Tambayoyi da Amsa a WhatsApp group namu ranar Lahadi 2/6/2024

1. Tambaya

Likita inada tambaya, wane magani zanyi amfani dashi wurin tsaida haihuwa baki daya

Amsa

 Jama'a me yasa kuke bullying din wata mata saboda ta yi tambaya, ya kamata mutane su gane, a rayuwa kowa da irin tasa matsala. Abinda wani ke nema wani matsala ne a gare shi, saboda haka tsangwamar wani don ya fadi damuwarsa ba dai dai bane a wannan group. Shi yasa muka ce bamu son fira ko gaishe-gaishe ko maganganu maras muhimmanci idan an bude.

Yar uwa zan amsa miki tambayar duk da kin goge, sbd naga tmnbyr sakamakon replies din da aka miki. Kuma nasan ba a son ranki kika goge ba.

Akwai hanyoyin daina haihuwa ga mata baki daya, ma'ana permanent methods of contraception kamar haka:

1. Ɗaure hanyoyin ƙwai guda biyu, abinda ake kira da BTL

2. Cire mahaifa, watau hysterectomy

Wadannan duka biyun sai anyi aikin tiyata.

Toh shawara a nan gareki shi ne, idan har kina son kara haihuwa daya, daga nan sai ki daina kwata-kwata, zaki iya samun ciki yanzu amma idan kinje haihuwa sai ayi miki aikin CS tare da ɗaya daga cikin wadancan hanyoyi da na ambata. Ma'ana sai a cire yaron sannan a ɗaure hanyoyin ƙwai ko kuma a cire mahaifar baki daya.

Idan kuma bakida bukatar sake haihuwa baki daya a yanzu toh zaki iya tafiya ayi miki daya daga cikin wadancan ayyukan.

Ko kuma abu mafi sauki shi ne kije a saka miki robar hana haihuwa ta cikin mahaifa (IUD). Wannan ba sai anyi aikin tiyata ba, ana iya sakawa a ɗaƙin likita cikn yan mintuna. Kuma tana da inganci sosai wajen hana haihuwa, wata takan ɗauki shekaru goma tana aiki. Sai dai ita wannan ba hanya ce ta har abada ba, ma'ana idan kin cire robar daga baya zaki iya samun ciki in shekarunki ba su wuce hakan ba.

So idan har zaki yi amfani da wannan hanyar dole duk bayan shekaru biyar zuwa goma zaki je a sabunta miki wannan robar mahaifa.

2. Tambaya

Assalamu Alaikum likita an tashi lafiya idan an daure hanyoyin kwai guda 2 in ana son asake haihuwa za'a iya bude su?

Amsa

Aa wannan hanya ce ta hana haihuwa ta dim dim dim, ba'a warwarewa. Amma duk da haka wasu ƙasashe da suka cigaba an ruwaito cewa akwai yadda suke domin gyara wadannan hanyoyin daga baya daga baya idan mace na bukatar sake haihuwa, shima wannan ya danganta da irin daurin da aka yi.

3. Tambaya

Assalama'alaikum.

Masha Allah.

Doctor barkan da Rana.

Haihuwa baiwace daga Allah subuhanahu wata'alah!👏🏻. Allah ya bamu masu albarka🤲🏻. Amman doctor yau wata uku ke nan da yin aure na.

Dan Allah Ina son doctor ya Dan bani shawara agame da yayin abinci ko shawara agame da samun ciki.

Allah ya Kara wa doctor lafiya da Imani da rayuwa Mai albarka 🤲🏻

Amsa 

Ka karanta wannan rubutun:

https://www.lafiyata.com.ng/2023/02/bayani-game-da-yadda-mace-zata-gane.html?m=1

4. Tambaya

Don mene ne maganin PID? Wllhi doctor haryanxu nasha magungunan da alluran amma ina fama dashi, please ko akwai wata hanyar?

Amsa

Baki kiyaye sauran abubuwan ba shi yasa. PID dole sai kinyi treating partner dinki, sannan zai wuce. Saboda ko kinsha magani kin ji sauki idan partner dinki bai warke ba toh zai kara liƙa miki.

A cikin rubutun da nayi, nayi bayanin cewa, matan da suke su biyu ko uku ko ma su hudu ga mijin su, idan aka samu daya da cutar PID, to da su da mijin dukkan su dole sai kowa yayi treating din PID yadda ya kamata completely, ko da mace daya ce kawai ta fara nuna alamun sa. Yin haka shi kadai zai sa PID ya bar gidan.

5. Tambaya

Dr meyake kawowa mutum ya rinka jin jiri yana daukansa?

Amsa

Ƙarancin jini shi ne yafi kawowa matan al'ummar mu jiri, sauran abubuwa sun hada da:

1. Ƙarancin ruwan jiki, musamman wanda yayi fama da amai da gudawa.

2. Low BP da kuma

3. Wasu magunguna

6. Tambaya

Aslm alkum Dr inamaku fatan alkairi wata yar uwata ce kwanaki tayi rashin lfy zawo da amai se Aka riketa likita se Akace cemata kodarta tanaso tasamu matsala to bayan an sakota seta gane cewa kulun setasha maganin ciwan jiki amma kuma batashan ruwa diyawa to setaci gaba da shan ruwa diyawa sosai to yanzu bayan wata hudu setaje Aka aunata akacemata ai kodarta lfya klau suke ,se Abu yabata mamaki se kuma ta saké wani asibiti nan ma Akace lfy kalau seda taje asuciti uku kuma pvt ce Aka Auna akace lfy kalau kodarta take

Shine muke tanbaya daman ana samun hakan dafarko Ance kodar tanaso tasamu matsala tacigaba da shan ruwa sosai an Auna Ance kuma lfy kalau suke.

Amsa

Eh ana samun haka sosai, akwai abinda ake cema AKI (Acute Kidney Injury), ciwon koda ne, wanda gudawa da aman da tayi da kuma yawan shan magungunan ciwon jiki duk zasu iya kawo mata shi. Shi wannan ciwon kodar na AKI idan anyi saurin gane shi aka ɗauki matakin da ya dace, toh koda ta kan farfado taci gaba da ayyukan ta kamar kullum ba tare da wani tangarda ba. Amma idan ba'a yi saurin ganewa ko daukar mataki ba toh yakan iya lalata kodar baki daya. 

7. Tambaya

Assalm Alykm, Dr Allah ya qarama basira, dun Allah meke kawo ciwon tsara, (Kunkukuru) ko ace baya.

Amsa

Abubuwan da ke kawo ciwon tsara sun danganta da

1. Aikin da kake yi na karfi

2. Shekarunka

3. Wasu cutuka kamar ciwon suga.

4. Da kuma ko ka taba jin ciwo a baya, ko samun hatsari, ko faɗuwar da ta sa bayanka ya bugu.

Shawara shi ne kaje asibiti a bincika miye asalin abinda ya kawo maka ciwon domin a dora ka akan maganin da ya dace. Kar ka dade kana shan magungunan rage ciwo bakaje asibiti ba, ka lura da tambayar da wata ta aiko dake sama a kan illolin su.

8. Tambaya 

Masha Allah, nagode sosai Allah ya saka da alkhairi,don Allah miye Ingancin fibrozin activated complex wajen maganin fibroid, ragewa kawai yake ko zai iya tafiyar dashi, sannan kma mai ciki zata iya sha?

Amsa

Baya tafiyar dashi baki daya, ba maganin da ke tafiyar da fibroid baki daya. Amma wadanda suka ƙirƙiri maganin sunyi iƙrarin cewa yana rage girman fibroid da kuma daidaita wa mace sinadaran hormones dinta a cikin jini. Kuma a gsky bansan safety din shi ba a pregnancy. Saboda natural product ne da yakeda supplement dayawa.

9. Tambaya 

Aslm Alkm doctor sannu da qoqari nace dan Allah akwai maganin da zansha na ciwon haure ,nasha magunguna da dama irinsu amoxicillin,Brustan N , flagyl, meloxicam protech,omeprazole,diclofenac. amma duk sai ahankali, ada innasha inasamun relief amma ynz basayimin aiki ko nasha sai dai inyita wahala har Allah yakawo min sauqi,ngd🙏

Amsa

Ane asibiti a bincika, a ga likitan hakori.

10. Doktor Amin bayani akan  detol dakuma amfaninsa wajen basir mai tsiro Dan Allah.

Amsa

Dettol antiseptic ne, ma'ana maganin kashe ƙwayoyin cuta. Zaka iya sanya shi cikin ruwan da zakayi gashi, amma dai kasani ba shi keda amfani ba, gishiri ne mafi amfani wajen gashin basir mai tsiro.

11. Tambaya

Dr barka da wuni muna godiya sosai da qoqari Allah ya cika a mizanin lada dan Allah dr miki sa mace taji batada shaawa kokadan gatanan qyamas. 

Amsa

Rashin sha'awa ga mace ya danganta da

1. Shekarunta

2. Daidaituwar sinadaran sex hormones a ke cikin jini.

3. Mood din da take akai, kamar, yanayin yawan damuwa ko depression.

Idan muka fara da shekaru, sha'awar dan adam tana fara raguwa sannu sannu daga ya kai shekaru 30 zuwa sama, raguwar sha'awar ya danganta daga wani mutum zuwa wani. Shi yasa mata da suka kai 45 ko lokacin ɗaukewar al'ada basu samun wani sha'awa.

Wasu lokuta mata suna samun ƙarancin sinadaran sex hormones a cikin jininsu. Wannan shi ma yakan rage musu sha'awa sosai, kamar matar da bata dade da haihuwa ba. Ɗaukewar hormones of pregnancy yakan kawo mata ɗaukewar sha'awa na wani dan lokaci 

Shiga yanayin damuwa shima yana interfering da level din hormones kuma yana ragewa mace sha'awa

Da karshe kuma amfani da wasu magungunan bada tazarar iyali suma suna kawo haka.

Wadannan sune suka fi kawowa mace wannan yanayi

Tambaya 

12. Assalamu Alaikum Doctor pls inaneman Karin bayani ance in ancirena mutum mahaifa bazai Kara yin period ba bale haihuwa. Yarayana biyu akaciremin mahaifa Shine nake Neman Karin bayani.

Amsa

Lallai haka ne, ai period din daga mahaifa yake zuwa, to an cire mahaifar ina maganar period? Though bansan dalilin da ya sa aka cire miki mahaifa ba. Amma maganar haihuwa shikenan gaskiya.

13. Tambaya

Please Duk don Allah Menene maganin Uric acid , ina fama da tsukun kashi da kafafu, Wanne calcium da uric ne. Sannan Idan üric din yayi daidai kafar zata daina ciwon. 

Amsa

Akwai magungunan rage uric acid daban daban, amma yafi kyau a san level din hauhawar uric acid dinka kafin a dora ka akai, wannan shi zai ba likitan da ke ganin ka damar sanin yadda zai dora ka akan magani. 

14. Tambaya

Aslm alkm Dr maiyake kawowa yin period sau biyu a Month

Amsa

Yin period ya danganta daga wata mace zuwa wata. Amma normal interval tsakanin daga ɗaukewar period kamin ya sake dawowa kwanaki 21 zuwa 35 ne. Idan yayi ƙasa da haka shine za'a ce may be akwai matsala. Idan yayi ƙasa da 21 days ko yafi 35 days shi ne za ace rikicewar al'ada. Munyi bayani sosai akan rikicewar da kuma abubuwan da ke kawowa.

https://www.lafiyata.com.ng/2023/01/rikicewar-alada-jinin-haila-da-kuma.html

15.  Tambaya

Doktor barka da yau allah yasaka da alkhairi don allah meke zafin jiki mai tsanani.

Amsa

Akwai abubuwa dayawa dake kawo zafin jiki. Zafin jiki mai tsanani ba alama ce dake nuna takamaiman wani ciwo ba. Alama ce da ke nuna cewa akwai wata matsala ko wasu ƙwayoyin cuta a cikin jinin mutum da ke buƙatar kulawa. Saboda haka aje asibiti.

16. Aslm dr sannu da qoqari don ina neman qarin bayani dr ina amfani da maganin qwayoyi wanda ake sha kullum wajen tsarin iyali Shin dr wannan magani yana da illa???

Amsa

Hanyoyin tsarin iyali, ko wace mace da irin wanda ke karɓar ta, wasu ƙwayoyi, wasu allura, wasu tsinke ko ashanar hannu wasu robar mahaifa. Dukkaninsu suna iya sanyawa wasu mata side effects, kamr zubar jini ba tsari, yin ƙiba da dai sauransu. Amma wadannan side effects din bakomi bane idan akayi la'akari da amfanin da suke yiwa mutum. Kuma mafi yawancin side effects din sukan daina idan mace ta daina amfani dasu. Saboda haka idan har ƙwayoyin suka karbe ki, ki cigaba kawai ba matsala.

Kammalawa 

Zaku iya shiga WhatsApp group dinmu domin turo mana naku tambayoyi ta hanyar danna hoton WhatsApp da ke hannuku na hagu a ƙasa. Idan kuma group din yana kulle zaku iya turo mana tambayoyin ku ta private message.

Post a Comment

0 Comments