Gabatarwa
Cutar kansar nono (Breast Cancer) na daga cikin manyan cututtukan da suka fi shafar mata a duniya, musamman mata ‘yan shekaru 40 zuwa sama. A cewar binciken lafiya na Æ™asa da Æ™asa, an kiyasta cewa miliyoyin mata a kowace shekara suna fama da cutar kansar nono, kuma a cikin su, mata daga Æ™asashe masu tasowa, ciki har da Najeriya, na cikin haÉ—arin rasa rayukan su saboda Æ™arancin ilimi, rashin gano cutar da wuri da kuma Æ™arancin kayan magani.
Wannan rubutu zai yi bayani dalla-dalla kan cutar kansar nono a Hausa domin wayar da kan mata da maza, tare da bayyana alamomi, hanyoyin rigakafi, gano cutar da wuri, da kuma maganin ciwon kansar nono.
Menene Cutar Kansar Nono?
Cutar kansar nono wata cuta ce ta kansa da ke tasowa lokacin da ƙwayoyin halitta (cells) na nono suka fara girma da sauri fiye da ƙima, sannan suka taru suka zama ƙurji (tumor). Idan ba a gano cutar kansar da wuri ba, zai iya bazuwa zuwa sauran sassan jiki kamar ƙashi, hanta, huhu, ko kwakwalwa.
Rubutu Mai Alaka: Bayani Game Da Tsiro, Kololo, Kumburi Ko Karin Girman Nonon Mace
Muhimmancin Wayar da Kan Jama'a Game da Cutar Kansar Nono
Gano cutar kansar nono da wuri yana iya ceton rai, domin magani kan fi yin tasiri idan an gano cutar a farkon matakinta.
Ilmantar da mata game da yadda za su binciki nononsu a kai a kai (breast self-examination).
Karfafa gwaje-gwajen lafiya kamar mammogram da hoton duba mai amfani da yanar sauti (ultrasound).
Rage tsoro da kunya da ke hana mata bayyana matsalar lafiya.
Alamomin Cutar Kansar Nono
Alamomin cutar kansar nono na iya bambanta daga mace zuwa wata mace, amma wasu daga cikinsu sun haÉ—a da:
1. Samun ƙurji ko ƙullutu (lump) a cikin nono ko a ƙasan hamata.
2. Sauyin siffa ko girman nono.
3. Fitar ruwa ko jini daga kan nono ba tare da shayarwa ba.
4. Fatar nono ta yi ƙanƙancewa ko ta yi launin ja.
5. Zafi ko kaikayi a nono ba tare da dalili ba.
6. Ƙurajen fata ko kumburi a wajen nono.
7. Takurewar fatar nono
Idan mace ta lura da É—aya daga cikin waÉ—annan alamomin cutar kansar nono, ya zama wajibi ta garzaya cibiyar duba lafiya domin duba lafiyar ta.
Rubutu Mai Alaka: Me Ke Kawo Ciwon Nono A Lokacin Jinin Al'ada (Period)?
Abubuwan Da Ke Haifar da Cutar Kansar Nono
Duk da cewa ba a san ainihin musabbabin cutar ba, akwai wasu abubuwan haɗari da ke iya ƙara yiwuwar mace ta kamu da cutar kansar nono kamar haka:
Shekaru – Yawan shekaru na Æ™ara haÉ—ari, musamman bayan mace ta wuce 40.
Tarihin cutar kansar nono a zuriya – Idan akwai wanda ya taba fama da ciwon nono a cikin dangi makusanta kamar uwa, Æ™anwa ko yaya, hakan na Æ™ara hadarin kamuwa da cutar kansar nono.
Canjin hormone – Matan da suka fara al’ada da wuri ko suka dade basu daina jinin al'ada ba. Misali yarinyar da ta fara jinin al'ada tun tana da shekaru 8 ko macen da ta wuce shekaru 45 - 50 bata daina yin jinin al'ada ba.
Fara haihuwa da wuri ko rashin haihuwa ga baki daya.
Ciwon kiba (obesity) – Musamman idan ya hadu da cin abinci mara kyau da rashin motsa jiki.
Shan giya da tabar sigari.
Radiation ko gurɓataccen muhalli.
Yadda ake Rigakafin Cutar Kansar Nono
Koda yake ba za'a iya kaucewa cutar gaba É—aya ba, akwai hanyoyin da za su rage haÉ—arin kamuwa da ita:
1. Kula da nauyin jiki ta hanyar cin abinci mai kyau da motsa jiki akai-akai.
2. Gujewa shan giya da tabar sigari.
3. Shayar da jariri (breastfeeding) – Yana rage yiwuwar kamuwa da cutar.
4. Gudanar da gwaje-gwajen da binciken lafiya akai-akai.
5. Binciken nono da hannu (self-exam) aƙalla sau ɗaya a wata.
Yadda Ake Binciken Nono da Hannu (Self-Examination)
Wannan hanya ce mai sauƙi da kowace mace za ta iya yi a gida domin gano cutar kansar nono da wuri:
1. Tsayawa a gaban madubi ki duba idan akwai sauyi a siffar nono.
2. Taɓa nono da hannu ta hanyar shafa nono gaba ɗaya don jin ko akwai ƙullutu ko kumburi.
3. Matsa kan nono domin duba ko akwai fitar ruwa daga nono.
4. Ana yin wannan bincike bayan gama jinin al’ada (period) domin a samun sakamako mafi kyau.
Cikakken Bayani: Yadda Mace Zata Dinga Yin Binciken Nono Ko Gwajin Nono A Gida Domin Gano Matsalar Nono Da Wuri
Yadda Ake Maganin Cutar Kansar Nono
Maganin cutar kansar nono ya danganta da irin matakin cutar da kuma lafiyar marar lafiya gaba É—aya. Hanyoyin magani sun haÉ—a da:
1. Tiyata (Surgery): Aikin tiyata domin cire wani sashen nono ko dukan nono gaba É—aya.
2. Maganin Kansa da Hasken Bature (Radiotherapy): Ana amfani da hasken bature don ƙone ƙwayoyin cutar kansa da suka rage.
3. Maganin Sinadaran Hormone: Domin rage tasirin hormones da ke habaka cutar kansar nono.
4. Chemotherapy: Amfani da magungunan kashe ƙwayoyin cutar kansa.
5. Targeted therapy: Magunguna da aka ƙera musamman don kai hari kan ƙwayoyin cutar kansa.
Matsalolin Da Ake Fuskanta Sakamakon Rashin Gano Kansa da Wuri
A kasashenmu, musamman a Arewa, mata da dama suna:
Jin kunya su sanar da matsalar.
Yin amfani da magungunan gargajiya kafin zuwa asibiti.
Rashin samun damar yin gwajin mammogram saboda ƙarancin cibiyoyin lafiya da ke gudanar da hoton gwajin.
Wannan na jawo asara ta rayuka da yawa, alhali kuwa gano cutar da wuri na iya ceton rai.
Ku karanta: Zubar Ruwan Nono Ga Budurwa Wanda Bayada Alaqa Da Shan Nono Ko Shayarwa - Galactorrhoea
Muhimmancin Gano Cutar Kansar Nono da Wuri
Mata da suka gano cutar kansar nono a farkon mataki suna da fiye da 80% damar samun lafiya idan an fara magani.
Gano cutar kansar nono da wuri yana rage tsawon lokaci da kuÉ—in magani.
Yana ba mace damar ci gaba da rayuwa da lafiya bayan warkewa.
Yana hanawa cutar kansar bazuwa a sauran sassan jiki idan an fara magani da wuri.
Yana bada damar a warkar da mace ta hanyar cire nonon da cutar kansar ta kama baki daya.
Kammalawa
Cutar kansar nono na daga cikin manyan cututtukan da ke barazana ga rayuwar mata, amma gano cutar da wuri, rigakafi, da magani na zamani suna iya ceton rayukan mata dayawa. Ya zama wajibi kowace mace ta:
- Yi binciken nono da hannu a kai-a kai.
- Ziyarci asibiti idan ta lura da daya daga cikin alamomin cutar kansar nono.
- Karanta ilimi da wayar da kai domin kare kanta da iyalanta.
Wayar da kan jama’a kan ciwon nono ba wai ya shafi mata kaÉ—ai ba ne, har ma da maza, domin mazaje ma na iya kamuwa da cutar kansar nono kodayake ba kamar mata ba.
A ƙarshe, mu haɗa kai wajen yaɗa wannan saƙo domin ceton rayuka.
No comments:
Post a Comment