Ad Code

Ticker

6/recent/ticker-posts

YADDA MACE ZATA GANE TANADA CIKI (HOW WOULD YOU KNOW YOU ARE PREGNANT?)

Gabatarwa:

Shin kina tsammanin kina da ciki? Haƙiƙanin tabbatarwa sai anyi gwajin ciki. Amma kafin ayi gwajin ciki akwai wasu alamomi da idan mace ta gansu suna ƙara ƙarfafa mata gwiwa da kuma kyautata mata zaton lallai tanada ciki. Yawancin waɗannan alamomin ba su keɓanta ga ciki ba.  Wasu na iya nuna cewa rashin lafiya yana batun kama mace ko kuma jinin hailarta ya kusa farawa.  Haka kuma, wata mace zata iya samun ciki ba tare da fuskantar yawancin waɗannan alamomin ba.


Alamomin shigar ciki a jikin mace 

 Manya-manyan alamomin farko da kan iya nuna mace ta ɗauki ciki sune kamar haka;

1. Rashin zuwan jinin al'ada

Idan mace na cikin shekarun haihuwa kuma mako guda ko fiye ya wuce ba tare da ta ga jinin hailar da take tsammani ba, zai iya yiwuwa ta samu ciki. Wannan ita ce babbar alamar ɗaukar ciki, amma duk da haka, wannan alamar na iya zama mai rikitarwa idan dama mace na fama da rikicin al'ada.

 2. Kumburar nono da ciwo kaɗan idan an taɓa

Canje-canje na sinadaran hormones a farkon ciki na iya sa nonuwan mace su kumbura, su ƙara jin taɓi kuma da ciwo kaɗan idan an taɓa. Jikin mace zai saba da wannan canje-canjen bayan cikin ya fara girma, don haka, nonuwan mace zasu dawo lafiya lau.

3. Yawan tashin zuciya ko amai 

Yawan tashin zuciya a farkon ciki ana kiran shi morning sickness da turanci saboda yafi faruwa da safe. Toh amma zai iya faruwa a kowane lokaci na yini ko dare, sau da yawa yana farawa cikin wata ɗaya zuwa biyu bayan mace ta sami ciki.  Duk da cewa, mafiyawanci mata suna jin yawan tashin zuciya a farkon samun ciki amma wasu kuma ba su taɓa samun tashin zuciya a lokacin da suke da ciki.  

4. Yawan fitsari

 Mace zata iya samun kanta tana yawan fitsari fiye da yadda ta saba.  Wannan ya samo asali ne saboda yawan jini a jikin mace yana ƙaruwa lokacin da ta dauki ciki, hakan yana haifar da kodar mace ta samar da fitsari mai yawa.

5. Kasala da yawan gajiya

Yawan gajiya yana ɗaya daga cikin manyan-manyan alamomin ɗaukar ciki. Bayan yawan gajiya, mata masu ɗanyen ciki suna fama da yawan bacci. Duk da cewa har yanzu masana basu gano takamaiman abinda ke sa mata yawan bacci a farkon ciki ba, amma mafi rinjaye suna alaƙanta shi da hauhawar sinadarin progesterone a lokacin da mace ta ɗauki ciki

Waɗannan alamomi biyar da muka lissafa a sama sune manyan alamomin da ke nuna mace wadda tayi jima'i ta samu dacewa da samun ciki. Haka zalika, mace zata iya fuskantar wasu ƙananan alamomi kamar haka:

Alamomin shigar ciki a satin farko

Shigar ciki a sati na daya bai faye nuna alamomin komai ba, idan ma ya nuna, to mafiyawanci alamomi ne da basu keɓanci shigar ciki ba.
 1. Yawan ɓacin rai: wannan yana faruwa ne saboda canje-canjen sinadaran hormones da ke faruwa a lokacin da mace ta ɗauki ciki. Watarana mace kan iya yin har kuka ba tare da anyi mata komai ba
 2. Yawan kumburin ciki idan mace taci abinci da kuma fitar da iska
 3. Zuwan wani jini ɗan kaɗan daga gaban mace. Wannan jinin wasu mata sukan ɗauka kamar al'ada ne, toh amma suna da bambanci sosai da jinin al'ada saboda bai kai jinin al'ada yawa ba kuma jinin al'ada yafi duhu da wari.
 4. Ciwon mara matsakaici
 5. Yawan jin ƙamshi ko warin abubuwa, ƙamshin wasu abubuwa yakan iya sa mace tayi amai
 6. Rashin jindaɗin abinci
 7. Ko kuma kwaɗayin wasu irin abinci
 8. Yawan toshewar hanci
 9. Yawan zazzaɓi ko ciwon kai
 10. Yawan taruwar yawu a baki
 11. Yawan toshewar hanci
 12. Fitar ƙuraje a fuska

Hanyoyin da mace zata gane tanada ciki

Dafarko idan mace tasan cewa lallai ta sadu da namiji ba tare da wata robar kariya ba kuma ta fara jin wasu alamomin da muka ambata a sama toh lallai dole ta fara zargin cewa ta samu ciki. Hanyoyin da zata bi ta tabbatar sune kamar haka:
 1. Mace zata iya fara yin awon ciki na fitsari tun a gida. Idan sakamakon ya nuna akwai ko babu sai taje asibiti ayi mata awon ciki na jini.
 2. Idan anga sakamakon awon ciki na  jini ya nuna akwai ciki toh sai aje ayi hoton ultrasound domin tabbatar da cikin da aka samu da lafiyarshi
 3. A ƙa'idar ilimin likitanci, ana tabbatar da cewa mace tana da ciki ne kawai idan anyi hoton ultrasound anga cikin acikin mahaifarta.

Kammalawa

A cikin wannan rubutu munga alamomi daban daban da ke nuna cewa mace tanada ciki. Haka kuma munga cewa waɗannan alamomin su kaɗai basu iya wadatarwa wajen tabbatar da mace tana da ciki har sai anje anyi hoton mahaifa anga ciki acikin mahaifarta.

Idan kuna da tambaya sai kuyi a cikin akwatin sharhi dake ƙasa, Insha Allah zamu karba ba tare da jinkiri ba. Haka kuma zaku iya shiga group dinmu na WhatsApp domin kasancewa damu damu a koda yaushe da kuma samun ingantattun bayanan mu a cikin sauki. Ku danna wannan domin shiga: Lafiyata Group 3. 
Print this post

Post a Comment

0 Comments