Maleriya cuta ce mai hatsari da ke kashe a ƙalla mutum 600,000 duk shekara a faɗin duniya. Fiye da mutum 9 cikin 10 da cutar maleriya ke kashewa suna zaune ne a Afirka, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya.
An saki dubban saurayen da aka sauya wa ƙwayoyin halitta a ƙasar Djibouti da manufar daƙile yaɗuwar saurayen da ke yaɗa cutar maleriya.
Saurayen da ake amfani da su wajen daƙile yaɗuwar cutar Maleriya, sauraye ne na Anopheles maza da ba su cizo, waɗanda kamfanin Birtaniya Oxitec ya ƙirƙira kuma suna ɗauke da wata ƙwayar halitta ne da ke kashe matan sauraye masu cizo tun kafin su balaga.
Da ma dai sauraye mata ne kawai ke cizo kuma suke yaɗa cutar maleriya da sauran cutuka. Sauraye mata suna cizo ne a ƙoƙarin su na tsotsan jini domin ƙyanƙyashe ƙwayayen su idan sun tashi hayayyafa.
Sakin irin wadannan sauraye a ƙasar Djibouti da akayi a ranar Alhamis da ta gabata shi ne karo na farko da aka saki saurayen a yankin Afirka ta Gabas kuma karo na biyu a faɗin nahiyar Afirka baki ɗaya.
An yi amfani da irin wannan fasahar cikin nasara a Cayman Islands, Brazil, da da Panama, da Indiya, a cewar hukumar kare yaɗuwar cutuka ta Amurka, American Centre for Disease Control and Prevention (CDC).
An saki irin wadannan saurayen da aka sauyawa ƙwayoyin halitta fiye da biliyan ɗaya a yankin Ambouli da ke birnin Djibouti ranar Alhamis 23 ga watan Mayu na 2024.
Wannan aikin gwaji ne tsakanin Oxitec Ltd, da gwamnatin Djibuti, da kuma ƙungiyar Association Mutualis.
"Mun ƙirƙiri saurayen da ba su cizo, ba su yaɗa cuta. Idan muka saki waɗannan sauraye, za su yi mu'amala da matan sauraye masu yaɗa cuta sannan su hallaka su," kamar yadda shugaban Oxitec ya faɗa wa BBC.
Saurayen da aka samar a ɗakunan gwaji na ɗauke da ƙwayar halittar da ke hana jariransu mata girma da zarar sun yi mu'amala tare.
Mazansu ne ke girma amma daga bisani kuma su mutu, a cewar masana kimiyyan da suka yi aikin.
Ba kamar sauraye maza na Anopheles colluzzi da aka saki a Burkina Faso a 2018 ba, saurayen da aka saki a Djibouti a yanzu masu suna stephensi za su iya saka ƙwai.
Tun shekara biyu da suka gabata aka fara gwajin saurayen waɗanda aka fara ganowa a 2012.
A lokacin, ƙasar Djibouti na ƙoƙarin kawo ƙarshen maleriya. Tun daga lokacin kuma zazzaɓin na maleriya ya dinga raguwa sosai a yankin.
Yanzu akwai irin waɗannan sauraye a ƙasashen Afirka 6, ƙasashen su ne - Habasha, Somaliya, Kenya, Sudan Najeriya, Ghana.
Masana sun gano cewa nau'in sauro na stephensi da suka samo asali a nahiyar Asiya, na da wuyar sha'ani. Kazalika ana kiran shi da sauron cikin birni da ya gagari magani. Yakan ciji mutum da rana da kuma dare.
Wani mai bai wa gwamnatin Djibuti shawara, Dr Abdoulilah A. Abdi, ya faɗa wa jaridar Financial Times cewa burin gwamnatin shi ne "daƙile maleriya cikin gaggawa a ƙasar, wanda ciwon ya ƙaru cikin shekara 10 da suka wuce".
"Yanzu kuma muna ganin marasa lafiya kusan a kullum a faɗin Djibuti. Akwai buƙatar ɗaukar ƙarin manyan matakai." Inji Abdi.
An daɗe ana cece-kuce kan halittun da ake sauya wa ƙwayoyin halitta a Afirka. Masu rajin kare muhalli sun yi ta gargaɗin abin da hakan zai iya haifar wa muhalli da kuma samar da abincin yau da kullum.
Amma Mista Frandsen shugaban samar da sauraye na Oxitec ya ce wannan aikin ba shida wata matsala ga muhalli ko lafiyar ɗan'adam da aka taɓa samu cikin shekara 10 - lokacin da kamfanin ya saki biliyoyin sauraye da aka sauya wa ƙwayar halitta.
"Wannan sabon salon zai iya jawo cece-kuce amma kuma shi ne makomarmu," a cewar Dr Abdi.
Idan tsarin ya yi nasara, za a faɗaɗa girman gwajin, inda za a ci gaba da sakin ƙarin sabbin sauraye har zuwa cikin shekara ta gaba a ƙasar Djibouti.
0 Comments