Gabatarwa
Ciwon damuwa (Depression) cuta ce ta kwakwalwa da take shafar tunanin mutum, yanayin jindadin zuciya (mood), da kuma yadda yake hulÉ—a da jama’a. Duk da cewa bakin ciki a wani dan lokaci yakan iya zarcewa ya zama ciwon damuwa, amma ciwon yana da bambanci da bakin ciki ba yau da kullum. Ba kamar bakin ciki na É—an lokaci ba, ciwon damuwa na iya É—aukar tsawon makonni, watanni, ko ma shekaru.
A Æ™asashe da dama ciki har da Najeriya, ana É—aukar ciwon damuwa a matsayin É—aya daga cikin manyan matsalolin lafiyar kwakwalwa da ke Æ™ara yawaita a cikin al'umma. Al’umma da dama na É—aukar ciwon damuwa a matsayin kawai “bakin ciki” ko “raunin zuciya,” amma gaskiyar magana ita ce cuta ce ta ainihi wadda ake buÆ™atar kulawa daga kwararrun likitocin kwakwalwa da kuma tallafin iyali.
Rubutu Mai Alaƙa: Yadda Ake Bude Kwakwalwa Da Kara Kaifin Basira
A cikin wannan rubutu za mu tattauna dalla-dallah game da alamomin ciwon damuwa, yadda ake gane shi, bambanci tsakaninsa da bakin ciki na al’ada, da kuma matakan da ya dace mutum ya É—auka idan ya fara ganin alamomin.
Menene Ciwon Damuwa?
Ciwon damuwa (Depression) yanayi ne da kwakwalwa ke shiga wanda ke shafar tunani, yanayi da dukkan halayyar mutum. Yana iya jawo mutum ya kasa gudanar da ayyukan yau da kullum, kamar aiki, karatu, ko ma hulÉ—a da jama’a.
Masana suna bayyana ciwon damuwa a matsayin “illness of the brain chemistry” wato matsalar rashin daidaiton sinadarai a kwakwalwa. Amma a zahiri, abubuwan da ke haddasa shi sun haÉ—a da haÉ—in gwiwar dalilai na matsalolin jiki, tunani, halayyar rayuwa, da muhalli.
Muhimmancin Gane Alamomin Ciwon Damuwa
- Yana taimakawa a gano cutar tun da wuri kafin ta tsananta.
- Yana kare mutum daga illolin ciwon damuwa masu haɗari kamar yanke ƙauna ko tunanin kashe kai.
- Yana sauƙaƙa tattaunawa tsakanin iyalai da abokai domin a bayar da tallafi.
- Yana rage tsangwama da rashin fahimta a cikin al’umma.
Manyan Alamomin Ciwon Damuwa
1. Bakin Ciki na Dogon Lokaci
Zaku iya Karanta: Illolin Istimna'i Da Yadda Mutum Zai Daina Istimna'i (Masturbation )
2. Rashin Sha’awa da Jin DaÉ—in Abubuwan da Ka Saba na Jindadi
3. Matsalolin Barci
Rashin barci (insomnia): Mutum na kasa yin barci da wuri ko kuma yana farkawa cikin dare ba tare da dalili ba.
4. Rashin Ci ko Yawan Cin Abinci
5. Gajiya da Rashin Kuzari
6. Tunanin Cewa Ba Su da Amfani
7. Rashin Mai da Hankali akan Komai
8. Alamomin Jiki na Ciwon Damuwa
- Ciwon kai akai-akai.
- Ciwon ciki da rashin narkewar abinci.
- Tsokoki da ƙasusuwa suna ciwo.
- Zuciya tana bugawa da sauri (palpitation).
9. Tunanin Kashe Kai
Wannan shi ne mafi haɗari daga cikin alamomin ciwon damuwa. Mutum zai iya fara ganin cewa mutuwa ce kawai mafita a garesa. Wannan alama ce da ke buƙatar kulawa ta gaggawa daga likita.
Ku karanta: Facts about Stroke: Types, Risk Factors, Signs, Symptoms, and Prevention
Bambanci Tsakanin Ciwon Damuwa da Bakin Ciki Na Yau da Kullum
Bakin ciki na al’ada: Yakan bayyana bayan wani abu mai sa damuwa (kamar mutuwar É—an uwa, kariyar arziki, rabuwar masoya, mutuwar aure) ya faru, amma irin wannan baÆ™in ciki yana raguwa sannu a hankali. Shi kuma ciwon damuwa, yana dawwama tsawon makonni ko watanni, kuma yana shafar rayuwar mutum gaba É—aya har ya hana shi gudanar da al’amuransa da ya saba yi na yau da kullum.
Bakin ciki na al'ada yakan iya zarcewa ya haifar da ciwon damuwa. Masana sun ayyana cewa duk wani bakin ciki ko damuwa da ya wuce sati biyu yana shafar rayuwar mutum toh ya zarce ya zama ciwon damuwa.
Abubuwan da Ke Haifar da Ciwon Damuwa
- Gadon iyali (genetics): Idan akwai tarihin damuwa a cikin iyali.
- Matsalolin rayuwa: Rashin aiki, matsalar aure, talauci, ko cin zarafi.
- Sinadarai a kwakwalwa: Rashin daidaituwar serotonin da dopamine.
- Rashin tallafi daga iyali ko abokai.
Karanta: Lalurar Shanyewar Sashen Fuska Da Karkacewar Baki - Bell's palsy
Me Ya Kamata a Yi Idan Aka Gane Alamomin Ciwon Damuwa?
Idan ka fara lura da waÉ—annan alamomi, ga abubuwan da zaka yi:
1. Nemi taimakon likita – musamman kwararren likitan kwakwalwa (psychiatrist).
2. Tattauna da wanda ka yarda da shi domin samun shawarwari na fahimta.
3. Ka guji shaye-shaye kamar giya ko miyagun ƙwayoyi domin suna tsananta cutar.
4. Motsa jiki akai-akai domin yana taimakawa wajen sakin sinadarai masu sanya farin ciki da nishadi (endorphins).
5. Cin abinci mai kyau da kuma yin barci mai isasshe.
Zaku iya Karanta: Disorders of Eating: Anorexia Nervosa and Bulimia Nervosa
Yadda ake Maganin Ciwon Damuwa
- Magunguna masu tasiri akan sinadaran farin ciki na kwakwalwa (antidepressants).
- Bada shawarwari (psychotherapy).
- Ƙarfafa mai ciwon damuwa da tallafa masa.
- Wani lokaci, sai an haÉ—a duk waÉ—annan hanyoyin kamin a cimma nasara.
Kammalawa
Damuwa ba alama ba ce ta rauni. Duk wanda yake fama da shi yana da damar murmurewa idan ya nemi taimako da wuri. Yin shiru ba mafita ba ne, neman taimako shi ne babban mataki.
No comments:
Post a Comment