Amfanin magunguna da alluran riga-kafi ga yara ƙanana

Gabatarwa;

Kuna so ku yi abin da ya fi dacewa ga yaranku? Kun san mahimmancin kayan masarufi, abubuwa masu tsada, da sauran hanyoyin kiyaye yaranku amma ko kun san cewa ɗayan mafi kyawun hanyoyin kare yaranku shine tabbatar da cewa sunyi dukkan allurar rigakafinsu?


 Allurar rigakafi na iya ceton rayuwar yaran ku.

A wannan zamani saboda ci gaban kimiyyar kiwon lafiya, ana samo hanyoyin kare yaranku daga wasu cututtuka fiye da kowane lokaci. An kawar da wasu cututtuka waɗanda a lokacin baya sun yiwa al'umma illah kuma sun kashe dubban yara, wasu cututtuka kuma suna dab da ƙarewa - duk dai saboda amintattun alluran rigakafi.  

Cutar shan innah ta Polio misali ɗaya ce na babban tasirin da alluran rigakafi suka yi a duniya. A can baya, cutar shan inna ta kasance cutar da tafi firgita Amurkawa sama da komi, wadda ke haddasa mace-mace da naƙasa a duk fadin ƙasar, amma a yau, sakamakon allurar rigakafin cutar, an shafe sama da shekaru 20 ba'a samu rahoton cutar shan inna ko daya a Amurka ba.

 Alurar riga kafi yana da aminci da inganci.  

Ana ba da alluran rigakafi ga yara ne kawai bayan dogon nazari da bincike daga masana kimiyya, likitoci, da ƙwararru a fannin kiwon lafiya.  Allurar riga kafi zai iya ƙunsar wasu rashin jin daɗi kuma yana iya haifar da jin ciwo, ja, ko taushi a wurin allurar, amma wannan kadan ne idan aka kwatanta da zafi, rashin jin daɗi, da illolin cututtukan da waɗannan alluran ke hanawa.  

Mummunan illolin da kan biyo bayan allurar rigakafi, kamar rashin lafiyar jiki mai tsanani, ba su da yawa. Amfanin rigakafin cututtuka na samun alluran rigakafi ya fi yawan illar da za a iya samu ga kusan dukkan yara.

Rigakafin yana kare 'yan uwa da abokan arziki.

Yara a Afrika har yanzu suna samun cututtukan da za a iya magance su ta hanyar rigakafi. A haƙiƙa, mun ga sake bullowar cutar kyanda (measles) da tarin fuka (pertussis) a cikin ƴan shekarun da suka gabata, a kwanakin nan ma har da cutar murar mashaƙo (diphtheria). 

Har ma a Amurka ita da muke gani babbar ƙasa, tun daga shekara ta 2010 sai  an sami kamuwa da tari tsakanin mutane 10,000 zuwa 50,000 kowace shekara a ƙasar. Haka kuma, kimanin jarirai 10 zuwa 20, waɗanda da yawa daga cikinsu sun yi kanana ba za a iya yi musu cikakken rigakafin ba, suna mutuwa a kowace shekara. 

Don taimakawa wajen kiyaye yaranmu, kula da lafiyar su da kuma bunƙasa dukkan sha'anin kiwon lafiyar al'umma yana da kyau mu tabbata anyiwa yaranmu alluran riga-kafi kamar yadda dokar riga-kafin ta kasa ta tanada.  Wannan ba kawai yana kare yaran ku ba, har ma yana taimakawa hana yaduwar waɗannan cututtuka ga yan'uwa da abokan arziki.

Yiwa yaranku riga-kafi yana rage muku kashe kudi da barnar lokaci.

Yaron da ya kamu da cutar da za'a iya karewa ta hanyar magunguna da alluran rigakafi za a iya hana shi halartar makarantu ko wuraren kula da yara. Wasu cututtukan da za a iya rigakafinsu na iya haifar da nakasu na tsawon lokaci kuma suna iya janyo asarar kuɗi tare da asarar lokacin aiki, ta hanyar kuɗin da za'a kashe wajen ganin likita ko kula da nakasa na dogon lokaci.  

Sabanin haka, yin allurar rigakafin waɗannan cututtuka shine jari mai kyau kuma yawanci ana yin shi ta hanyar inshora a wasu kasashe, bal toh mu anan Nigeria mafi yawancin duka allurar riga-kafin kyauta ake yi. Shirin Alurar rigakafin yara, shiri ne na tarayya wanda ke ba da alluran rigakafi kyauta ga yara zuwa ga iyalai masu karamin karfi har ma da kowa.

Rigakafin yana kare zuriyarmu masu zuwa.  

Alurar riga kafi suna ragewa kuma suna kawar da wasu cututtuka da yawa waɗanda ke kashe mutane ko nakasassu ƴan lokuta kaɗan da suka wuce.  Misali, rigakafin cutar small pox ya kawar da cutar a duk duniya.  'Ya'yanku ba dole ba ne su sake yin allurar rigakafin ƙwayar cutar saboda cutar ba ta wanzuwa a yanzu. 

Ta hanyar yi wa yara allurar rigakafin cutar rubella, haɗarin da mata masu juna biyu za su iya yaɗawa ɗan tayin da ke cikin su ya ragu sosai, kuma an daina ganin lahanin haihuwa da ke da alaƙa da wannan cutar a Nigeria. 

Idan muka ci gaba da yin alluran rigakafi a yanzu, kuma muna yin alluran duka gaba ɗaya kamar yadda dokar ƙasa ta tanada, toh iyaye a nan gaba za su iya amincewa cewa da kansu wasu cututtuka na yau ba za su sake cutar da 'ya'yansu ko jikokinsu a nan gaba ba. 

Idan kuna da tambaya sai kuyi a cikin akwatin sharhi dake ƙasa, Insha Allah zamu karba ba tare da jinkiri ba. Haka kuma zaku iya shiga group dinmu na WhatsApp domin kasancewa damu damu a koda yaushe da kuma samun ingantattun bayanan mu a cikin sauki. Ku danna wannan domin shiga: Lafiyata Group 3. 

 Nassoshi

Post a Comment

0 Comments