Ad Code

Ticker

6/recent/ticker-posts

Yadda Ake Bude Kwakwalwa Da Kara Kaifin Basira

Maganin kaifin basira


Yayin da zamani ke chanjawa cikin sauri inda ilmin kimiya da fasaha ke ci gaba da bankaɗo mana sauye-sauye a rayuwar ɗan adam ta yau da kullum. Ƙwaƙwalwar mu ta ɗan adam ba ta shirya gudanar da dukan ayyukan da muke yi a yanzu ba, kuma tana shiryawa ne a sannu - sannu.

Amma duk da haka muna samun daidaito a wannan zamanin, kuma muna sauya kanmu saboda irin sauye-sauyen da ake samu na yau da kullum.

Ƙwakwalwar mu ce ke tabbatar da wadannan al'amuran, domin ita ƙwaƙwalwa wani ɓangaren jiki ne da ke iya karbar sabbin abubuwa tare da haɓaka yanayin aikinta.

Yanzu abin tambaya a nan shi ne, ta yaya za mu iya kiyayewa da tabbatar da lafiyar wannan ɓangaren jiki mai ban al'ajabi? Shin akwai wata hanya da za mu iya ƙarfafa kwakwalwar mu tare da buɗe ta ko ƙara mata kaifi?

Wakiliyar BBC a fannin kimiyya da fasaha, Melissa Hogenboom ta yi nazari kan sabbin bincike-bincike kuma ta tattauna da wasu masana domin samun amsoshin wadannan tambayoyin.

Thorstein Barnhofer, farfesa ne kuma ƙwararre a fannin ilimin halayyar ɗan’adam a Jami'ar Surrey ta Ingila, ya shaida wa wakiliyar BBC Melissa cewa mu yan adam za mu iya ƙara ƙarfin ƙwaƙwalwar mu ta hanyoyi da yawa. "Akwai hanyoyin da ke rage damuwa a cikin 'yan makonni ƙalilan kuma suna habaka kaifin tunani ," in ji shi.

Ana iya guje wa cutuka kamar su cutar mantuwa lalacewar ƙwaƙwalwa ta hanyar habaka kaifin ta. Ba ma wannan kadai ba, ana iya rage dakushewar ƙwaƙwalwa sakamakon fuskantar munanan yanayi.” Hanyoyin da za'a bi domin bude ƙwaƙwalwar dan adam da kuma kara mata kaifi sun ƙunshi wadannan:

1. Faɗaɗa hanyoyin isar da saƙo a jikin dan’adam

‘Plasticity’ shi ne ikon da kwakwalwarmu ke da shi na sauya yanayin ta sakamakon bayanan da take samu daga waje ta hanyar jakadun ta.

Wani kwararre kuma masanin ilimin halayyar dan Adam Rajesh Pandey ya shaida wa wakilin BBC Adarsh Rathore a wata hira, cewa, a zahiri, ‘neuroplasticity’ shi ne haɗin gwiwa da ke samuwa da kuma canzawa a cikin jijiyoyi da ke cikin kwakwalwar mu, waɗanda ake kira ‘neurons’.

Ya ce, “Kwakwalwar mu na ƙunshe da abubuwa kamar wayoyin lantarki. Ta ƙunshi biliyoyin jijiyoyin ƙwaƙwalwa (Neurons) da ke isar da sakonni zuwa dukkanin ɓangarorin jiki, kamar su idanu, da kunnuwa da hanci da baki da kuma fata.

Ƙwaƙwalwa tana adana wannan bayani ne saboda haɗin kai da take samu tsakanin wadannan hanyoyi na ‘neurons’."

“A lokacin haihuwa alakar da ke tsakanin waɗannan jijiyoyin ba ta da yawa. Amma akwai dan ƙaramin haɗin kai a tsakaninsu, kamar lokacin da jariri zai janye hannunsa lokacin da ya taɓa abu mai zafi.

Amma jaririn zai iya jefa maciji a bakinsa, domin bai kammala samun irin wadannan bayanan ba, na cewa maciji na cutar wa.

Bayan haka, jarirai suna koyo a yayin da ake karin samun haɗin gwiwa tsakannin jijiyoyin.

Rajesh Pandey ya yi nuni da cewa alaƙar nan na canzawa a yayin da sabbin abubuwan ke gudana. Wannan tsari ana kiransa ‘neuroplasticity’.

Wannan aikin shi ne zai taimaka wa ɗan’adam wurin koyon abubuwa da gogewa da tattara abubuwan da za a tuna da su.

Farfesa Thorsten Barnhoff ya ce damuwa tana karuwa saboda yawan tunanin abubuw masu yawa a lokaci daya.

Haka zalika, ya ce yin tunani iri ɗaya akai-akai yana da lahani ga ƙwaƙwalwa, saboda yana ƙara haɓaka sinadarin ‘cortisol’.

Wannan sinadari na cortisol yana cutar da ƙwaƙwalwa kuma yana rage mata kaifi.

Akwai hanyoyin da za a kauce wa wannan - wadanda suka ƙunshi kiyayewa. ‘Kiyayewa’ a nan na nufin sanin abubuwan da ke kewaye da mutum, da tunanin sa da kuma hankalin sa.

Wato maimakon yin tunani da yawa, ku samu wani abu da zaku yi a duk lokacin da kuka ji wannan tunani ya bijiro muku.

Ƙwararren masanin ilimin halayyar dan adam Rajesh Pandey ya ci gaba da cewa, "A sauƙaƙe ‘kiyayewa’, na nufin sanin bayanan da ke shigowa cikin ƙwaƙwalwa daga waje da kuma yadda ake amfani da bayanan da ake tattarawa." Ya ce, “A taƙaice, tsari ne na mai da hankali ga gabobi.

Mai da hankali kan gabobi kamar numfashin ku, da kuma ƙamshi da sautunan da ke kewaye da ku.

“Za ku ga idan mutum ya mai da hankalinsa kan waɗannan gabobin na tsawon mintuna 15 a rana, ayyukansa kamar tafiya, da magana da dariya da murmushi za su canza baki daya.”

2. Rage damuwa

Kwanan nan an gano cewa tsarin ƙwaƙwalwa kuma yana canzawa yayin da kaifin ta ke ƙaruwa.

Don tabbatar da wannan zancen, Melissa Hogenboom ta ɗauki hoton ƙwaƙwalwarta da na’ura, bayan ta yi tunani cikin natsuwa na tsawon sati shida sannan ta sake ɗaukar wani hoton.

Bayan ta kwatanta hotunan biyu da ta dauka, Farfesa Barnhofer ya ce kaifin ƙwaƙwalwar Melissa ya ƙaru a cikin sati shida.

Farfesa ya ce, “Girman wani ɓangaren ƙwaƙwalwa da ake kira amygdala ya ragu ta gefensa na dama.

Wannan ya faru ne saboda raguwar damuwa, saboda mutanen da ke cikin matuƙar damuwa, wannan ɓangaren yakan ƙara girma.

Mun gani a baya cewa horar da ƙwaƙwalwa da tunani yakan sauya wannan ɓangaren.

A lokaci guda kuma, an sami canji a bayan ƙwaƙwalwa. Wannan yana nufin cewa yanayin yawan tunani ya ragu.”

3. Motsa jiki

A cewar masana, motsa jiki shi ma na iya taka muhimmiyar rawa wajen haɓaka kaifin ƙwaƙwalwa.

A cewar Farfesa Angele Quattrone, daraktan cibiyar 'Centro Neurolesi' ta Italiya, motsa jiki na mintuna 30 a rana na tsawon kwanaki 4 zuwa 5 a mako yana da amfani sosai ga ƙwaƙwalwa.

Gillian Forrester, Farfesa a Jami'ar Sussex, ya ce canje-canje a cikin ƙwaƙwalwa na da alaƙa da yawan motsa jiki.

Ya ce, “Mun gano cewa idan ɗan Adam yana da matsalar magana, mutumin zai iya yin magana ta hanyar kwatantawa da hannunsa.

A haƙiƙa, ɓangaren ƙwaƙwalwarmu da ke taimaka mana wurin magana yana da alaƙa da motsi, wato, ɓangaren da ke taimaka mana aiki da hannu, da ƙafa ko kafaɗu.

Watakila wannan saboda harshe ya samo asali ne ta hanyar kwatantawa (kamar maganar Kurame)."

4. Koyon sabon abu

Baya ga zurfafa tunani cikin natsuwa, motsa jiki na iya rage damuwa, in ji Dokta Ori Osami a Makarantar Ilimin halayyar dan’adam wadda ke Birkbeck, Jami'ar London.

Ya ce, “Kwakwalwarmu kullum tana canja kanta. Amma a cikin yara wannan tsari yafi faruwa da sauri.

An lura cewa jariran da ke motsa hannayensu da ƙafafu a cikin sauri, za su iya magana da kyau fiye da takwarorin su da basa yi. 

Haka kuma, a cikin waɗanda ba sa yin hakan, wasu na iya samun matsala daga baya na magana ko zamantakewa.”

Masanin ilimin halayyar ɗan'adam Rajesh Pandey ya ce yin wani sabon abu kamar koyon kaɗe-kaɗe ko yare, ba motsa jiki kaɗai ba, na iya ƙara kaifin ƙwaƙwalwa.

Domin ana samun karuwar sabbin hanyoyin sadarwa a cikin ƙwaƙwalwa idan muna gani, ko koyon sabbin abubuwa ko tunani game da wani abu.

Ya ce, “Ƙwaƙwalwar ɗan'adam na iya koyon sabon abu har tsawon rayuwa, za mu iya koyon sabon harshe ko da muna da shekaru 90 ne.

Haka kuma, zuwa sababbin wurare, da gudanar da abubuwa saɓannin na yau da kullum na da nasu alfanun.’’

Cibiyar 'Centro Neurolesi' ta Italiya tana taimaka wa marasa lafiya da ke fama da matsalolin ƙwaƙwalwa ta hanyar amfani da fasahar zamani.

Daraktan wannan cibiya, Farfesa Angel Quattro, ya ce an ƙirƙiro wani wasa na musamman ga mutanen da ba sa iya tafiya da kansu.

Wannan yana ƙara kaifin ƙwaƙwalwa kuma yana ba da damar sake jadadda haɗin gwiwa tsakanin ɓangarorin ƙwaƙwalwa da suka samu matsala sakamakon haɗari ko shanyewar ɓangaren jiki. Wannan shi ake kira ‘rewiring’ a likitanci.

Har zuwa yanzu, an yi tunanin cewa ‘neuroplasticity’ ya fi yawa a cikin yara ne, amma yanzu ana amfani da shi a manya a duniya domin tabbatar da aikin ƙwaƙwalwa da kuma rage lalacewarta.

Zoe Kortji, farfesa a fannin ilimin halayyar dan’dam a Jami'ar Cambridge, ta ce ƙwaƙwalwar kowane dan adam na da nasa tsarin.

Ta shaida wa Melissa Hogenboom, “Ƙwaƙwalwar kowa tana aiki a cikin salon ta.

''Idan mutum ya fahimci yadda ƙwaƙwalwarsa ke aiki, za a iya inganta koyar da shi da kuma haɓaka ƙwaƙwalwar.”

Wani gwaji da aka yi a jami’ar kwararru ta Cambridge ya buƙaci mutane su amsa wasu ‘yan tambayoyi.

Daga baya sai aka auna ƙididdigar yadda ƙwaƙwalwar su ke yin aiki, haka nan idan aka yi tambaya bisa ga wannan salon, mutum zai iya ba da amsa da kyau.

Wannan binciken har yanzu yana kan matakin farko, kuma ana fatan nan gaba za a iya koya wa mutane yadda ƙwaƙwalwar su ke yin aiki, wanda zai taimaka wurin inganta kaifin kwakwalwar ta su.

Print this post

Post a Comment

0 Comments