Ad Code

Ticker

6/recent/ticker-posts

Cututtukan da ke yaɗuwa ta hanyar amfani da gurɓataccen ruwa a Nigeria

Gabatarwa:

 Masana sun ce ruwa, sune rai, in babu ruwa toh babu rai.  Wannan maganar gaskiya ce kawai idan an sami damar samun tsaftataccen ruwan sha.  Ruwa mai datti ko gurɓataccen ruwa, abu ne da ya kamata mutum ya guje shi ta kowane hali.  Ruwan datti ya ƙunshi abubuwa da yawa da ba za ku so a cikin jikin ku ba, kamar ƙwayoyin cuta, ciki har da bacteria, viruses, tsutsotsi, ƙwari da wasu sinadarai masu cutarwa.  Lokacin da irin wannan ruwa ya shiga cikin jikin mutum, zai iya haifar da rashin lafiya da cututtuka.  Cututtukan da ake kamuwa da su ta hanyar ruwa ana kiransu da turanci 'water borne disease' ma'ana cututtukan da ruwa ke haifarwa[¹].


 Kamar yadda muka gani a sama, cututtukan da  ruwa ke haifarwa su ne cututtuka ko rashin lafiyar da ake samu ta hanyar amfani da gurbataccen ruwa. A lura cewa, ba sai ka sha ruwan kafin ka kamu da wasu cututtukan da ruwa ke haifarwa ba.  Yin amfani da ruwan wajen wanke hannu ko yin amfani da shi wajen dafa abinci shima hanya ce ta kamuwa da cutar.  Don haka yana da kyau mutum ya tafasa ruwansa kafin ya sha sannan ya riƙa amfani da sabulu wajen wanke hannu kuma ya tabbata abinci ya dafu sosai[¹].

 A cikin rubutun mu na yau, za mu duba wasu cututtukan da ake yawan samu a cikin ruwa a ƙasar mu ta Najeriya.

 1. Cutar kwalara

 Kwalara cuta ce da ta zama ruwan dare gama gari musamman a nan Najeriya.  Ƙwayoyin cutar bacteria mai suna Vibrio cholerae su ke haifar da cutar kwalara, kuma waɗannan ƙwayoyin suna samun hanyar zuwa ruwa ta hanyar najasa ko duk wani abu da ya gurɓata. Mutanen da suka sha irin wannan ruwan ko amfani da shi wajen dafa abinci za su kamu da cutar kwalara. 

 Kwalara na iya zama mai mutuƙar haɗari idan ba a kula da ita ba, amma 1 cikin mutane 10 ne kawai su ke kamuwa da munanan alamun cutar, a cewar mujallar Lifewater.  Kwalara cuta ce da har yanzu take yaɗuwa a Najeriya, kuma cuta ce da ke faruwa a wani yanayin shekara. Tafi faruwa kowace shekara a lokacin damina kuma mafi yawa a yankunan da ba su da tsafta, wasu daga cikin alamomin cutar kwalara sun hada da amai, tashin zuciya, da gudawa.

 Cutar kwalara ta zama ruwan dare a wurare masu datti da rashin tsafta, kamar a ƙauyuka, inda kuma tafi yawan yaɗuwa, saboda rashin  tsaftataccen ruwan sha wanke hannu da girki.

 Don kiyaye kwalara, yi ƙoƙarin wanke hannunka da kyau da sabulu da ruwa mai tsafta a kowane lokaci.  Akwai wasu hanyoyi masu sauƙi don tsaftace ruwa a gida, ya kamata kowa ya koye  su kuma ya yi amfani da su. A tabbatar da an tafasa ruwan sha kafin a sha, an tafasa nama da kifi kafin aci. A wanke kayan aiki sosai kafin amfani.  Yin duk waɗannan abubuwan zai kiyaye ku da ƙaunatattun ku daga cutar kwalara.

 2. Zawo

 Cutar gudawa wata cuta ce da ke yaɗuwa ta hanyar amfani da gurɓataccen ruwa.  Yana faruwa sanadiyyar nau'ikan ƙwayoyin cuta da yawa waɗanda ke zama a cikin ruwa.  Kodayake yana shafar mutane masu shekaru daban-daban, yafi shafar yara ƙanana. Alamomin gama gari sun haɗa da ganin juwa, yawan gudanawa, farin fata, rashin ƙwarin jiki da rasa hayyaci a lokacin da zawon ya tsananta. Yana iya kaiwa ga mutuwa idan ba a bada kulawa a cikin lokaci ba.

Don kare aukuwar cutar gudawa, yakamata ku ɗauki tsaftar  ku da mahimmanci ta hanyar tabbatar da cewa muhallinku yana da tsafta.  Har ila yau, ku tabbatar da cewa ruwan da kuke amfani da shi yana da tsafta kuma mai kyau ne.

 3. Zazzabin Dengue

 Wannan wata cuta ce da ake kamuwa da ita ta hanyar ruwa.  Cutar tana yaɗuwa ta hanyar macen sauro  da ake kira Aedes aegypti (wani sauro ne daga dangin Aedes). Duk da cewa sauro ne ke yaɗa wannan cutar, amma waɗannan sauro suna hayayyafa a cikin ruwa. Wannan ya sa cutar ta zama ruwan dare gama gari a wuraren da suke amfani da ruwa mai datti.  Wannan cuta da tana wanzuwa har yanzu a Najeriya, an ce tana shafar dubunnan 'yan Najeriya a duk shekara. Alamominta sun haɗa da zazzabi, ciwon kai, tashin zuciya, da sauransu.[¹][²].

 Don kiyaye kanku daga zazzabin dengue, ku share ko'ina da ko'ina na muhallin ku don hana ko wane irin sauro yawo a kusa da ku. Kuyi amfani da magungunan sauro, kuma ku dinga barci a ƙarƙashin gidan sauro.

 4. Zazzabin typhoid

 Hakanan ita ma cutar zazzaɓin typhoid tana yaɗuwa ne ta hanyar gurbataccen ruwa. Ƙwayoyin cutar bacteria dangin Salmonella typhi da Salmonella paratyphi su ke kawo cutar zazzaɓin typhoid, kuma duk ana samun su ne ta hanyar gurɓataccen ruwa. Haka kuma cutar tana da saurin yaɗuwa, ma’ana idan mutum daya ya same shi, aka bar shi ba a yi masa magani ba, za a iya samun bullar cutar a tsakanin al’umma.  Wasu daga cikin alamomin cutar sun haɗa da zazzabi, ciwon jiki, ciwon ciki, ciwon kai, maƙarƙashiya, rashin cin abinci da dai sauransu.

 Don hana kamuwa da cutar zazzaɓin typhoid, a guji shan duk wani ruwan da ba a cikin kwalba ko a rufe ba, kuma kada ku ci abinci daga gidajen abinci marasa tsafta ko masu siyar da abinci a titi.  Duk da haka, magance shi yana da sauƙi saboda akwai maganin rigakafi[²].

 5. Ciwon hanta na hepatitis A

 Hepatitis A cuta ce da ke shafar hanta kuma ana samunta ta hanyar shan gurbataccen ruwa.  Hakanan ana iya kamuwa da ita ta hanyar saduwa da wanda ke dauke da cutar saboda cutar tana da saurin yaɗuwa. Alamomin cutar sun haɗa da tashin zuciya, rashin cin abinci, zazzabi, ɗorawar idanu da dai sauransu.

 Don hana ciwon hanta da ƙwayoyin cutar virus na hepatitis A ke kawo wa, a tafasa ruwa kamin a sha, haka kuma a dafa abinci sosai kamin aci  Ko da yake, hanya mafi kyau don rigakafin cutar hanta ta hepatitis A ita ce hanyar yin alluran rigakafin cutar.

 6. Ciwon ciki

 Daya daga cikin cututtukan da gurɓataccen ruwa yake haifarwa a Najeriya shine ciwon hanji da aka fi sani da dysentery. Dysentery cuta ce da ke haifar da ciwon ciki hade da zawo mai tsanani, tare da jini da majina a cikin zawon.

 Don gujewa kamuwa da cutar dysentery, dole ne a rika wanke hannu ko da yaushe, domin wannan cuta ta ruwa tana yaduwa ta hanyar rashin tsafta.  Ana iya samun shi ta hanyar ƙwayoyin cuta waɗanda ke cikin abinci da ruwa marasa tsafta.  Hakanan ana iya samun wannan cuta ta hanyar haɗuwa da najasar bayan gari. Dysentery na iya zama mai tsanani idan marar lafiya ba zai iya maye gurbin ruwan da ya rasa ta hanyar zawo da sauri ba.

Kammalawa

 Don guje wa waɗannan cututtuka da amfani da gurɓataccen ruwa yake haifarwa ya kamata a rinka wanke hannunwa da sabulu ko amfani da abin wanke hannu akai-akai. Mutum ya rinƙa shan ruwan kwalba yayin tafiya zuwa yankin karkara. Kuma ku sha ruwan leda daga sanannun kamfanonin ruwan leda da ke kusa da ku kawai.

Idan mai kuna da tambaya sai kuyi a cikin akwatin sharhi dake ƙasa, Insha Allah zamu karba ba tare da jinkiri ba. Haka kuma zaku iya shiga group dinmu na WhatsApp domin kasancewa damu damu a koda yaushe da kuma samun ingantattun bayanan mu a cikin sauki. Ku danna wannan domin shiga: Lafiyata Group 3. 

Nassoshi


Print this post

Post a Comment

0 Comments