Yadda ake bada agajin gaggawa ga mutanen da suka yi hatsarin ababen hawa

 Gabatarwa:

Hatsarin mota abu ne mai muni da yawa wanda ke haifar da wasu munanan raunuka har ma da mutuwa(1). A Najeriya, hukumar kiyaye haÉ—urra ta kasa (FRSC)  ta fitar da rahoton  cewa suna samun haÉ—urra 826 a fadin kasar cikin wata daya(2). A wasu lokuta, mutanen da ke mutuwa sakamakon hatsarin mota ba sa mutuwa daga yin hatsarin kai tsaye, amma suna mutuwa ne bayan mintuna ko ma sa'o'i saboda rashin kulawa da ya kamata. Mafi yawanci akwai tazara mai nisa tsakanin asibiti mafi kusa da wuraren da hatsari ke faruwa, gashi mutanen da ke taruwa don taimaka wa waÉ—anda hatsarin ya shafa ba su san Æ™a'idar abin da za su yi don taimaka musu ba.  Wannan shi ya sa samun kyakkyawan horo game da matakan taimakon farko na gaggawa da za a É—auka bayan hatsarin hanya yana da mahimmanci sosai ga kowa da kowa.



Bayar da maganin gaggawa nan da nan bayan wani hatsari na iya taimakawa ceton rayuka har ma da hana munanan raunuka ko abubuwa kamar yanke wa. Ba dole ba ne mutum ya zama likita ko nas ko mai ba da agajin gaggawa kafin ya iya ba da agajin farko na gaggawa. Mutum yana buƙatar kawai sanin abin da zai yi ne(2).

 Anan, za mu duba wasu taimakon agajin gaggawa da za ku iya ba wa waÉ—anda hatsarin mota ya shafa.

1. Zuwa Wurin da Hatsarin ya Auku

 Lokacin da kuka gamu da hatsari kan hanya, abu na farko da kuke buÆ™atar sani shine ko wurin yana da amincin da zaku iya shiga kamin yunÆ™urin shiga ku ba da agajin farko.  Wannan shi ne don tabbatar da amincin ku da farko kamin taimakawa waÉ—anda suka jikkata.

 2. Kira a asibiti ko lambar taimakon gaggawa 

 Abu na gaba da ya kamata ku yi kafin ku fara Æ™oÆ™arin taimakawa shine ku kira asibiti mafi kusa da zaran kun ga hatsarin mota. Ku fahimci cewa taimakon farko magani ne na É—an lokaci kuma za a garzaya da waÉ—anda abin ya shafa asibiti bayan haka.  Don haka, kafin lokacin da motar daukar marasa lafiya ta zo, shi ne lokacin da ya kamata ku yi taimakon farko.

 3. Ka Fara Bincika Mutane Masu Munanan Raunuka

 Abu na gaba, yakamata ku bincika mutanen da suka ji rauni sosai. Ba kowane hatsarin mota ke haifar da munanan raunuka ba.  Fasinjojin na iya samun Æ™ananan raunuka da karce. Amma babu yadda za a yi ka san hakan sai dai idan ka tantance halin da waÉ—anda abin ya shafa suke.  Yawancin lokaci, mutanen da suka ji rauni su ne waÉ—anda ke da wahalar amsa kira. Hakanan suna iya zubar da jini sosai kuma suna nishi saboda tsananin zafi. WaÉ—annan su ne mutanen da ke buÆ™atar kulawa nan da nan. Ku fara taimakawa mutanen da basa iya yin magana, ko kuma basa motsi domin su ke buÆ™atar taimako na gaggawa domin ceton rayuwarsu, kamin ku taimakawa masu ihu da kururuwa suna faÉ—in ku taimake su(1).

 4. Kada Ka Yi ƘoÆ™arin Matsar da waÉ—anda abin ya shafa ko canja musu wuri

 Abu daya da ya kamata ku guji yi shine Æ™oÆ™arin motsa mutanen da suka ji rauni.  Motsawa ko canza matsayinsu zai iya haifar da É“arna fiye da yadda kuke tsammani.  Ka bar su a daidai inda suke, sai dai in suna wuri mai matuÆ™ar haÉ—arin gaske, kamar a kan titi ko kuma inda wuta ta kama. Maimakon matsar da su kuna iya share duk wani cikas ko wani abu da zai iya haifar musu da rashin jin daÉ—i.  Kuna iya kwance aninansu ko buÉ—e rigarsu.  Amma kada ku yi Æ™oÆ™arin canza musu wurin da suke(2).

 5. Matakan Taimakon Farko

 Akwai matakan taimakon farko da za ku iya gwadawa don taimaka wa mutum wanda ke raye. Da farko shi ne kuyi ma mutum magana, idan har ya karÉ“a to baya da matsalar numfashi. Idan mutum yana da matsala ta numfashi za ku iya gwada farfaÉ—o da shi ta hanyar duba bakinsa da hancinsa ku cire jini ko duk wani abu da zai toshe sa ya hana masa numfashi. Idan kunyi haka kuma bai fara numfashi ba to a nan kuna iya fara bada numfashin baki-da-baki ko baki-da-hanci (wanda aka fi sani da CPR) don samun kulawar numfashin mutum.  Amma ya kamata ku yi haka kawai idan kun san yadda ake yi.

 6. Dakatar da zubar Jini

 Wani abu da za ku iya yi don taimakawa shi ne dakatar da zubar da jini, idan akwai wani mai zubar da jini.  Kuna iya É—aura wani zane a saman hannu ko Æ™afar da ke zubar da jini tare da matsi sosai. Wannan zai taimaka wajen shawo kan zubar da jini.  Idan kuna da akwatin taimakon farko a kusa da ku, zaku iya Æ™oÆ™arin bakara raunuka da ruhi, amma kuyi haka don Æ™ananan raunuka da yankewa kawai.

Kammalawa

WaÉ—annan matakai da muka lissafa a sama su ne abubuwan da ya kamata kowa ya sani kuma ya iya domin ceton yan'uwa watarana. Ba dole sai ma'aikatan lafiya ba kowa ma zai iya taimakawa. Allah ya tsare mu baki É—aya.

Idan mai kuna da tambaya sai kuyi a cikin akwatin sharhi dake Æ™asa, Insha Allah zamu karba ba tare da jinkiri ba. Haka kuma zaku iya shiga group dinmu na WhatsApp domin kasancewa damu damu a koda yaushe da kuma samun ingantattun bayanan mu a cikin sauki. Ku danna wannan domin shiga: Lafiyata Group 3. 

Nassoshi

1. Emmy De Buck, Hans Van Remoortel, Tessa Dieltjens, Hans Verstraeten, Matthieu Clarysse, Olaf Moens, Philippe Vandekerckhove, Evidence-based educational pathway for the integration of first aid training in school curricula, Resuscitation, Volume 94, 2015, Pages 8-22, ISSN 0300-9572.
 https://doi.org/10.1016/j.resuscitation.2015.06.008 (https://www.sciencedirect.com/science/article/pii/S0300957215002531)

Post a Comment

0 Comments