÉ—e ko ya canza yana bukatar dubawar likita.

4. Shin kansar mama tana ciwo?

A yawancin lokuta, kansar mama ba ta ciwo a matakin farko. Amma idan zafi ya daɗe ko yana ƙaruwa, yana da kyau a ga likita.

5. Shin mata matasa na iya kamuwa da kansar mama?

Eh. Ko da yake ta fi yawa ga mata masu shekaru 40 zuwa sama, matasa ma na iya kamuwa da ita.

6. Shin namiji na iya kamuwa da kansar mama?

Eh, namiji na iya kamuwa da kansar mama, amma hakan ba kasafai yake faruwa ba.

7. Me ke jawo kansar mama?

Ba abu É—aya kaÉ—ai ke jawo kansar mama ba. Abubuwan haÉ—ari sun haÉ—a da:

  • Tarihin kansar mama a iyali
  • Shekaru masu yawa
  • Sauyin hormone
  • Rashin motsa jiki da kiba

8. Yaya ake gano kansar mama da wuri?

Ana iya gano kansar mama da wuri ta hanyar:

  • Duba mama da kai a duk wata (self breast examination)
  • Gwajin likita
  • Gwajin mammography idan likita ya bada shawara

9. Shin kansar mama na warkewa?

Eh. Idan aka gano kansar mama da wuri, akwai babban damar samun cikakkiyar warkewa.

10. Yaushe ya kamata mace ta je asibiti?

Mace ya kamata ta je asibiti idan:

  • Ta ga Æ™umburi a mama
  • Ta lura da sauyin fata ko kan nono
  • Ta ga jini ko ruwa daga nono ba tare da shayarwa ba

11. Shin shayarwa na rage haÉ—arin kansar mama?

Eh. Shayarwa na taimakawa wajen rage yiwuwar kamuwa da kansar mama.

12. Shin ana iya hana kansar mama gaba É—aya?

Ba za a iya hana ta gaba É—aya ba, amma ana iya rage haÉ—ari ta hanyar:

  • Motsa jiki akai-akai
  • Cin abinci mai kyau
  • Gujewa shan taba
  • Duba mama da kai lokaci-lokaci

13. Sau nawa mace ya kamata ta duba mamanta da kanta?

Ana bada shawarar mace ta duba mamanta sau É—aya a wata, kwanaki 5–7 bayan haila.

14. Shin canjin kan nono alama ce ta kansar mama?

Eh. Canjin kan nono kamar shigar kan nono ciki, jin zafi, ko fitar ruwa na iya zama alamar kansar mama.

15. Me ya sa gano kansar mama da wuri yake da muhimmanci?

Gano cutar da wuri yana:

  • SauÆ™aÆ™a magani
  • Rage kashe kuÉ—i
  • Ƙara damar warkewa
  • Rage mace-mace ta hanyar cutar 

No comments: