Yadda ake Magance Ciwon Ciki: Jagora Mai Zurfi don Kula da Lafiyar Ciki

Gabatarwa

Ciwon ciki (abdominal pain) na nufin kowanne irin jin zafi ko rashin jin daÉ—i a yankin da ke tsakanin Æ™irji da Æ™ugu. Wannan ciwo na iya kasancewa mai sauÆ™i ko kuma mai tsanani, kuma yana iya É—aukar lokaci kaÉ—an ko tsawon kwanaki. A fannin kiwon lafiya, ciwon ciki yana daga cikin manyan dalilan da ke sa mutane zuwa asibiti akai-akai. 

A cikin wannan rubutun, za mu yi zurfin nazari kan me ke kawo ciwon ciki, alamomin ciwon ciki, yadda ake magance ciwon ciki, da kuma hanyoyin kariya daga ciwon ciki. Idan kana neman bayanai kan ciwon hanji, ciwon mara, ko ciwon ciki na mata, toh wannan rubutun zai taimaka maka sosai wajen yi maka jagora.

Maganin ciwon ciki

A matsayin sa na abu mai muhimmanci, ciwon ciki ba abu ne na wasa ba, domin yana iya nuna wata babbar cuta kamar acute appendicitis ko gallstones. A cewar masana lafiya, fiye da miliyan 10 na mutane a Amurka suna fuskantar ciwon ciki a kowace shekara, kuma ciwon ciki na iya shafar yara, manya, da tsofaffi.

Idan ka kasance kana fama da ciwon ciki na yau da kullum ko kuma mai tsanani, kar ka yi wasa ka tuntuɓi likita don gano abun da ke damun ka da a cikin lokaci. A ƙasa, za mu yi bayani dalla-dallah kan waɗannan batutuwa don ku samu ilimi mai zurfi kan lafiyar cikin ku.

Meke Kawo Ciwon Ciki

Sanadi ko abubuwan da ke kawo ciwon ciki na iya zama da yawa sosai, kowane irin ciwon ciki yana dogara ne da sanadin ciwon a wurin ciwo, irin ciwo, da kuma lokacin da ciwon yake faruwa. A ƙasa, za mu rarraba sanadin ciwon ciki bisa ga nau'insa.

Sanadin Ciwon Ciki na Yau da Kullum

Akasarin lokuta, ciwon ciki na faruwa saboda abubuwan da ba su da tsanani sosai. Misali:

1. Ciwon hanji na yau da kullum: Kamar rashin narkewar abinci (indigestion), iska (gas), maÆ™arÆ™ashiya (constipation), ko gudawa (diarrhea). WaÉ—annan na iya faruwa bayan cin abinci mai mai ko abinci mai yaji.

2. Cututtukan abinci: Kamar cin abinci da ya lalace (food poisoning) ko cin wani abinci wanda cikin ka vai yarda dashi ba, kamar lactose intolerance.

3. Ciwon ciki na mata: Kamar ciwon mara a lokacin jinin haila (menstrual cramps), ko ciwon ovulation, wanda ke faruwa tare da sauran alamomin ovulation a lokacin da mace ke sake kwai.

Waɗannan sanadin ciwon ciki na yau da kullum ba sa buƙatar magani mai tsanani, kuma suna iya wucewa da kansu bayan 'yan kwanaki ko da ba'a yi wani magani ba.

Sanadin Ciwon Ciki Masu Tsanani

A wasu lokuta, ciwon ciki na iya zama alamar babbar cuta da ke buƙatar magani nan take. Misali:

Appendicitis: Ciwon ciki mai tsanani a gefen dama na ƙasa, wanda ke faruwa saboda toshewar appendix. Idan ba a yi magani ba, yana iya fashewa da haifar yaɗuwa kwayoyin cuta a cikin yadin peritoneum.

Gallstones ko cholecystitis: Ciwon ciki a gefen dama na sama, wanda ke faruwa saboda toshewar gallbladder. Wannan na iya haifar da jaundice (É—orawar fata da idanu).

Kidney stones: Ciwon ciki mai tsanani da ke motsawa zuwa baya ko makwancinsa, saboda samun dutse ko tsakuwa a koda.

Pancreatitis: Ciwon ciki a tsakiyar ciki ko gefen hagu na sama, wanda ke faruwa saboda kumburin pancreas.

Cututtukan hanji masu tsanani: Kamar Crohn's disease, ulcerative colitis, ko diverticulitis, waÉ—anda ke haifar da ciwon ciki na dogon lokaci.

Cututtukan mata: Kamar ectopic pregnancy (samun ciki a bayan mahaifa) ko tsiro a cikin kwan haihuwa na mata watau, ovarian cysts, waÉ—anda ke haifar da ciwon ciki mai tsanani a mata.

Sanadin Ciwon Ciki, Dake La'akari Da Wurin Ciwo 

Don saukin gano abun da ya kawowa mutum ciwon ciki, masana lafiya suna rarraba sanadin ciwon ciki bisa ga wurin da ciwon yake:

Ciwon saman ciki a gefen dama: Yawanci daga hanta (hepatitis), gallbladder (gallstones), ko kodar gefen dama.

Ciwon saman ciki a gefen hagu: Yawanci yana samo asali ne daga tumbi (gastritis, ulcer), pancreas (pancreatitis), ko spleen.

Ciwon ƙasan ciki a gefen dama: Ciwon Appendix (Appendicitis) ko ciwon ovarian cyst ga mata kawai (banda maza) ko cututtukan hanji.

Ciwon ƙasan ciki a gefen hagu: Diverticulitis ko ciwon ovarian cyst ga mata.

Ciwon ciki na tsakiya: Yawanci daga hanji ko mara, kk farkon ciwon Appendix. Idan ka san wurin ciwon ciki, zai taimaka wa likita don ganowa da sauri.

Alamomin Ciwon Ciki

Alamomin ciwon ciki na iya bambanta, amma yawanci suna haÉ—uwa da abubuwan kamar:

Iri na ciwon ciki: Mai sauki mara suka (dull), mai tsananin suka (sharp), mai takura (crampy), ko mai murÉ—awa (colicky), ko mai zafi (burning).

Lokaci: Yana iya faruwa bayan cin abinci, lokacin haila, ko ba tare da wani ƙayyadadden lokaci ba.

A yara, ciwon ciki na iya haɗuwa da ciwon kai ko rashin jin daɗi gaba ɗaya. A mata masu juna biyu, ciwon ciki na iya zama alamar ectopic pregnancy ko preeclampsia, wanda ke buƙatar magani nan take.

Lokacin da ya Kamata Ka Nemi Likita idan Kana Fama da Ciwon Ciki 

Ba duk ciwon ciki ba ne ke buƙatar neman likita, amma idan ka lura da alamomi kamar haka, ka nemi likita nan take:

  • Ciwon ciki mai tsanani da ba za ka iya motsawa ba.
  • Amai mai tsanani ko gudawa da ke ci gaba fiye da kwanaki 2.
  • Jini a amai, bayan gida, ko fitsari.
  • Zazzabi mai tsanani ko É—orawar idanu ko fata.
  • Kumburin ciki.
  • Rashin iya cin abinci ko shan ruwa, wanda ke haifar da rashin ruwa a jiki.
  • Ciwon ciki bayan rauni ko bayan tiyata.
  • A mata masu juna biyu, duk wani ciwon ciki mai tsanani yana buÆ™atar dubawa don kauce wa haÉ—ari. 
  • A tsofaffi, ciwon ciki na iya nuna ciwon zuciya ko kansa, don haka kar ka yi jinkiri.

Yadda Ake Gano Me Ke Kawo Ciwon Ciki

Ganowar ciwon ciki na farawa da tarihi na lafiya da duban jiki. Likita zai yi tambayoyi kan:

  • Wurin ciwo, irinsa, da lokacinsa.
  • Alamomin da ciwon ciki ke iya zuwa dasu kamar amai ko gudawa.
  • Tarihi na cututtuka ko magunguna.
  • Sannan, za a iya yin wasu gwaje-gwaje kamar:
  • - Gwajin jini da fitsari don gano cututtuka.
  • - Duban ciki da ultrasound ko CT scan don ganin abubuwan ciki.
  • - Endoscopy ko colonoscopy don duban hanji.
  • - X-ray don ganin toshewa ko tsakuwa.

WaÉ—annan gwaje-gwaje suna taimakawa wajen gano sanadin ciwon ciki da sauri, don haka za a iya fara magani nan take.

Yadda ake Magance Ciwon Ciki

Magance ciwon ciki yana dogara da abin da ya kawo wannan ciwon ciki, watau sanadinsa. A ƙasa, za mu yi bayani kan magunguna na gida da na likita.

Magunguna na Gida don Ciwon Ciki

Idan ciwon ciki ba shi da tsanani, ka yi amfani da waÉ—annan hanyoyi:

Bawa hanji hutu: Ka daina cin abinci na dan lokaci, ko ka ci abinci mai sauki kamar burodi ko ayaba.

Shan ruwa da yawa: Don kauce wa rashin ruwan jiki, yana da kyau kasha ruwa ko ruwan rayuwa, har dai idan ciwon ciki ya haÉ—u da zawo ko amai.

Amfani da zafi: Ka saka kwalbar ruwan zafi a wurin ciwo don rage ciwo, kamar mata masu amfani da hot water bottle a lokacin jinin haila.

Magunguna na gargajiya: Kamar shan ginger don rage rashin narkewar abinci a ciki, peppermint don kwantar da hanji, ko licorice don rage iska da kumburin ciki.

Kar ka yi amfani da magungunan rage ciwo kamar aspirin ba tare da shawarar likita ba, domin suna iya kara tsananta maka ciwon ciki.

Magungunan Ciwon Ciki na Asibiti 

Idan sanadin ciwon ciki wata cuta ce mai tsanani ana amfani da wadannan hanyoyin domin maganin ciwon ciki a asibiti:

Magunguna: Kamar antibiotics don maganin ciwon ciki wanda kwayoyin cutar bakteriya sukw kawowa, antacids don ciwon ciki wanda na ulcer, ko pain relievers da likita ya rubuta.

Tiyata: Don abubuwan kamar ciwon ciki na Appendix (appendicitis), ko dutse a cikin gall bladder (gallstones), ko toshewar hanji.

Magani na dogon lokaci: Don cututtuka kamar IBS ko Crohn's disease, wanda ke buƙatar magunguna na musamman da canjin abinci.

A mafi yawan lokuta 80% na ciwon ciki ana iya magancewa da magunguna na gida, amma idan ba ka samu sauki ba, ka nemi likita.

Yadda ake Samun Kariya daga Ciwon Ciki

Don kauce wa ciwon ciki, yi amfani da waÉ—annan shawarwari:

Cin abinci mai lafiya: Ci abinci mai yawan fiber kamar 'ya'yan itace da kayan lambu, ka rage abinci mai mai da yaji.

Motsa jiki na yau da kullum: Yi tafiya bayan cin abinci don taimakawa abinci narkewa a ciki.

Rage damuwa: Yi abubuwan kwantar da hankali kamar wasannin nishadi.

Rage shan abubuwa masu É—auke da caffeine da barasa: WaÉ—annan na iya haifar da ciwon ciki sosai.

Ka yi gwaje-gwaje na yau da kullum: Don gano cututtuka da wuri yana da kyau kaje asibiti ana gwada ka akai-akai, musamman idan kana da tarihi na cututtukan ciki.

Ka sha ruwa da yawa: Aƙalla kofin gilashi 8 a rana don kauce wa maƙarƙashiya (constipation).

Ta hanyar bin waÉ—annan, za ka iya rage yawan ciwon ciki da kuma inganta lafiyar ciki gaba É—aya.

Kammalawa

Ciwon ciki ciwo ne na yau da kullum, amma yana iya zama alamar babbar matsala. Ta hanyar sanin sanadin ciwon ciki, alamomin ciwon ciki, da magance ciwon ciki, za ka iya kare lafiyarka daga samun babbar matsala. Idan ka lura da alamomi masu tsanani, ka nemi likita nan take don kauce wa haÉ—ari. 

Rubutu Masu Alaka 



No comments: