Gabatarwa:
Wannan tambaya ce da mutane da yawa ke yi akai-akai. To bincike ya nuna duk da cewa yawan fitar da maniyyi ba ya haifar da babbar matsala ga jikin É—an adam, amma adadin lokutan da mutum ya ke fitar da ruwan maniyyi, zai iya shafar lafiyarsa.
Haka kuma babu wata shaida da ta ce rashin fitar da maniyyi na tsawon lokaci yana haifar da wata matsala ta kiwon lafiya, amma bincike ya nuna fitar da maniyyi akai-akai yadda ya kamata na iya rage barazanar kamuwa da cutar sankara ta prostate, kamar yadda saduwa ta aure mai gamsarwa na iya inganta lafiyar mutum(1).
A cikin wannan rubutun, za mu dubi sau nawa mutum ya kamata ya fitar da maniyyi, da kuma mene ne matsalar ko illar fitar da maniyyi akai-akai ko da yaushe.
Yawan fitar da maniyyi kullum
Da farko dai, fitar da maniyyi kullum ko lokaci-lokaci tsari ne na halitta da na al'ada(1).
Wasu masu bincike suna da'awar cewa babu wani adadin da ya kamata namiji ya fitar da maniyyi. Wani bincike ya nuna cewa yara samari 'yan tsakanin shekaru 14 zuwa 17 dayawa suna yin wasa da al'aurarsu har su kawo maniyyi. Duk da cewa yana da kyau a rika fitar da maniyyi daga jiki, amma fitar da maniyyi kullum kullum ta hanyar wasa da al'aura ko jima'i yana iya kawo ƙarancin wasu sinadarai masu amfani a jikin mutum. Bugu da ƙari, yawan wasa da al'aura har a fitar da maniyyi ko yin istimna'i har ayi inzali akai-akai yakan iya haifar da ciwon ƙwaƙwalwa. Kuma yakan iya zama jaraba mutum ya kasa dainawa ko da yayi aure.
Samuwar maniyyi abu ne da ke faruwa da kan sa a cikin jikinmu ba tare da saninmu ba. Babu wani matsala don an fitar dashi, amma idan ana fitar dashi shi kowace rana, tabbas hakan ba shi da kyau.
Mai fitar da maniyyi fiye da sau 3 yau da kullum zai iya samun cuta ta hankali musamman idan yana fitarwa ne ta hanyar wasa da al'aura ko istimna'i. Yin wasa da al'aura ko kuma istimna'i yau da kullum yana da haÉ—ari saboda yana iya shafar rayuwar mutum kuma ya karkatar da hankalin sa daga burin sa.
Haka zalika, masana sun tabbatar da cewa fitar da maniyyi sau biyu ko sau uku a kullum yana iya haifar da, raunin tunani, yawan mantuwa da kuma daƙushewar basira.
Fitar da maniyyi aiki ne mai buƙatar kuzari da ƙarfin jiki, saboda haka yawwn fitar da maniyyi sau biyu ko uku ko ma fiye da haka a rana ɗaya yana haifar da gajiyar jiki. Wani lahani da zai iya aukuwa sanadiyyar sakin maniyyi sau da yawa kullum, shine yana haifar da karancin sinadarin zinc a jiki.
Kowa ya sani cewa sinadaran protein da zinc sune abubuwa masu mahimmanci a cikin ruwan maniyyi. Sinadarin zinc sinadari ne da jiki bazai iya samar dashi ba dole sai mutum ya same shi ta hanyar abincin da yake ci, kuma sinadarin yanada wahalar narkewa. Ana fitar da mafi yawan miligram 3 na zinc lokacin fitar da maniyyi. Dole ne mutum ya rage yawan lokutan da yake yin istimna'i ko fitar da maniyyi saboda shan sinadarin zinc ba shi da sauƙi don yana da ƙarancin nutsewa a cikin jiki.
Wani bincike da aka yi a shekarar 2015 ya bayyana cewa mazan da ke fitar da maniyyi a kullum har na tsawon kwanaki goma sha hudu a jere, yawan maniyyin da suke fitarwa ya ɗan ragu. Alhamdulillahi, raguwar bai sa adadin maniyyinsu ya faɗo ƙasa da adadin da ake buƙata domin yi wa mace ciki ba. Kuma hakan bai shafi wasu matakan lafiyar maniyyinsu ba.
Amma duk da haka, fa'idodin fitar da maniyyi yadda ya kamata sun haÉ—a da rage haÉ—arin cutar kansar prostate ga mazan da ke tsakanin shekaru 40-49. A lura cewa bincike bai nuna cewa yawan fitar da maniyyi yane kare samari daga haÉ—arin ciwon daji na prostate ba(2).
Kada maza su samu damuwa da samar da maniyyi domin jiki kullum yana samar da maniyyi yadda ya kamata, saboda haka, yawan fitar da maniyyi baya haifar ƙarancin maniyyin da zai iya hana namiji haihuwa. Duk da cewa yana ɗaukar maniyyi aƙalla kwanaki saba'in da huɗu kamin ya gama girma, jiki yana samar da miliyoyin maniyyi a kowace rana(2).
A taƙaice, kuma a kimiyance babu daidai adadin da ya kamata mutum ya kama fitar da maniyyi, wannan ya danganta daga wani mutum zuwa wani. Duk da cewa sakin maniyyi akai-akai yana ba da fa'idodi da yawa na kiwon lafiya, babu wata hujja da ta nuna cewa rashin sakin maniyyi lokaci-lokaci yana haifar da wata matsalar kiwon lafiya. Haka kuma sakin maniyyi fiye da ƙima kamar sau biyu zuwa uku kulli-yaumin yana gajiyar da jiki da kuma ƙwaƙwalwa kamar yadda mukayi bayani a sama(2).
Kammalawa
Don amsa tambayar: shin ko akwai matsala na sakin maniyyi kullum? Amsar za ta kasance E da A’a. E, domin yana iya haifar da gajiyar jiki da Æ™waÆ™walwa da rage yawan maniyyi (ragewar bata haifar da Æ™arancin maniyyi), da kuma haifar da jaraba. A'a, saboda babu wasu matsalolin kiwon lafiya masu tsanani da ke samuwa sanadiyyar sakin maniyyi kullum.
Idan mai kuna da tambaya sai kuyi a cikin akwatin sharhi dake ƙasa, Insha Allah zamu karba ba tare da jinkiri ba. Haka kuma zaku iya shiga group dinmu na WhatsApp domin kasancewa damu damu a koda yaushe da kuma samun ingantattun bayanan mu a cikin sauki. Ku danna wannan domin shiga: Lafiyata Group 3.
0 Comments