Ba ko yaushe canjawar kalar fitsari yake zama sakamakon wata matsala ba, haka kuma, a wasu lokuta yakan iya zama alamar wasu cututtuka. A cikin wannan rubutu zamu fayyace zare da abawa akan canjawar kalar fitsari wanda yake sakamakon wasu cutuka da kuma canjawar kalar fitsari wanda ba matsala ba.
Akwai mahimman dalilai da idan aka haɗu da ɗaya daga cikin su launin fitsari zai iya canjawa daga kalar sa da kuma yanayin yadda za'a ji shi a hanci wato yanayin ƙanshi ko warin sa, warin sa. Daga cikin abubuwan dake canja kalar fitsari waɗanda ba matsala ba akwai;
- 1- Shan wasu magunguna
- 2- Canjin yanayi
- 3- Rashin shan ruwa
- 4- Amfani da wasu kayan abinci.
Manyan cututtuka ko matsalolin da ke haifar da canjawar launin fitsari su kuma sun haÉ—a da:
- 1- Matsalolin ciwon ƙoda
- 2- Matsalolin ciwon magudanan fitsari
- 3- Matsalar ciwon sugar
- 4- Matsalar ciwon hanta
- 5- Cutar zazzaɓin cizon sauron na maleriya
- 6. Cutar sikila
- 7. Ƙarancin ruwan jiki
Abubuwan Da Ke Canja Launin Fitsari
Fitsari na sai naga ya koma kalar ruwan ƙwai ko kuma kalar ja, toh, me hakan ke nufi? Daga cikin dalilai waɗanda ke haifar da canjawar kalar fitsari sun hada:-
1. Amfani Da Wasu Magunguna
Anfani da wasu magunguna kamar magungunan zazzaɓin cizon sauro na maleriya dangin ACT su na canja kalar fitsari zuwa kalar yellow, kamar yadda ita kanta cutar maleriya ta kan iya canja launin fitsari zuwa yellow ko kalar ja. Kaɗan daga cikin wasu magunguna da ke iya canja launin fitsari zuwa wata kala sun haɗa da:
- 1- Rifampicin
- 2- Jawaron
- 3- Artemether/Lumenfantrin
- 4- Mist Potcit
- 5- Isoniazid
- 6- Ethambutol
- 7- Pyrazinamide
- 8- Vitamin B. Complex
- 9- Folic acid
- 10- Fesolate
- 11- Blood Tonic
- 12- Becombiom
- 13- Iron Dextrose
- 14- Diclofenac
- 15- Piroxicam
- 16- Aldomet
A lokacin da wani ko wata ke amfani da ɗaya daga cikin waɗannan magungunan ko wani magani wanda ya ƙunshi ɗaya daga cikin waɗannan magunguna da muka ambata a sama kan iya samun canjin launin fitsarin sa zuwa wata kala ta daban. Dan haka ba lallai wannan ya zama matsala ba, daga an daina shan maganin launin fitsarin zai iya dawowa daidai.
2. Rashin Shan Ruwa
Rashin shan wadataccen ruwa, idan ba'a samun damar shan ruwa kan lokaci na daga cikin dalilan da kan iya canja launin fitsari zuwa kalar ɗorawa ko kuma launin ja. Haka kuma idan mutum ya samu matsalar ƙarancin ruwan jiki wanda kan iya biyo bayan amai da gudawa, ko ciwon atini, shi ma yakan sanya fitsari yin duhu ya zama kamar kalar ɗorawa.
3. Yanayin Zafi
Zama ko rayuwa cikin zafi, canjin yanayi na zafi, iska da bazara yana sa fitsari ya rika canja kala yayi duhu sosai, haka kuma yawan fitsari yakan ragu.
4. Cututtuka
Canjawar launin fitsari zuwa kalar jaa ko ɗorawa kaɗan ne daga cikin alamomin wasu cutuka kama daga cutar zazzaɓin cizon sauro na malaria, matsalolin ƙoda, hanta da dai sauran su. Haka zalika cutar magudanan fitsari da kuma cutar sanyin mara suna iya canja launin fitsarin mutum zuwa fari, ko fitsari mai hazo-hazo ko kuma fitsari mai kama da madara.
Bugu da ƙari, hauhawar wasu sinadarai ko chemicals a cikin jini waɗanda ake iya samu a fitsari, kamar hauhawan sinadarin haemoglobin wanda cutar sikila ke kawo wa saboda fashewar jajayen halittun jini, da kuma hauhawar sinadarin myoglobin saboda fashewar tantanin halittun tsokoki, duk suna maida fitsari kalar jaa ko deep yellow.
Fitsari kan zo da kala daban daban wanda kowane nada abin da yake nufi. Ba lallai canjawar fitsari musamman yellow ya zama alama ta wata matsala ba.
Maganin Canjawar Kalar Fitsari
Babbar mafita shi ne yawaita shan ruwa dayawa, shan ruwa na baiwa ƙoda damar magance matsalar basai ansha magani ba. Idan kuwa cututtuka ne suka kawo rikiɗewar fitsari zuwa wani kala, kamar ciwon ƙoda, ciwon hanta, cutar sikila ko cututtukan magudanan fitsari, toh dole ne sai an magance waɗannan cutuka. Haka kuma, rikiɗewar da shan wani magani ya kawo, daga an daina shan maganin cikin 'yan kwanaki fitsarin zai koma normal.
0 Comments