Ad Code

Ticker

6/recent/ticker-posts

Me Yasa Ake Haihuwar Yara Da Nakasa Ko Tawaya? - Congenital Abnormalities

Yaro mai nakasa

Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta ce kimanin jarirai dubu dari biyu da arba'in (240,000) ne ke mutuwa a duniya a cikin kwanaki 28 da haihuwa a kowace shekara saboda an haifo su da tawaya ko nakasa.

Hukumar ta ce naƙasa na haifar da ƙarin mutuwar yara dubu ɗari da saba'in (170 000) tsakanin watanni 1 zuwa shekaru 5 kuma tara daga cikin yara goma da aka haifa tare da tawaya suna cikin ƙasashe masu matsakaicin ƙarfi.

Haihuwar yara da nakasa ko tawaya na nufin a haifi jariri ba tare da ya samu cikkakiyar halitta ba, ya zama wani gaɓar jikin sa bai sami cikakkiyar halitta ba, tawaya za ta iya shafan kowane bangaren jiki, harda ƙwaƙwalwa da hankali har ma da tunani.

Ana haihuwar wasu jarirai da tawaya ko naƙasa bayyane a wane sashen jikinsu kamar hannu ko ƙafa, wasu kuma da tawaya a sassan jikinsu na ciki, kamar a haifi yaro da ƙoda ɗaya ko huduwa a zuciya, ko a haifi yaro ba dubara ta kashi.

Wasu yaran kuma ba su samun tawaya ta bayyane ko a wani sashen jikinsu na ciki, suna samun tawaya ne a ƙwaƙwalwa, a inda zaku ga yaro yaƙi saurin girma ko ya tashi dolo-dolo ba wayo.

Tawaya ko nakasa na iya kasancewa na dogon lokaci, wanda ke yin tasiri sosai ga ɗaiɗaikun mutane da kuma iyalai kamar yadda wasu iyaye ke shaidawa asibiti irin ƙalubalen da suke fuskanta wajen renon yaron da ke da tawaya ko nakasa.

Yayin ganawa da wata mai renon yaron da ke da tawaya, matar ta ce ba ita ta haifi yaron ba, inda ta ce uwar da ta haifi yaron 'Æ´ar wata makwaciyarta ce, kuma uwar ta so zubar da cikin lokacin da ta gano tana da juna biyu.

Matar ta ce uwar ta ɗauki cikin ne ba ta da aure, tsoron iyayenta da gudun maganganun mutanen duniya ne ya sa ta nemi hanyar da za ta zubar da cikin, inda ta sami wata ƙawarta ta ba ta shawarar siyan wasu magungunar zubar da ciki.

"Uwar da kanta ta faɗa min cewa ita da wata ƙawarta suka je suka nemo magungunan zubar da cikin, wanda ta share kwanaki uku tana sha, amma cikin ya ƙi zubewa." Inji matar.

Matar ta ci gaba da cewa "A lokacin da uwar ta ga cikin ya ƙi zubewa kuma kafin iyayenta su gano ta, sai ta sake komawa ta nemi wani magani mai ƙarfi da yafi nafarko, amma duk da hakan, cikin ya ƙi zubewa, daga baya dai iyayen ta su ka gano tana da juna biyu, a lokacin kuma cikin ya riga ya kai mizanin watanni shida (6)."

"Ganin haka ne, iyayen su ka ce toh ta san yadda za ta yi da cikin, kar ta sake ta kawo musu wani É—a a gidan su da bashi da uba, saboda su ma wahala suke sha, basu da kuÉ—i, cin abinci wahala, a yadda take bada labari."

Toh ita kuma matar da me renon ba ta da yara kuma mijinta ya rasu, shine kawai ta ce idan uwar ta haihu, za ta karɓi jaririn ta rene shi.

Matar ta ce "ko da uwar ta haifo yaron, gaba ɗaya sai a hankali, hannun sa a lanƙwashe, ƙafafun sa a lanƙwashe, bakin sa a karkace, a haka ta ce ta karbi jaririn."

"Uwar na haifar yaron suka bar garin, suka koma asalin garinsu da ke Kaduna, yau shekara 5 kenan, ita ke renon yaron."

Matar ta ce a lokacin da aka haifi yaron, ta kai shi asibiti domin ta gano ko za a iya masa magani, amma ta ce a nan ne likitan ya tambaye ta ko ita ta haifi yaron, sai ta ba shi labarin yadda abun ya faru, shine likitan ya ce mata yaron ya fito a haka ne ta sanadiyyar magungunan da mahaifiyar shi ta sha domin zubar da cikin.

Wadanne Abubuwa Ke Haddasa Tawaya Ko Naƙasa a Jarirai

Abubuwan da ke kawo tawaya a jarirai sun kasu kashi-kashi.

1. Akwai abun da ya shafi ƙwayoyin halitta wanda ake gadon su kamar tubalin halitta, wato gene kenan da chromosomes waɗanda ke iya sa cututtuka daban-daban da ake haihuwar jarirai da su kamar irin su 'Down syndrome'.

2. Ana kuma iya samun tawaya saboda muhalli kamar irin wuraren da ke da sinadarai masu gurɓata muhalli kuma mace mai juna biyu tana zama a irin wuraren.

3. Sai kuma idan ya kasance mahaifiyar jaririn tana da matsalar ƙarancin sinadarai masu inganci na abinci kafin ta sami juna biyu ko kuma farkon juna biyun har zuwa kusan mako takwas, wannan yana iya haddasa haihuwar jariri da tawaya. Misali, ƙarancin sinadarin abinci na folic acid yana sa a haifi yarp da wata tawaya a bayan sa.

Haihuwar yara masu tawaya

4. Da kuma idan mahaifiya ta kasance tana amfani da magunguna masu ƙarfi na sha ko na shafawa, na asibiti ko na gargajiya, musamman a lokacin da cikin yake karami, waɗannan magungunan suna iya zama sun shafi jariri.

5. Da kuma idan mahaifiya tayi wasu cututtuka a lokacin da cikin ya ke É—anye, kamin yakai makonni goma sha biyu, kamar irin cutar rubella, shi ma wannan yana iya sa jaririnta ya samu tawaya.

6. Haka kuma mata masu shaye-shaye, musamman masu shan barasa, suna haihuwar yara masu tawaya, idan sun cigaba da shan barasa a lokacin da suke da cikin.

7. Yunkurin zubar da ciki bayan an same shi, hakan ma yakan ma yakan sa yaro ya fito da nakasa ko wata tawaya a jikinsa.

8. Idan ya kasance mahaifiya ta tsufa kuma ta sami juna biyu, shi ma yana É—aya daga cikin abubuwan da ke kawo hatsarin haifar jariri da tawaya, amma kuma wannan ba ya faruwa sosai.

Wadanne Ire-iren Tawaya Ko Naƙasa Jarirai Kan Iya Samu?

Tawaya ko naƙasa na iya shafar kusan kowanne ɓangare na jikin jariri.

Ana iya haifar jariri da ƙaton kai ko da ɗan ƙaramin kai, ko kuma a haife shi da matsala a idanun sa ko a sami matsala da ta shafi hanci ko kuma ya zama dasashin sa ya ɓarke. Wannan tawayar na iya shafar laɓɓa ma, ana iya samun su ma leɓɓa sun ɓarke, ana kuma iya samun ɗan gajeran wuya ko mai faɗi."

Ana kuma iya samun tawaya ta shafi zuciya, kuma tawaya na iya sa a haifi yaro da hanji a waje, ko hanji a mirÉ—e, ko kuma a samu matsalar da ta shafi laka wato abin da ake kira da 'spina bifida'.

Haihuwar jariri da hanji waje

Haka kuma ana iya haifar jariri da matsala a hannu ko ƙafa su zamo 'yan gajeru ko kuma a lanƙwashe, ko ya rasa hannun ko ƙafa ma baki daya.

Ana iya samun a gaban jaririn a same shi da matsala, kamar kaga an haifi jariri mata-maza ko kuma matsala ta wajen dubara, wanda zai iya shafar hankalin mutum da yanayin yadda yake abubuwa idan yana girma.

Magungunan zubar da ciki na yin tasiri wajen haifar jariri da tawaya ko naƙasa.

Ana iya gane jariri na É—auke da tawaya tun a ciki?

Idan aka je awo, ana iya gane cewar jaririn da ake ɗauke da shi yana da naƙasa, wannan shi ya sa musamman ake yin wani hoto na jariri domin a gane ko shin jaririn lafiyayye ne ko yana da wata matsala kafin a haife shi. Ana yin wannan hoton ne a lokacin da cikin ya kai wata biyar (5).

Ga waÉ—anda ba su zuwa asibiti awo, gaskiya zai yi wahala a gane cewar jaririn su na da nakasa saboda dai ba hoto aka yi ba ballantana a ga jaririn kuma a gane cewa yana da tawaya.

Sannan idan ya kasance mahaifiya tana shan sigari ko barasa ko kuma ƙwayoyi da suke sa maye, duka suna iya sa ta haifi jariri da tawaya ko nakasa.

Hanyoyin Kariya Daga Haihuwar Jarirai Masu Tawaya

Akwai wasu abubuwa da idan aka guje su, za a samu saukin hatsarin haihuwar yaro mai tawaya. Abubuwan kuwa su ne kamar haka:

  1. Mace mai juna biyu ta guji shan taba da giya da kuma shaye-shayen ƙwayoyin da ke sa maye.
  2. Mace ta kasance kafin lokacin da za ta sami juna biyu, tana cin abinci mai sinadarai na gina jiki musamman sinadarin folic acid. An so mace ta dinga shan maganin folic acid daga zarar ta ƙudurta niyyar haihuwa.
  3. Idan mace na da ciwon sukari, ya kasance an É—auki mataki yadda za a shawo kan cutar kafin ta samu juna biyu.
  4. Idan mace na da juna biyu, ya kamata a duba sauran cutuka kamar su cutar 'rubella' da kuma matakin da ya kamata a bi wajen magance su.
  5. Mace ta guji shan magunguna barkatai musamman idan mace na farkon samun juna biyu ko ana tunanin za ta sami juna biyu da kuma guje wa magungunan zubar da ciki.
  6. Mace ta gujewa shan ruwan da ba shi da inganci da kuma ko wane irin gurɓataccen ruwa.
  7. A dage da zuwa asibiti da wuri domin awo saboda a yi bincike a gane cewar jaririn da aka ɗauka na cikin ƙoshin lafiya. Ana so mace taje ayi hoton duba lafiyar jariri a lokacin da ya kai watanni biyar (5 months), ko kuma makonni ashirin zuwa ashirin da biyu (20-22 weeks).

Print this post

Post a Comment

0 Comments