Ad Code

Ticker

6/recent/ticker-posts

Matsanancin laulayi a farkon samun ciki da kuma yadda ake maganinsa (Hyperemesis gravidarum)

Gabatarwa:

Mafi yawancin mata suna fuskantar yanayin laulayi a lokacin da suke ɗauke da juna biyu. A wasu lokuta laulayi shi ne alama ta farko da wata mace zata fara gane tana ɗauke da ciki tun kamin tayi ɓatan wata. 

Matsanancin laulayi yafi damuwar mata waɗanda suke ɗauke da cikinsu na farko da kuma mata waɗanda suka ɗauki ciki suna da ƙananan shekaru koda ba shi ne cikin su na farko ba. A cikin wannan rubutu zamuyi bayani dallah-dallah game da laulayi da kuma hanyoyin da ake bi domin maganin sa a ilmin kimiyya na likitanci.




Mene ne matsanancin laulayi?

Laulayi shi ne amai da tashin zuciya wanda bayada alaƙa da wata cuta da ke faruwa a lokacin da mace take ɗauke da ciki. Laulayin da ba mai tsanani ba ana kiransa da morning sickness a turance, kuma yana daya daga cikin alamomin daukar ciki.

Likitoci masu ƙwarewa ta musamman a fannin kiwon lafiyar mata masu ciki da kuma ɗaukacin al'aurar mata sun fassara matsanancin laulayi da rashin lafiya mai haifar da mummunan tashin zuciya da amai ga mata masu sabon ciki wanda baya da dangantaka da wata cuta wanda kuma zai iya sanadiyyar ƙarancin ruwan jiki ko kuma samun sinadaran ketones a cikin fitsari ko kuma hasarar aƙalla kashi biyar cikin ɗari (5%) na nauyin jikin mace kafin ta samu ciki.

Alamomin matsanancin laulayi

Alamomin matsanancin laulayi suna faruwa ne a cikin wata uku na farko da samun ciki, wasu mata sukan wuce haka. Mace na fama da matsanancin laulayi idan tana ɗauke da ciki kuma tana fama da wasu daga cikin waɗannan alamomin:
  1. Yawan tashin zuciya (Nausea)
  2. Yawan amai - Vomitting (aƙalla sau uku ko fiye a cikin kwana ɗaya)
  3. Ganin juwa (Dizziness)
  4. Yawan kasala (Fatigue)
  5. Rashin ƙarfin jiki (Body weakness)
  6. Yawan tara yawu a baki (a turanci ana kiransa da ptyalism ko kuma sialorrhea gravidarum a likitance)
  7. Rashin bacci isasshe (Insomnia)
  8. Shiga yanayin ɓacin rai da ƙunci ba gaira ba dalili (Anxiety and depression)
  9. Rashin jin ɗanɗanon abinci (Dysgeusia)
  10. Rashin son ƙamshin abubuwa (Hyperolfaction)


Wace mace ce zata iya samun matsanancin laulayi?

Halin haɗari (risk factor) shine wani abu da ke ƙara yawan damar mutum ta kamuwa da cuta ko yanayin rashin lafiya.  Ko da mutum yanada halin haɗarin wata cuta ba ya nuna cewa dole ne sai mutum ya kamu da cutar ko rashin lafiyar.

 A cikin yanayin matsanancin laulayi, waɗannan mata su keda halin haɗarin kamuwa da wannan matsalar, ma'ana sunfi kowa damar kamuwa da matsanancin laulayi:
  1. Mace mai ɗauke da cikin ta na farko
  2. Mace mai ciki da ƙananan shekaru
  3. Mace mai ƙiba (taiɓa)
  4. Mace mai ɗauke da cikin tagwaye
  5. Mace wadda mahaifiyarta ko cikin zuriyarsu wata ta samu matsanancin laulayi
  6. Wadda ta taɓa samun matsalar matsanancin laulayi a baya.
  7. Mace mai yawan chin abinci
  8. Mace mai ɗauke da cutar GTD (gestational trophoblastic disease).

Yadda ake gane mai matsalar matsanancin laulayi a asibiti

Ma'aikacin kiwon lafiya zai yiwa mai ɗauke da ciki tambayoyi game da alamun matsanancin laulayi, haka kuma zai ɗauki cikakken tarihin yadda rashin lafiyar ya fara sannan kuma yayi gwajin jiki. Zai duba ɗaukacin lafiyar jikinta a kan gadon asibiti tare da duba na musamman game da yanayin ruwan jikinta (hydration status).  Bugu da ƙari, mai ba da kiwon lafiya na iya yin odar wasu gwaje-gwajen lab don taimakawa wajen ƙara tabbatarwa da kuma gane zurfin illar da cutar tayi wa marar lafiya. 
Gwaje-gwajen sun haɗa da
  1. Urinalysis
  2. EuCr
  3. Obstetrics scan
  4. Thyroid function tests
  5. Liver function tests
  6. Da dai sauransu.

Yadda ake maganin matsanancin laulayi

Da farko dai za'a wayar ma marar lafiya kai game da yanayin da take ciki, haka kuma za'a bata shawarwari akan abubuwan da ke tayar mata da wannan matsalar da kuma irin kalar abincin da ya kamata taci.

Yana da kyau a duba idan har mace tazo da matsanancin ƙarancin ruwan jiki sakamakon yawan amai da take yi, toh dole ne a kwantar da ita a asibiti a sa mata ruwan jijiya domin maye gurbin ruwan da ta rasa.

A lura cewa mace mai ciki, mutum ce ta musamman. Saboda haka ba kowane magani ake bata ba saboda gujewa matsala gareta da kuma abinda ke cikinta. Magani ɗaya da FDA ta yarda ayi amfani dashi wajen magance tashin zuciya da amai a lokacin juna biyu shi ne Doxylamine/Pyridoxine. FDA (Food and drug administration) wata babbar ƙungiya ce mai tantance ingancin magani da abinci a Amurka.
Sauran magungunan da za'a iya amfani da su ba tare da wata matsala ba, sun haɗa da:
  1. Promethazine
  2. Pyridoxine
  3. Ginger
  4. Prochloperazine
  5. Chlorpromazine
  6. Metoclopramide
  7. Meclizine
  8. Diphenhydramine
  9. Ondansetron
  10. Methylprednisolone

Yadda mai ciki zata kare kanta daga matsanancin laulayi

Kodayake ba a san wasu takamaiman hanyoyin da za a iya hana matsanancin laulayi gaba ɗaya ba, duk da haka matakan da ke biyowa a ƙasa na iya taimakawa wajen kiyaye laulayi daga zama mai tsanani.
  1. Chin abinci kaɗan amma akai-akai
  2.  Jira har sai tashin zuciya ya kwanta kafin sha ko chin wani abu.
  3.  Yawan shan ginger
  4. Abinci mai gina jiki

Illolin da matsanancin laulayi kan iya kawo wa

  1. Ƙarancin ruwan jiki (Dehydration)
  2. Rashin daidaituwar sinadaran jiki (electrolyte imbalance)
  3. Ƙarancin jini (Anaemia)
  4. Ciwon yunwa (Malnutrition)
  5. Ciwon ƙoda (Kidney failure)
  6. Haifuwar ƙaramin jariri (Low birth weight)
  7. Ɓarin ciki (Miscarriage)

Kammalawa

A ƙarshe zamu iya cewa laulayi wani yanayin rashin lafiya ne dake haifar da tashin zuciya da amai wanda ke damuwar mafi yawancin mata masu juna biyu. Duk da haka matsanancin laulayi bai cika faruwa ba, sai ga wasu mata ƙalilan masu halin haɗarin wannan rashin lafiyar. Hakazalika munga hanyoyin da magungunan da ake amfani dasu wajen magance laulayi da kuma matsanancin laulayi.

Idan kuna da tambaya sai kuyi a cikin akwatin sharhi dake ƙasa, Insha Allah zamu karba ba tare da jinkiri ba. Haka kuma zaku iya shiga group dinmu na WhatsApp domin kasancewa damu damu a koda yaushe da kuma samun ingantattun bayanan mu a cikin sauki. Ku danna wannan domin shiga: Lafiyata Group 3. 
Print this post

Post a Comment

0 Comments