Gabatarwa:
A rubutun da mukayi a baya game da gyambon ciki mai taken "Alamomi da ingantaccen maganin gyambon ciki ko ciwon ulcer". Munyi bayani dallah-dallah game da ciwon gyambon ciki, alamomin shi abubuwan da ke kawo shi da kuma yadda ake maganinsa a asibiti. Sai dai ciwon gyambon ciki ciwo ne da baya warkewa kai tsaye idan ba'a kiyaye abubuwan da ke haifar da ciwon da kuma abubuwan da ke harzuƙa shi ba. Wannan shi yasa wasu mutane suke tunanin ciwon ma baya warkewa baki ɗaya saboda sunyi ta neman magani amma ba'a dace ba. Idan har mutum yana so ya warke daga cutar gyambon ciki ya zama dole bayan fara shan magani yasan abubuwan da ke haɓaka ciwon da kuma abubuwan da ke kawo ciwon sannan ya nisance su. Wannan shi yasa a cikin wannan rubutu zamu kawo muku jerin abubuwan da ya kamata ku nisanta idan kuna ɗauke da ciwon gyambon ciki domin warkewa.
Yayin da ake amfani da magunguna akai-akai don magance cututtukan gyambon ciki da kuma Helicobacter pylori, gyare-gyaren abinci da sauya salon rayuwa na iya taimakawa wajen rage bayyanar alamomin ciwon da kuma hanzarta waraka dagareshi. Ya kamata duk masu cutar gyambon ciki su guji wasu kalolin abinci na musamman tunda suna iya ƙara haɓaka cutar da kuma kawo jinkirin warkewa. Nau'ikan abincin sun ƙunshi:
1. Abinci mai yaji
Mafi munin abincin da za a ci tare da cutar gyambon ciki shine abinci mai yaji. Abincin yaji yana tsananta alamun gyambon ciki, kamar tashin zuciya, kumburin ciki, da ciwon ciki. Kuyi tunanin abinda zai faru idan kuna da gyambo a jikin fatar ku ta waje sai kuka zuba masa yaji, toh balle gyambon cikin ciki.
2. Soyayyen abinci
Soyayyen abinci musamman mai kitse dayawa yana samun ƙalubalen narkewa, wanda hakan zai iya harzuka fatar cikin ku kuma ya ƙara tsananin zafin gyambon ciki.
3. Abincin mai sinadarin acid
'Ya'yan itacen Citrus da tumatir abinci ne masu ɗauke da sinadarin acid wanda zai iya ƙara samar da acid na ciki da kuma tsananta alamun gyambon ciki, musamman ma idan kuna samun ƙwarnafi. Saboda haka ba'a shan waɗannan abubuwan zallarsu. Shan miyar tumatir bayada illah, amma ba'a son shan tumatir ɗanye kai tsaye.
4. Kaya masu maiƙo
Wasu masu fama da gyambon ciki na iya zama marasa jure wa lactose, wanda ke nufin cin irin waÉ—annan kayan na iya sa su ji rashin lafiya ga cikinsu kuma ya haifar da gudawa, da kumburin ciki.
5. Abubuwan sha masu iskar gas
Abubuwan sha masu ɗauke da iskar gas na iya ƙara alamun cutar gyambon ciki, musamman idan kuna da ciki marar kyau, saboda suna iya haifar da kumburin ciki, yawan gyashi ko gyashin magus.
6. Abubuwan Sha masu É—auke da Caffeine
Alamun cutar gyambon ciki, irinsu zafin zuciya, ƙwarnafi, da rashin jin daɗin ciki, na yin muni saboda shan abubuwa masu sinadarin Caffeine. Sinadarin Caffeine yana haɓaka samar da acid a acikin ciki. Abubuwan da ke ɗauke da Caffeine sun ƙunshi: Lipton, Coffee, Black tea, Nescafe da dai sauransu.
7. Barasa
Barasa na iya tsananta kumburin ciki da kuma ƙara samar da acid a cikin ciki, wanda zai iya tsananta alamun gyambon ciki, kamar tashin zuciya, amai, ƙwarnafi da ciwon ciki.
8. Abincin da aka sarrafa
Ɗaya daga cikin abincin da ba za ku ci ba idan kuna da gyambon ciki shi ne abincin da aka sarrafa dayawa. Kamar irin abincin da aka soya akai-akai, abinci mai yawan sukari, abinci mai yawan gishiri, da abinci mai yawan kitse. Waɗannan nau'ikan abinci zasu iya harzuka fatar tumbi a cikin cikinku sannan su ƙara alamun gyambon ciki.
9. Jan nama
Ba'a son mai cutar gyambon ciki ya faye cin jan nama, saboda jan nama na iya samun ƙalubale wajen narkewa kuma yana iya ƙara samar da acid a cikin ciki, hakan yana tsananta alamun gyambon ciki, kamar kumburin ciki da ciwon ciki.
10. Kayan zaki na wucin gadi
Abubuwan zaki da ake amfani da su na wucin gadi, kamar aspartame da sucralose, na iya harzuƙa gyambon ciki da dagula alamun ciwon ulcer na wasu mutane.
11. Chocolate
Musamman, idan kun taɓa fuskantar zafin zuciya ko ƙwannafi, ba'a son mai gyambon ciki na yawan cin chocolate. Saboda mafi yawancin chocolate suna ɗauke da sinadarin Caffeine wanda mukayi bayani a baya yana haɓaka samar da acid a cikin ciki. Hakan na iya sa alamun gyambon ciki su yi muni.
12. Wasu É—anyun kayan lambu
Danyen kayan lambu na iya zama da wahala wajen narkewa kuma su harzuƙa fatar cikin ku idan kuna da gyambon ciki, musamman idan suna da sinadarin fiber mai yawa ko suna ɗauke da fatu masu tauri kamar ɗanyen alayyafu, latas, mangoro da gwaiba. Dafa kayan lambu irin su alayyafu na iya sa su narke a cikin sauki kuma ba za su iya haifar da rashin jin daɗi ba.
Bugu da kari, akan abubuwan da bai kamata ku ci ba idan kuna da gyambon ciki akwai abubuwa na salon rayuwa da suke sa ciwon gyambon ciki ya ta'azzara. Kamar irin su:
13. Shan taba (sigari)
Shan taba yana cutarwa sosai ga wanda ya kamu da gyambon ciki. Yana iya harzuka fatar ciki, yana haifar da kumburi da rashin warkewar gyambon ciki ko da ana shan magani yadda ya kamata.
Barin shan taba yana da amfani sosai ga mutanen da ke da gyambon ciki. Hakan zai iya taimakawa wajen rage tsananin alamun bayyanar cututtuka da kuma hanzarta warkewa.
14. Damuwa da gajiya
Alamun gyambon ciki na iya ƙara tsanantuwa a lokacin gajiya da damuwa. A lokacin gajiya da damuwa jiki yana samar da sinadarin hormone na cortisol, wannan sinadarin hormone din yakan haɓaka samar da sinadarin acid a cikin ciki. Wannan na iya haifar da ƙarin bayyanar ciwon gyambon ciki kamar tashin zuciya, ciwon ciki, da gudawa.
15. Magungunan kashe ciwon jiki dangin NSAIDS
16. Magungunan antibiotics
Kodayake ana yawan amfani da magungunan antibiotics don magance cututtukan H. pylori da sauran cututtuka, amma waɗannan magungunan idan an faye amfani da su suna iya yin illa ga tsarin narkewar abinci, gami da sanya gudawa da kumburin ciki. Hakanan suna iya dagula ma'aunin ƙwayoyin bacteria masu amfani da ke cikin hanji.
Kammalawa
Don sarrafa alamomin gyambon ciki da kuma inganta warkewa daga cutar, mutanen da ke da ciwon gyambon ciki ya kamata su yi hankali game da abincin da suke ci. Abincin da zai iya tsananta alamomin da ke da alaƙa da gyambon ciki sun haɗa da abinci mai yaji, abincin da aka sarrafa dayawa, barasa, kayan abinci masu maiƙo, abinci mai ɗauke da sinadarin acid da kuma abinsha mai ɗauke da Caffeine. Don haka ya kamata masu fama da wannan cutar su guji waɗannan abubuwan ko suyi taka tsantsan wajen amfani da su.
Bugu da ƙari, rage gajiya da damuwa, barin shan taba, da nisantar magungunan kashe ciwon jiki na NSAIDs na taimakawa wajen samun sauƙi da warkewa baki ɗaya daga cutar gyambon ciki.
1 Comments
Alhmd mungode
ReplyDelete