Lalurar Shanyewar Sashen Fuska Da Karkacewar Baki - Bell's palsy

Maganin karkacewar baki


Shanyewar barin fuska larura ce da ke faruwa sakamakon lahani ga tushen jijiyar lakka ta bakwai (7) a cikin lakkokin Æ™waÆ™walwa 12, ko kuma a hanyarta bayan ta fito daga Æ™waÆ™walwa zuwa tsokokin fuska. 

Jijiyar lakka ta bakwai wadda aka fi sani da fascial nerve a likitance, ko seventh cranial nerve a turance, wata jakadiya ce da ke kai-komo a tsakanin ƙwaƙwalwa da fuska.

Wannan jijiyar ita ce ke kula da sarrafa dukan tsokokin fuska da aiwatar da dukkan ayyukan da fuska ke yi, kamar irin su, murmushi, ƙyafta ido, runtse ido, juye baki, ɗaga gira, bayyana gurayen goshi da dai sauran su.

Maganin karkacewar baki
Wannan jijiyar lakkar ta bakwai a cikin lakkokin Æ™waÆ™walwa ta na iya samun matsala kamar shaÆ™ewa, dannewa, lahani daga harbin Æ™wayoyin cuta ko kuma samun rauni sakamakon bugu daga waje ko duk wani kalar rauni a kan hanyarta daga Æ™waÆ™walwa zuwa fuska domin kai saÆ™onni zuwa tsokokin fuska, jakar yawu, jakar hawaye, tsinin harshe, da wata tsoka da ke daidaita sauti da ke cikin kunne wadda ake kira stapedius, da dai sauransu. 

Idan daya daga cikin waÉ—annan matsaloli ya faru, aikin jijiyar lakkar zai yi sanyi ko rauni sai kuma daga baya barin fuska ya shanye. Kowane mutum yana da wannan jijiyar guda biya, É—aya a É“angaren dama É—aya kuma a É“angaren hagu, kowace tana kula da irin É“angaren ta na fuska.

Yadda ake gane barin fuska ya shanye


  • Karkacewar baki: wanda hakan zai sa wahalar riÆ™e abinci a baki ko kawo zirarewar abinci ko abinsha daga baki.
  • Zubowar yawu ta barin da bakin ya shanye.
  • Saukowar gira da kuma yawan zubar hawaye a É“angaren da ya shanye. 
  • Gazawa ko wahalar rufe ido É—aya
  • Gazawa ko wahalar bayyana labarin zuciya a fuska, kamar yin murmushi, fushi da dai sauransu.
  • Matsalar kasa É—aga gira ko tattare fatar goshi ko bayyanar da gurayen goshi.
  • Karuwar jin Æ™ara ko sauti a kunne ta É“arin da fuskar ta shanye.
  • Rashin jin É—anÉ—ano a tsinin harshe
  • Da dai sauransu.

Meke kawo shanyewar barin fuska?

  • Shanyewar barin jiki (stroke), wasu masu shanyewar É“arin jiki kan zo da shanyewar barin fuska.
  • Ciwon sugar 
  • Fashewar jijiyar jini a cikin kai.
  • Ciwon kunne.
  • Matsananciyar mura mai naci.
  • Buguwa/rauni a kai ko fuska.
  • Doguwar tafiya a kan abin hawa tare da iska mai karfi na bugun É“arin fuska tsawon lokaci.

Wannan matsalar ta shanyewar ɓarin fuska na ci wa masu fama da ita tuwo a ƙwarya, kama daga samun wahalhalu wajen cin abin ci ko shan abin sha, zubar hawaye ko yawu wanda ke sa su jin kunyar bayyana fuskar su a cikin jama'a, wanda hakan kan iya saka su ƙauracewa jama'a, ko kuma tilasta musu rufe fuskar su domin gudun tsangwama daga mutane.

Maganin karkacewar fuska

Wannan jinya ta shanyewar ɓarin fuska ana warkewa sarai kamar ba a yi ba, duk da cewa samun waraka ya danganta da tsananin raunin da lakkar ta samu da kuma miye ya kawo raunin. Don haka, idan kina / kana fama da wannan matsala tuntuɓi likitan fisiyo a asibiti mafi kusa da kai.

Likitan fisiyo na amfani da hanyoyin ƙwarewa domin yi wa jijiyar laka da tsokokin ɓarin fuskar atisaye domin ƙara musu ƙaimi da saurin farfaɗowa daga shanyewar da suka yi

Nassoshi 

1. Physiotherapy Hausa

2. Bell's palsy - Medscape

Post a Comment

0 Comments