Ad Code

Ticker

6/recent/ticker-posts

Alamomin gargaɗi masu nuna ciwon zuciya

Gabatarwa:

Kana neman alamomin gargaɗi masu nuna zuciyarka bata aiki yadda ya kamata? Dubban mutane na mutuwa a kowace shekara dalilin cututtukan da ke da alaƙa da zuciya ko bugawar zuciya.

Cibiyar kula da cututtuka (CDC) ta bayyana cewa kimanin mutane 610,000 ke mutuwa a kowace
shekara sakamakon bugawar zuciya kawai a
Amurka, don haka yanzu za ku iya tunani da kanku game da yanayin duk duniya.

Ciwon zuciya na iya kama maza da mata; zai iya bayyana da wuri idan kuna da yanayin gudanar da rayuwa mara kyau kamar irin yawan cin kitse da rashin motsa jiki da kuma yanayin jiki mara kyau kamar ƙiba da taiɓa.

Mafi yawan mutane suna watsi da waɗannan
alamomin gargadi wanda hakan yana gayyato babbar matsala. Duk da cewa ciwon zuciya yana faruwa saboda wasu dalilai dayawa, amma salon gudanar da rayuwarku ta yau da kullum yana matuƙar taka rawar gani.



A wannan rubutun, za mu yi tsokaci akan wasu alamun gargadi da ke faruwa da wuri masu nuna zuciyar mutum ba ta aiki yadda ya kamata. ldan kuna so ku samu ingantacciyar fahimta domin kare kanku daga ciwon zuciya toh ku daure ku karanta rubutun har zuwa ƙarshe.

Alamomin Gargadi masu nuna ciwon zuciya

1. Ciwon ƙirji da yake shafar hannun hagu

Ciwon ƙirji mai raɗaɗi da yake tasowa daga ƙirji zuwa sashen hannun hagu babban alamu ne na ciwon zuciya. Wasu lokuta maza suna jin raɗaɗi a hannunsu na hagu kawai, amma mata suna jin zafi kamar haka a gwiwar hannu da damtsen su. Wannan ciwon yana ta'azzara idan mutum yayi wani ɗan aiki, haka kuma akan samu sauƙin sa yayin hutawa.

2. Matsalar tari akai-akai

Mutum na iya samun matsalar tari saboda
dalilai da yawa, amma idan ana samun fitowar majina da jini ko majina mai kumfa sosai, to wannan na iya zama alamar cewa zuciyarka ba ta aiki yadda ya kamata.

3. Kumburin ƙafafu ko kumburin jiki da ya fara daga ƙafafu

Babban aikin zuciya shi ne karɓan jini daga sauran sassan jiki domin ta harba jinin zuwa cikin huhu a inda zai haɗu da iskar oxygen, haka zalika, zuciya ce za ta kuma karɓo jinin da aka sanyawa iskar oxygen daga huhu ta sake harba shi zuwa sauran sassan jiki. Idan har zuciya ta fara gazawa ba za ta iya karɓan dukkan jinin da yake zuwa mata daga sassan jiki ba, wannan yana haifar da tsaiko ga komawar jini a zuciya. Wannan tsaiko zai sanya ruwan da ke cikin jini su bar jijiyoyin jini su fara taruwa a ƙafafu. Taruwan wannan ruwan zai haifar da kumburi wanda idan abu yayi tsanani zai iya sa dukan jiki ya kumbura.

4. Wahalar numfashi

Kamar yadda mukayi bayanin aikin zuciya a sakin layi da ke sama, idan har zuciya ta fara gazawa ba za ta iya karɓan dukkan jinin da yake zuwa mata daga huhu ba, wannan zai sa jini ya koma ya taru a cikin huhu ya haifar da wahalar numfashi.

Wahalar nunfashin da ke faruwa sakamakon gazawar zuciya yana ƙaruwa sosai idan mutum yayi aiki ko da ƙanƙani ne, haka kuma yana ƙaruwa a lokacin da mutum ya kwanta rairam ba tare da yayi amfani da pillow ba. Wanda ke da gazawar zuciya mai tsanani baya iya yin bacci sai da pillow. Watarana wahalar numfashin takan iya ta da shi daga bacci.

5. Rashin cin abinci da tashin zuciya

Mutanen da ke fama da cutar da ke da alaka
da zuciya suna fuskantar rashin sha'awar cin abinci. Kuma akai-akai zasuji sun ƙoshi ko da kuwa sun ci abinci kadan ne ko kuma basu ma ci komai ba.

Wannan matsalar tana faruwa ne saboda hanta na kewaye da ruwan da muka yi bayanin suna ficewa daga jijiyoyin jini a ɗazu. Hanta ita ce keda alhakin narkar da abinci da kuma adana shi a matsayin sinadarin glucose domin samar da ƙarfin jiki da kuzarin aiki. Idan wannan ruwa ya kewaye hanta yana hana ta yin aikinta kuma yasa ta kumbura, wannan kumburin zai iya haifar da ciwon ciki a ɓangaren ciki na dama.

6. Jiri da kuma ji kamar mutum zai suma

Suma na wani ɗan lokaci kaɗan ko samun jiri alamu ne na gargadi cewa zuciyarka ba ta aiki
yadda ya kamata.

Idan kana jin wahalar numfashi kuma kana samun jiri ba tare da wani dalili ba, kuma hakan yana faruwa sau da yawa, to lokaci ya yi da za
ka ziyarci likitanka da sauri.

7. Ƙarin hasken fata ko duhun fata ko kuma rikiɗewar fata zuwa kalan bula

Ƙarin hasken fata ba wata alama ce mai muhimmanci da ke nuna ciwon zuciya ba amma ana iya samun ta ga masu ciwon zuciya, wannan alama tana nuna ƙarancin jini a jikin mutum.

Ƙarin duhun fata ko rikiɗewar fata musamman fatar leɓɓa da cikin baki zuwa kalan blue yana faruwaa ne a lokacin da iskar oxygen tayi ƙaranci a cikin jinin mutum, wannan babbar alama ce ta ciwon zuciya da ciwon huhu. An fi samun wannan alama ga ƙananan yara masu ciwon zuciya da manya masu ciwon huhu.

8. Yawan faɗuwar gaba

Yawan faɗuwar gaba ba tare da dalili ba shima yana ɗaya daga cikin alamomin cututtukan zuciya. Duk da cewa akwai wasu cututtuka masu kawo wannan alama.

9. Yawan saurin gajiya

Duk da cewa akwai abubuwa da yawa da ke da alhakin gajiya ko gajiya mai yawa. Amma idan kana jin gajiya kwatsam ko da baka yi aikin komai ba ko kuma kana yawan samun gajiya da wahalar numfashi daga kayi yunƙurin aiki ɗan kaɗan kamar tafiya kaɗan ko hawan bene, toh wannan alama ce ta gazawar zuciya.

10. Yawan zufa a kowane lokaci

Ana kuma ƙirga yawan zufa ko gumi a matsayin alamar gargadi na matsalolin zuciya musamman ga yara ƙanana masu shan nono. Duk da cewa mutum na iya samun gumi a lokacin zazzabi, yanayin zafi, ko wani dalili na daban.

Kammalawa

Zuciyar ka ita ce mafi muhimmanci a jikinka, kuma lafiyarta itace mafi muhimmanci a lafiyar gaɓɓan jiki, saboda haka kula da lafiyar ta ya zama wajibi. 

Gane ciwon zuciya tunda sauri da ɗaukar matakan da suka dace na ɗaya daga cikin hanyoyin riga-kafi da kuma hana ciwon yiwa mutum illah, riga-kafi tafi magani inji malam Bahaushe. don haka muna fatan wannan rubutun zai taimaka maka wajen lura da fadakarwa tare da sanar da abokai da yan'uwa game da wadannan alamomin gargadi don kare abubuwan da suka shafi zuciya.


Idan kuna da tambaya sai kuyi a cikin akwatin sharhi dake ƙasa, Insha Allah zamu karba ba tare da jinkiri ba. Haka kuma zaku iya shiga group dinmu na WhatsApp domin kasancewa damu damu a koda yaushe da kuma samun ingantattun bayanan mu a cikin sauki. Ku danna wannan domin shiga: Lafiyata Group 3. 

Nassoshi


Print this post

Post a Comment

0 Comments