Yara masu tasowa suna da rauni sosai, ba raunin jiki kadai ba har na da raunin garkuwar jiki, hakan ya sanya su akan hatsarin kamuwa da cututtuka da yawa. Wannan shi ne babban dalilin da yake da matuƙar mahimmanci ayiwa jarirai da ƙananan yara allurai da magungunan rigakafi tun lokacin haihuwa. Childhood immunisation shi ne aikin ba wa yara magunguna da alluran rigakafin da zasu taimakawa garkuwar jikinsu wajen yaki da cututtuka masu yaɗuwa.
Irin waɗannan cututtuka na iya kawo cikas ga girman yaro, wasu kuma na haifar da nakasa ko ma mutuwar yara. Yin rigakafi yana sa yaron ya zama mai kariya daga irin waɗannan cututtuka ta hanyar haɓaka tsarin garkuwar jikinsa, wanda hakan yana sauƙaƙawa garkuwar jiki yaƙar cututtuka dayawa.
Ga jarirai da yara ƙanana, rigakafi ya kasance hanya mafi aminci kuma mafi inganci don kare su daga cututtuka.
Da yake yawancin cututtukan da yara ke iya kamuwa da su suna da tsanani sosai, maganin su ba shi ne mafi cancanta ba. Abu mafi cancanta shi ne, tun da farko yara su kasance masu kariya daga cututtukan. Har ila yau, wasu cututtuka ba su da magani amma ana iya kare su ta hanyar rigakafi, kuma mafi kyawun damar da za a iya magance su shine yin rigakafi da wuri. Babban misali shi ne ciwon hanta wanda ƙwayar cutar hepatitis B yake kawowa.
Yin rigakafi ba kawai yana taimakawa yara ƙanana ba, har ma da duniya gaba ɗaya saboda yana kawar da irin waɗannan cututtuka sannu a hankali, yana sa cutar ta kasance ta daina yaɗuwa a tsakanin al'umma, hakan yana samar da al'umma mai lafiya ta hanyar rigakafi na al'umma. A matsayinku na iyaye, yakamata ku tabbata cewa yaranku sun karɓi rigakafi lokacin da ake buƙata.
A Najeriya, rigakafi ya taimaka sosai wajen shawo kan wasu cututtuka. Kwanan nan ne aka ayyana Najeriya babu cutar shan inna (Poliomyelitis). Abin da hakan ke nufi shi ne, cutar ta daina yin barazana a ƙasar, saboda kasar ba ta da cutar shan inna a cikin shekaru 4 da suka gabata. Irin wannan nasarar ana samun ta ne kawai ta hanyar rigakafi akai-akai ga yara.
Ba a yanzu ne aka fara wannan ba, domin ana iya bibiyar abin tun lokacin da aka ƙaddamar da Faɗaɗɗen Shirin Rigakafi a 1976. Makasudin shirin shi ne a magance matsalar cutar shan inna, kyanda, zazzabin yellow fever, da dai sauransu, ta hanyar rigakafi.
A yanzu labarin ya ɗan canza kaɗan, kuma ribar duk wannan ƙoƙarin a bayyane yake. Yara suna samun rigakafi daga cutar hepatitis, mumps, chickenpox, kyanda, da dai sauransu. A ƙasa, za mu kalli wasu daga cikin waɗannan cututtuka.
Gwamnati ce ke da alhakin Æ™irÆ™ira da sabunta jadawalin da za a bi, kuma ana shawartar iyaye da ma’aikatan lafiya da su bi tsarin da aka tsara a kowane lokaci.
Cutar shan inna: Cutar shan inna cuta ce mai saurin yaɗuwa, cutar tana haifar da gurgujewa, wanda hakan kan sa hannayensu ko ƙafafu su zama marar amfani, yana sa su yi musu wahala su rayu da kansu. Hakanan wannan cutar tana da saurin yaɗuwa, tana iya yaduwa ta gurɓataccen ruwa ko abinci. Ana samun rigakafin cutar shan inna a cikin Najeriya.
Hepatitis: Wannan cuta ce ta hanta, mai alamar kumburin jiki baki É—aya, cutar tana lalata hanta baki É—aya. Mafi yawan nau'ikan da ke shafar yara sune Hepatitis A da B.
Zazzabin yellow fever: Wannan cuta ce ta wani nau'in sauro da ake samu a Afirka da Kudancin Amurka. Cizon wannan sauron yakan haifar da zazzabi mai tsananin gaske kuma yana iya haifar da lalacewar hanta, yana shafar sauran kayan ciki suma.
Mumps: Wannan ƙwayar cuta ce da ke haifar da kumburi a gefen kumatu, zazzaɓi da ciwo kuma tana iya haifar da kumburin ƴaƴan marina.
Zazzabin Typhoid: Wannan wata cuta ce da zata iya kashe mutum kai tsaye idan ba a kula da ita ba. Kwayar cutar salmonella ce ke haifar da wannan cutar, mutane na samun wannan cutar ta hanyar gurɓataccen abinci da ruwa.
Yana da matukar muhimmanci ka ba wa yaronka maganin a cikin ƙayyadadden lokaci. Wadannan alluran rigakafin za su kasance masu mahimmanci ga girma da lafiyar yaron. Hakanan zai ba ku kwanciyar hankali a matsayinku na iyaye, sanin cewa yaranku ba su da kamuwa da cututtuka da yawa.
Idan mai kuna da tambaya sai kuyi a cikin akwatin sharhi dake ƙasa, Insha Allah zamu karba ba tare da jinkiri ba. Haka kuma zaku iya shiga group dinmu na WhatsApp domin kasancewa damu damu a koda yaushe da kuma samun ingantattun bayanan mu a cikin sauki. Ku danna wannan domin shiga: Lafiyata Group 3.
0 Comments