Nankarwa ko kuma stretch marks a turanci, wani abu ne mai kama da ƙuraje da kan fitowa a fatar mutane, musamman mata, nankarwa ta kan zamo mai tsananin ƙaiƙayi ko zafi ne, sannan kuma mai wahalar warkewar saboda haɗakar abubuwa guda biyu:
(a). BubbuÉ—ewa da kumburin fatar wurin da nankarwar take.
(b). Kokarin warkewar da fatar wurin take yi.
Wata nankarwar kuma takan fito har ta daÉ—e a jikin mace ba tare da wani kaikayi ko ciwo ba, musamman irin nankarwar da ke fitowa mata a ciki bayan sunyi haihuwar farko.
Meke kawo fitowar nankarwa?
Nankarwa tafi fitowa mata a jikin su, musamman a damtsen hannuwa, ko jikin nonuwa, ko cinyoyi, ko ɗuwawu, ko, kwuiɓi, ko ciki, ko baya, ko sharaba, da dai sauransu.
Babban abin da yake kawo fitowar nankarwa shi ne yin ƙiba, ko juna biyu, ko ramewa. Ma'ana, idan mace ta yi ƙiba, sannan ta rame daga baya, toh, akwai yiwuwar nankarwa ta fito mata daga baya.
Idan mace ta samu juna biyu bayan ta haihu takan samu nankarwa a cikinta sakamakon bubbuÉ—ewa da talewar fatar cikin a lokacin da jariri ke girma a cikin, nankarwar tagi tsanani a haihuwar farko, kuma wasu takan zauna har iya tsawon rayuwarsu.
Hakanan kuma, idan nonuwan mace su ka bunƙasa suka girma a lokacin da take shayarwa, sannan, idan sun rage girma bayan ta daina shayarwar, toh, akwai yiwuwar nankarwa ta fito mata a nonuwan.
Bugu da ƙari, ramewa bayan yin ƙiba a sauran sassan jiki, bubbuɗewar fata a irin wannan zai haddasa yagewar zaren da yake haɗe tsakanin sassan fatar jiki (collagen) da kuma zaren da yake sanya fatar ta iya talewa (elastin).
Daga nan sai wannan abin ya haifar da tabo na nankarwa su fito ruÉ—u-ruÉ—u a jikin fata. Kuma tasirantuwar da fata keyi (skin response) ne ga waÉ—annan abubuwan, yake haddasa kumburi da kaikayi ko jin zafi a wurin nankarwar.
Meke kawo kaikayi, ciwo ko jin zafin nankarwa
Warkewa (healing ) daga yagewar fata wadda ke haifar da nankarwa, shima yana sanya jin kaikayi da kuma wahalar magancewar nankarwar, musamman idan mace tana yawan sosawa.
Idan ana yawan sosawa, jijiyoyin jini zasu rika bubbuɗewa (dilation) domin tura jini mai yawa zuwa nankarwar, haka kuma jakadun ƙwaƙwalwa da ke kan fata (nerve fibers) zasu tasirantu da wannan sosawar, sai ƙara ƙaimi wajen aikawa ƙwaƙwalwa sakon cewa zaren collagen da elastin na wurin sun yage, kuma akwai buƙatar su warke.
Toh, a lokacin da ƙwaƙwalwa ta bayar da umurnin warkewar wurin, kuma sabbin ƙwayoyin halittun fata (new skin cells) suke fitowa, wurin zai rika yin kaikayi.
Bugu da ƙari, bushewar fatar nankarwa (dryness of stretch marks), sakamakon rashin shafa mayukan samar da danshi (moisturizers) a wurin, shima yana haifar da jin ƙaiƙayi sosai. Sannan yana sanya nankarwa tayi ruɗu-ruɗu sosai, tayi wahalar warkewa.
Rashin kaurin fatar nankarwa (thinning skin structure of the stretch marks) shi ma yana haddasa jin ƙaiƙayi da wahalar warkewa. Ma'ana, idan nankarwa ta fito, toh, fatar wurin za ta zamo ba ta da kauri kamar yadda sauran fatar sassan jiki take, kuma hakan zai sanya jin kaikayi a wurin.
Bayan haka, rashin kaurin fatar zai sanya ta daÉ—e bata warke ba, musamman idan mace tana sosawa, ko kuma tana sanya matsattun tufafi suna yawan gugar wurin.
Nau'in kumburin da nankarwa ta haddasa, shi ma yana haifar da jinkirin warkewa ko kuma ƙaiƙayin. Ma'ana, wata nankarwa tana fin wata yin ruɗu-ruɗu a jiki. Don haka, gwargwadon tsananin ta, gwargwadon yanayin ƙaiƙayin ta da wahalar warkewar ta.
Yadda ake maganin nankarwa
Magungunan da ake yin amfani da su wajen maganin nankarwa, yawanci mayuka ne da sabulai masu samar da danshi a jikin fata. Sai kuma magungunan hana kumburi da ƙaiƙayin fata, waɗanda duk likita ne zai iya bayar wa a asibiti. Sannan yawanci magungunan suna rage tsananin ta ne kawai, amma basu gusar da ita gaba-ɗaya.
WalLahu A'lam
0 Comments