Wadannan magungunan na steroids artificial forms ne na sinadarin hormone na cortisol, shi kuma sinadarin hormone na cortisol wani sinadari ne da glands din da ke saman ƙoda yake samar wa domin taimakawa mutane a wurin abubuwa kamar haka:
- Taimakawa mutane a manejin stress (gajiya)
- Taimakawa wajen narkar da abinci da sarrafa shi a cikin jini
- Taimakawa garkuwar jiki
Magungunan na steroids suna daya daga cikin magungunan mafi hatsari masu arha da mutum zai iya samu a shagunan magani a yanzu. Asali an ƙirƙire su ne saboda wasu cututtuka da ake kira chronic inflammatory conditions, kamar irin su cutar garkuwar jiki ta Lupus , cutar asthma, ciwon gaɓɓai na arthritis, wasu cututtukan kansa da dai sauran abubuwa dayawa.
Wannan shi yasa magungunan steroids suna daga cikin magungunan da ake kira "controlled drugs," ma'ana, magungunan da mutum ba zai iya siya da kansa ba sai ya nuna takardan shaidar cewa likita ne ya rubuta.
Duk da haka akwai wasu kalan magungunan steroids da ake shafawa wanda mutum zai iya samu ba tare da takardar shaida ba, haka kuma, akwai steroids din da ake shaƙawa kamar irin wadanda ake maganin asthma dasu, wadannan duka basu da wani illa sosai saboda basu ɗauke da sinadarin dayawa a cikin su.
Ana amfani ne da steroids na shafawa a wurin magance wasu ƙurajen fata, ƙaiƙayin jiki da kuma wasu inflammatory conditions na fata. Amma duk wasu magungunan steroids wadanda za'a sha ko za'a yi alluran su, toh baya dacewa ayi amfani dasu sai da umurnin likita. Idan kuwa mutum ya dage da amfani dasu toh lallai kuwa akwai matsala.
Mafi akasari, dalilin da ke sa mutane amfani da magungunan steroids ba bisa ka'ida ba shi ne domin karin kiba, musamman mata. Haka kuma ko a cikin maza akwai masu amfani dasu domin karin kiba da kuma karin ƙwanji da girman tsokokin jiki, musamman maza ma'abota daukan karfe (gymnastics) da kuma yan wasanni, musamman 'yan dambe.
Shin Magungunan Sha Ka Fashe Na Steroids Suna Karin Kiba Da Gaske?
Yin kiba, ba dalili ne da zai sa mutum yasha magungunan steroids ba, kuma ba likita mai hankali da zai rubutawa mutum É—aya daga cikin magungunan steroids domin yin kiba.
Amma tabbas magungunan steroids kamar su dexamethasone suna sanya mutum yayi kiba, kuma suna sanyawa maza masu shan su ba bisa ka'ida ba girman tsokoki da kuma girman jiki da murɗewar ƙundodi.
Magungunan steroids suna sanya kiba ta hanya uku kamar haka:
- Stimulation of Appetite: Sanya mutum yawan chin abinci da saurin jin yunwa.
- Water Retention: Riƙe ruwan jiki
- Fat Redistribution: YaÉ—uwar kitse a jikin mutum
Illolin Magungunan Sha Ka Fashe Na Steroids A Jikin Mutane
1. Cushing Syndrome
Wannan wata cuta ce da ke faruwa sakamakon yawan sinadarin hormone na cortisol a cikin jini. Kamar yadda mukayi bayani a baya, magungunan sha ka fashe na steroids suna É—auke ne da sinadarin cortisol.
Wannan shi yasa yawan amfani da magungunan sha ka fashe na steroids kamar irin su dexamethasone yakan sanya wannan hormone yayi yawa a cikin jini har ya haifar wa mutum da cutar Kushin (Cushing Syndrome).
Cutar Cushing ta kan sanya wanda ya kamu da ita ya chanja kamanni, yayi ƙaton ciki da doro, fatar sa ta lalace, wuyansa yayi kamar na shanu kamar yadda kuke gani a wannan hoton da yake ƙasa, wannan she ake kira Cushnoid appearance da turanci.
Bugu da ƙari, wannan cutar Cushing ta kan raunana ƙasusuwa, al'amarin da ake kira osteoporosis, osteoporosis zai iya sanya ciwon ƙasusuwa, gaɓɓai da kuma saurin karaya, faɗuwa kaɗan sai ka ga mutum ya karye.
2. Magungunan steroids suna ƙara hawan jini, saboda suna sanya ƙodar mutum ya riƙe gishiri da ruwa.
3. Yawan shan magungunan steroids yana kawo ciwon sugar, saboda suna ƙara yawan sinadarin sugar na glucose a cikin jini ta hanyar hanawa sinadarin insulin yin aikin sa.
4. Yawan shan magungunan steroids yana karya garkuwar jiki. Wannan yakan sa mutum yayi ta samun infections da cutuka kala-kala, saboda magungunan steroids da yake sha don yayi ƙiba sun raunana garkuwar jikinsa.
5. Magungunan steroids suna kawo wa mata rikicewar al'ada.
6. Magungunan steroids suna sanya cutar ulcer da kumburin tumbi (gastritis).
7. Tsaida shan magungunan steroids kai tsaye na iya haifar da Adrenal Insufficiency
Toh fa duk illolin da muka ambata a baya ba komi ba ne idan anyi la'akari da wannan illah ta adrenal insufficiency da yawan shan magungunan steroids yake kawowa.
Adrenal insufficiency wani al'amari ne da ke faruwa a lokacin da mutum yake yawan shan magungunan steroids sai ya zo ya daina sha kwatsam kai tsaye, watakila rashin halin abin siya, ko kuma yana so ya daina a baki daya. Wannan babban al'amari ne mai iya kisa idan har an dade ana amfani da wadancan magungunan na steroids.
Kamar yadda mukayi bayani a baya, magungunan steroids suna ɗauke da sinadarin hormone na cortisol, a lokacin da mutum ya yawaita shan magungunan steroids ƙwaƙwalwarsa za ta gane cewa yana samun sinadarin na cortisol isasshe daga waje ta hanyar wadannan magungunan, don haka za ta aika sakon cewa a daina samar da wannan sinadarin cortisol a cikin jini, tunda ana samun wadatacce daga wadannan magungunan.
Toh a lokacin da mutum ya daina shan magungunan kwatsam, ga ƙwaƙwalwar ta ce a daina samar da sinadarin cortisol, mutum zai zo da ƙarancin sinadarin cortisol sosai, wannan al'amari ne, mai buƙatar kulawar gaggawa, in ba haka ba yana iya kisa.
Idan mutum yana shan magungunan steroids na wani ɗan lokaci, ba'a dainawa kwatsam, ana dainawa ne sannu - sannu har a daina baki ɗaya. Wannan shi ne zai ba ƙwaƙwalwa damar gane yankewar sinadarin cortisol da take samu daga magungunan sannu-sannu, sannan ta yi umurni da fara samar da shi a cikin jini daga suprarenal glands.
Yadda ake daina shan wadannan magungunan shi ne, kamar yanzu mutum yana shan magani biyu kullum, zai iya ragewa ya fara shan magani É—aya kullum har na sati É—aya, sannan ya kara ragewa ya fara shan rabin magani kullum har na kwana biyar, sannan ya kara ragewa ya fara shan rabin magani duk bayan kwana biyu har na sati daya sannan sai ya daina baki daya.
0 Comments