Ad Code

Ticker

6/recent/ticker-posts

Amfanin abarba ga kara lafiyar maza da iyalansu

 Gabatarwa:

Abarba 'ya'yan itace ne da ake samu a wurare masu zafi wanda aka sani da dandano mai dadi da ƙamshi.  Ya fito ne daga Kudancin Amurka, amma yanzu ana noma shi sosai a sassa da yawa na duniya.  Ana iya gane 'ya'yan itacen da sauƙi ta wurin fatar sa ƙaƙƙarfa da siffa ta musamman, wadda aka lulluɓe da kambi na ganye masu kauri tamkar fatar kada.

Abarba 'ya'yan itace ne mai daɗi kuma mai gina jiki wanda ke ba da fa'idodin kiwon lafiya da yawa ga mutane da ma kowane jinsi. Haka kuma, akwai wasu dalilan da ya sa maza, sukan sami fa'idodin kiwon lafiya na musamman daga abarba a cikin abincinsu.


 A cikin wannan shafi na rubuce-rubucen mu, za mu dubi dalilin da ya sa abarba ke da amfani ga maza da kuma yadda za ta iya taimakawa wajen inganta lafiyarsu da jin dadinsu.

 Amfanin Abarba 10 Ga Lafiyar Namiji

 Ga wasu fa'idodin kiwon lafiya da maza za su iya samu ta hanyar shan abarba:

 1. Ƙara motsa sha'awar namiji

 Ana kiran abarba a matsayin "Viagra na asali" saboda yadda take haɓaka sha'awar maza.

 Abarba tana da wadata a cikin manganese, wanda ke taimakawa wajen haɓaka sha'awar jima'i na namiji.  Yawancin lokuta, sha'awar mutum yana dogara ne akan sinadarin manganese da ke cikin jininsa, kuma abarba yana da wadataccen sinadarin manganese da bitamin C. Kofin abarba ɗaya yana ba da 109% na darajar manganese da ake buƙatar mutum ya samu a kullum.

 Duk da yake akwai taƙaitaccen bincike na kimiyya game da batun, wasu bincike sun nuna cewa cin abarba yana yin tasiri mai kyau akan aikin jima'i da motsa sha'awa.

 2. Yana ƙarfafa garkuwar jiki

 Hakanan cin abarba na taimakawa wajen haɓaka garkuwar jikin maza ta hanyar samar da mahimman bitamin, minerals, da enzymes masu mahimmanci ga tsarin rigakafin cututtuka.

 Abarba yana da wadataccen tushen bitamin C, antioxidant wanda ke da mahimmanci ga tsarin rigakafi mai kyau. Vitamin C yana taimakawa wajen samar da fararen tantanin halittun da ke cikin jini, wanda su ne layin farko na kariya daga cututtuka.

 3. Yana haɓaka sinadarin testosterone a cikin jini

 Abarba ya ƙunshi bromelain, bromelain wani enzyme ne wanda yake taimakawa wajen daidaita matakan testosterone a jinin maza.  Testosterone wani muhimmin sinadarin hormone ne da ke sarrafa sha'awar jima'i da kuma ƙarfin jima'in namiji, kiyaye samun lafiyayyen wannan hormone na taimakawa aikin jima'i.

 4. Rage lalacewar tsoka da kumburin motsa jiki

 Abubuwan da ke cikin bromelain na abarba, ban da taimakawa wajen samar da sinadarin testosterone, suna taimakawa wajen inganta farfadowa da rage lalacewar tsokoki da kumburin da yawan motsa jiki ke haifarwa. Haka kuma, abarba yana cike da antioxidants, waɗannan antioxidant sun mai da shi daya daga cikin mafi kyawun 'ya'yan itatuwa ga maza.

 5. Yana haɓaka sinadaran hormones na jima'i ga namiji da haihuwa

 Bincike ya nuna cewa wadataccen antioxidants na abarba ya sa abarba ya zama 'ya'yan itace mai mahimmanci wanda ke inganta matakan ƙwayoyin jima'i da haihuwa.

 Ga mutumin da yake son kara samun haihuwa da kuma ƙarin damar yiwa mace ciki, abarba ita ce mafi kyawun 'ya'yan itacen da ya kamata ya samu.

 Har wa yau, abun cikin abarba na bitamin C yana taimakawa wajen rage tabarbarewar mazakuta da kuma lalaci akan gado. Rahoton 2018  ya tabbatar da cewa abun ciki na bitamin C na abarba yana da fa'ida ga miƙewar azzakari da ƙarfin gaba.

 6. Ƙara ƙarfin jima'i

 Wata fa'idar abarba ga maza ta fannin lafiya ita ce tana ba maza kuzari da ƙarfin jima'i.  Yana ba maza ƙarfin kuzari don dawwama a gado. Abarba tana hana namiji saurin gajiya da jima'i.

 Bugu da kari, yana inganta ƙamshin maniyyi.  Yana ƙara pH na maniyyi, wanda hakan yana sa maniyyi ya fi kyau kuma ya fi dadi.

 7. Taimakawa wajen rigakafin ciwon daji

 Abarba na da wadataccen sinadarin ‘Antioxidants’, irin su Vitamin C da manganese, waɗanda ke taimakawa wajen kare jiki daga lalacewa.  Lalacewar jiki ta hanyar oxidation shine babban sanadin cutar kansa, kuma yawan cin abubuwa masu ɗauke da antioxidants kamar abarba na iya taimakawa wajen rage haɗarin kamuwa da cutar kansa.

 Yayin da ake buƙatar ƙarin bincike da yin nazari don fahimtar alaƙar da ke tsakanin abarba da rigakafin kansa, wasu bincike sun nuna cewa sinadirai da enzymes da ake samu a cikin abarba na iya taka rawa wajen rage haɗarin wasu nau'in ciwon daji, musamman ga maza.

 8. Yana taimakawa wajen narkewar abinci a ciki

 Abarba yana da wadata a cikin bitamin C, fibers, da bromelain waɗanda ke taimakawa ayyukan narkewar abinci a cikin hanji.  Yana hana matsalolin lalacewar ciki kamar bushewar ciki idan aka yawaita shan shi.

 9. Yana rage kumburi da ciwon gaɓɓai

 Kumburi da ciwon gaɓɓai (arthritis) na iya zama mai raɗaɗi da damuwa.  Abubuwan da ke cikin abarba na bromelain suna hana kumburi da ciwon gaɓɓai.

 10. Yana inganta idanunku

 Abarba ya ƙunshi ɗimbin bitamin C da antioxidants masu ɗauke da flavinoids waɗanda ke taimakawa wajen haɓaka gani ta hanyar rage tasirin tsufa akan idanu.  Har ila yau, yana rage haɗarin rashin gani da dare kuma yana inganta hangen nesa.

 Kammalawa

 Abarba na da amfani ga maza sosai ta hanyar jima'i da kuma lafiyar yau da kullum.  Don more fa'idodin kiwon lafiya na sama da abarba ke samarwa ga maza, ku tabbatar da cewa kuna shan abarba ko kuna matsawa mazajenku shan abarba.  Kuna iya shan shi a matsayin ruwan 'ya'yan itacen ko ku ci naman abarba kai tsaye.  Idan kun je sayen abarba ku siye sabo, ku gujewa wanda aka adana ta hanyar sinadarai.

Idan mai kuna da tambaya sai kuyi a cikin akwatin sharhi dake ƙasa, Insha Allah zamu karba ba tare da jinkiri ba. Haka kuma zaku iya shiga group dinmu na WhatsApp domin kasancewa damu damu a koda yaushe da kuma samun ingantattun bayanan mu a cikin sauki. Ku danna wannan domin shiga: Lafiyata Group 3. 

Nassoshi

Print this post

Post a Comment

0 Comments