Ciwon Mara na Sha'awa – Sanin Abin da Ke Haddasa Shi da Hanyoyin Magancewa

Akwai lokuta da mata ko maza ke fama da ciwon mara yayin ko bayan sha'awa, ko kuma a lokacin jima’i. Wannan nau’in ciwo ana yawan danganta shi da ciwon mara na sha’awa. Ko da yake wasu na iya É—aukar hakan a matsayin al’ada, yana da matuÆ™ar muhimmanci a fahimci musabbabin ciwon mara, irin ciwon da ake nufi, da hanyoyin magance shi yadda ya dace.

Wannan rubutu zai bayyana ainihin ciwon mara da ke da nasaba da sha’awa, da yadda zai shafi lafiyar ma'aurata, musamman mata. Za mu tattauna abubuwan da ke haifar da ciwon, alamu, da kuma hanyoyin maganin sa, domin ku iya kula da lafiyar ku yadda ya kamata.

GargaÉ—i: Wannan rubutu anyi shi ne kawai saboda ilmantar wa da kuma inganta kyakkyawar zamantakewa da mu'amala tsakanin ma'aurata, duk wanda yayi ma rubutun wata mummunar fahimta, ko ya bashi wata mummunar ma'ana ko yayi amfani dashi ta hanyar da bata dace ba, toh ya ha'inci marubucin.


Ciwon mara na sha'awa


Me ake nufi da Ciwon Mara na Sha’awa?

Ciwon mara na sha’awa ciwo ne da ke tasowa a Æ™asan ciki (mara), wanda ke faruwa yayin da mutum ke jin sha’awa, a lokacin jima’i, ko bayan jima’i. Yana iya kasancewa mai rauni ko mai tsanani. Sau da yawa ya fi shafar mata fiye da maza.

Abubuwan da ke Haddasa Ciwon Mara na Sha’awa

1. Ciwon Mahaifa (Endometriosis)

Wannan cuta na faruwa ne idan tantanin halittun bangon mahaifa na ciki suna fitowa daga inda ya dace. Yana haifar da zafi yayin ko bayan saduwa.

2. Cutar Sanyin Mara (PID - Pelvic Inflammatory Disease)

Wannan ciwo na faruwa ne idan akwai kamuwa da cuta a cikin mahaifa ko bututun haihuwa, wannan ma yana kawo zafi yayin sha’awa da yayin jima'i.

3. Raunin Farji (Vaginal Tear ko Dryness):

Rashin isasshen danshi a farji yana iya haifar da  rauni ko Æ™aiÆ™ayi da ciwon mara.

4. Kurjin Ovaries (Ovarian Cyst):

Idan akwai Æ™urji a cikin ovaries na mace, zai iya haifar da zafi a mara yayi ko bayan sha’awa.

5. Saduwa da Karfi 

Lokacin da aka yi amfani da matsanancin Æ™arfi ko rashin kwanciyar hankali yayin jima’i.

6. Damuwa ko Tsoro (Psychological Factors):

Lokacin da mace ke cikin damuwa ko rashin nutsuwa, yana iya haifar da tsantsar ciwo a mara.

Alamomin da ke Tafe da Ciwon Mara na Sha’awa

  • Ciwon mara mai tsanani a lokacin jima’i
  • Jin zafi ko Æ™aiÆ™ayi a farji
  • Fitar ruwa mai wari ko launin baÆ™i daga farji
  • Jin nauyi a Æ™asan ciki
  • Fitar jini bayan jima’i
  • Jin kasala ko gajiya a jiki
  • Ciwon mara yayin da duk sha'awa ta motsa 

Yadda Ake Magance Ciwon Mara na Sha’awa

1. Ziyarci Likita

Abu na farko shi ne a ga likitan mata ko urologist, musamman idan ciwon yana maimaituwa lokaci zuwa lokaci.

2. Gwaje-gwaje

Likita zai iya bada shawarar a yi ultrasound, scan ko gwajin fitsari domin gano musabbabin ciwon.

3. Magunguna

Idan cutar infection ce (kamar PID), antibiotics za su taimaka. Idan endometriosis ce, ana bada magunguna rage radadi ko ayi tiyata.

4. Lubricants (Man-shafawa)

Idan ciwon yana da alaÆ™a da bushewar farji, amfani da man shafawa mai ruwa zai taimaka wajen sauÆ™aÆ™e jima’i.

5. Sauya salon Jima’i

Sauya salo da É—aukar lokaci a wajen wasannin tsokano sha'awa (foreplay) yana taimakawa rage ciwo yayin jima'i.

6. Kawar da Damuwa

Yana da kyau neman shawarwarin likita ko kwararren lafiyar kwakwalwa idan damuwa ko tsoro ke haddasa ciwon.

Yadda Za Ki Kare Kanki daga Ciwon Mara na Sha’awa

  • Kula da tsaftar gabobin jiki musamman bayan saduwa
  • Kada a yi jima’i da karfi ko cikin rashin natsuwa
  • Kula da lafiyar mahaifa ta hanyar zuwa duba lafiya lokaci-lokaci
  • Gujewa amfani da kayan da ke busar da farji
  • Shan ruwa sosai da cin abinci mai kyau
  • Ka guji canza abokan jima’i domin kare kai daga cututtukan jima’i kamar su PID.

Kammalawa

Ciwon mara na sha’awa ba abu bane da ya kamata a kyale ba. Yana iya zama alamar matsala mai tsanani da ke buÆ™atar kulawar likita. Idan kina fama da wannan matsala, to kada ki ji kunya ko tsoro wajen nema taimakon likita. Yin hakan zai taimaka wajen kare lafiyar mahaifa da jin daÉ—in jima’i a cikin aure.


Rubutu Masu AlaÆ™a 

1. Jin Zafi Yayin Saduwa: Abubuwan da Ke Kawowa da Kuma Yadda Ake Maganin sa

2. Yadda ake maganin ciwon mara ga budurwa a lokacin jinin al'ada 

3. Alamomin sanyin mara da yadda ake maganin sanyin mara na mata(PID)

4. Yadda ake maganin infections (Vaginal infections)

5. Sanyin Mata: Illolin cututtuka masu yaduwa ta hanyar saduwa (STIs)