Ad Code

Ticker

6/recent/ticker-posts

Tambayoyi Da Amsa Akan Karin Mahaifa (Fibroid), Cutar Sanyin PID Da Yawan Barin Ciki

Mene ne Cutar Fibroid (Ƙarin Mahaifa)?

Cutar fibroid (ƙarin mahaifa ko ƙullutun mahaifa) cuta ne da ke sanya wani sashe na naman mahaifa ya kumbura ya dunƙule ya zama ƙari ko ƙullutu sannan ya ci gaba da tsiro yana girma a hakan. Tsiron fibroid duk da wani sa'ilin yana girma sosai, ba tsiron ciwon daji bane, ma'ana, ba cancer ba ne kuma baya zama cancer daga baya.

Mata dayawa suna da wannan tsiron a mahaifar su sai dai wasu baza su taba ganewa ba saboda nasu fibroid din ƙarami ne kuma baya basu matsalar komai.

Karin mahaifa

Meke Kawo Cutar Karin Mahaifa (Fibroid)?

Har ila yanzu ba'a san takamaiman asalin me ke kawo cutar fibroid ba. Amma masana sun alaƙanta cutar fibroid da hauhawar sinadaran hormones na mata watau estrogen da progesterone. Bisa ga wannan masana sun ayyana wasu abubuwan hatsari da kan iya sa mace ta samu cutar fibroid a mahaifarta. Matan da ke da wadannan abubuwan hatsari su ne suka fi kowa samun cutar fibroid. Abubuwan hatsarin su ne kamar haka:

1. Gado; Macen da mamar ta ko cikin ƙannen ta ko yayyun ta akwai masu dauke da cutar fibroid

2. Mace mai kiba

3. Macen da tayi saurin fara al'ada (ta fara kamin ta kai shekaru 13)

4. Macen da ta wuce shekaru 45 amma bata daina yin al'ada ba

5. Mace mai shan barasa ko sigari

6. Matan Afrika sun fi turawa samun cutar fibroid

Wa Zai Iya Samun Karin Mahaifa Fibroid)?

Wadannan abubuwan hatsari suna nuna cewa mace tana iya kamuwa da cutar fibroid, amma ba dole bane kuma sai ta kamu da cutar ba. Haka kuma akwai wasu matan da basu ɗauke da ko ɗaya daga cikin wadannan abubuwan hatsari amma kuma suna iya samun cutar fibroid.

Mene ne Alamomin Fibroid?

Mafi akasari fibroid baya nuna alamar komai ko da yana ƙunshe dayawa a cikin mahaifar mace, wasu mata ma har su gama rayuwar su ba za su gane suna da ba. Wasu kuma ana ganin shi ne kwatsam a lokacin da ake yiwa mace hoton awon ciki.

Amma duk da haka wasu fibroid suna ba da alamomi, suna sanya mata matsaloli kamar haka:

1. Zubar jinin al'ada dayawa har ya wuce kwanaki takwas (Wannan ita ce babbar alamar fibroid). Wani lokaci al'adan yakan zo wa mace da matsanancin ciwo kuma zai dade bai dauke ba ko kuma ya dinga zuba da ƙarfi har na wasu kwanaki.

2. Rikicewar jinin al'ada

3. Yawan yin fitsari

4. Girman ciki: Wannan ya danganta da girman fibroid da kuma yawan su. Wani fibroid yakan tsiro ya girma sosai, har ma mace ta dauka ciki ne ta samu. Wani fibroid ma yakan fi cikin da yakai watanni 9 girma.

5. Alamomin ƙarancin jini, saboda fibroid yana sa wa mace ƙarancin jini ta hanyar yawan zubar jini da yake saka ta a lokacin jinin al'ada.

Yadda ake gane cutar fibroid

Ana gane cutar fibroid ne ta hanyar yin abdomino-pelvic utrasound, ma'ana hoton kayan ciki da na'ura mai amfani da sauti. A cikin wannan hoton za'a ga mahaifar mace da duk abin da ke cikin ta, idan akwai fibroids za'a iya ganin su da auna girman su da ƙirga yawan su da kuma muhallin da suka tsiro a cikin mahaifa.

Maganin Cutar Fibroid

Mafi akasari a asibiti cutar fibroid ba'a fara maganin ta sai in fibroid din na kawowa mace wata matsala, kamar irin alamomin da muka zayyana a baya. Ma'ana ko da an gane mace na ɗauke da fibroid in dai baya ba ta wani matsala to ba'a bada maganin komai.

Amma idan yana kawo wa mace rikicewar al'ada ana iya bata maganin daidaita al'ada. 

Idan girma yake ana iya ba ta maganin da zai hanashi ƙara girma da dai sauransu.

Amma waɗannan duk magunguna ne kawai na wuccin gadi, takamaiman maganin cutar fibroid shi ne ayi aikin tiyata a cire ƙarin ko ƙullutun da ya tsiro yake girma a cikin mahaifa ko ma a cire mahaifar baki daya idan mace bata da buƙatar sake haihuwa.

***

Shin Alluran Gentamicin Yana Maganin PID?

Alluran gentamicin a kowane irin ciwo da akeyin amfani da ita ba'a so a wuce na kwanaki biyar saboda illolin da take iya haifar wa ga koda da kuma jin dan adam👂🏼

Duk da cewa gentamicin antibiotic ne mai kyau, baya cikin magungunan da ake amfani da su wajen maganin pid. Baya cikin magungunan da FDA tayi approving domin treatment na pid.

Dukkan magungunan da ake amfani da su munyi bayanin su dalla dallah a cikin wancan rubutun da na turo a baya.

A lura a daina shan magungunan ba akan tsari ba, saboda kowane magani yana da wata illah da yake iya haifar wa. A tabbata duk maganin da za ayi amfani da shi to likita ne ya bayar.

***

Wane Irin Infection Ke Sa Zazzabi Har Na Tsawon Makonni Biyar?

Cututtuka da ke kawo zazzabi sunfi miliyan talatin, ba wanda zai gane wane irin cuta ke damun marar lafiya ta hanyar zazzaɓi kawai. 

In fact a likitanci zazzabi yana cikin alamomin da ake kira da "non specific symptoms" ma'ana alamomin da basu nuna takamaiman ko wane irin cuta ke damun marar lafiya.

Abubuwan da zazzabi yake nunawa su ne

1. Kwayoyin cuta sunyi nasarar shiga a jikin dan Adam haka kuma garkuwar jikinsa tana kokarin fada da ƙwayoyin.

2. Akwai wata damuwa dake bukatar kulawar gaggawa a jikin mutum

***

Me Ke Kawo Wa Mata Yawan Bari Kuma Ya Ake Maganin Yawan Zubewar Ciki?

Abubuwan da ke kawo yawan bari suna da matukar yawa gaskiya. Gane takamaiman abinda ke kawo yawan bari ya danganta da lokacin da mace ke yawan barin.

Misali wasu suna yawan bari ne a lokacin da cikin yake karami kamin ya kai watanni uku, wasu kuma sai cikin ya tasa, wasu ma sai cikin yakai wata bakwai ko ya wuce sannan su ke yawan bari. Toh duk wadannan akwai abubuwa daban daban da ke kawo bari a kowane lokaci.

Anan al'ummar mu ta Nigeria da sauran kananan kasashe, vaginal infections, ma'ana cututtukan infections na al'aura suna kan gaba cikin abubuwan da ke kawo wa matan mu yawan bari. Amma a gaskiya gane takamaiman abinda ke kawowa mace yawan bari sai an je asibiti anyi gwaje-gwaje.

***

Me Ke Kawo Yawan Barin Ciki Kamin Yakai Watanni Uku

Abubuwa uku sune kan gaba wajen kawo yawan bari a wannan lokaci su ne:

1. Chromosomal abnormalities: Wannan matsaloli ne dangane da tantanin halittar jaririn da ke cikin ciki. Akwai wasu matsaloli da kan iya faruwa a lokacin da tantanin halittun uwa suke haduwa da na uba domin halittar jariri, idan waɗannan matsaloli sun auku, mafi yawanci yaron bazai iya rayuwa ba, hakan yakan sa cikin ya zube. Wasu abnormalities kuma 'they're compatible with life' ma'ana yaron zai iya rayuwa, so cikin yakan dorewa ba zai zube ba amma ana iya haihuwar yaron da wata nakasa.

2. Congenital abnormality of female genital tract: Wannan yana nufin akwai wasu matsaloli da aka haifi mace da ita a mahaifa ko a wani sashe na al'aurarta da ke hana  mahaifarta iya rike ciki.

3. Vaginal infections: Cututtukan infections na al'aura kamar yadda mukay bayani a baya.

4. Haka kuma akwai wani cuta da ake cema anti-phospholipid syndrome, ita ma tana yawan kawo bari a wannan lokaci. Ita wannan cutar takan sa mace tayi producing wasu sojojin garkuwan jiki da zasu je suyi fada da cikin su ƙwamushe cikin ya zube.

***

Shin ko cutar Pneumonia na sanya warin numfashi?

Pneumonia kan iya sanya warin numfashi a lokacin da ta ta'azzara har ta haifar da maruru a cikin huhu, complication din da muke cewa lung abscess. 

Munyi bayani akan warin numfashi a cikin wannan rubutu Bayani game da warin baki da kuma yadda ake maganin sa

Zaku iya shiga WhatsApp group dinmu domin turo mana naku tambayoyi ta hanyar danna hoton WhatsApp da ke hannuku na hagu a ƙasa.

Print this post

Post a Comment

0 Comments