Kafin mu tsunduma cikin bayanin cutar garkuwar jiki ta Lupus yana da kyau mu É—an yi tsokaci game da menene cututtukan garkuwar jiki a matsayin shimfiÉ—a. Saboda wannan shimfiÉ—ar za ta gina wa mai karatu tubalin fahimtar ita kanta cutar Lupus da sauran cututtuka na garkuwar jiki.
Cututtukan garkuwar jiki ana kiran su da "Autoimmune diseases" a turance. Cututtuka ne masu sanya garkuwar jiki yin faÉ—a da kuma neman hallaka wane sashe ko wasu sassan jikin mutum a bisa kuskure.
Mun san cewa babban aikin garkuwar jiki shi ne sanya sojojin ta domin yaƙi da miyagun ƙwayoyin cututtuka da kuma duk wani baƙon abu da ya shiga a jikin mutum. Lafiyayyar garkuwar jiki ta san dukkan ƙwayoyin halittun mai ita kuma ta kan iya bambanta dukkan ƙwayoyin halittun mai ita daga wasu baƙin ƙwayoyin. Wannnan shi zai ba ta damar bada kariya ga ƙwayoyin halittun jikinta da kuma faɗa da duk wani baƙon abu.
Masu fama da cututtukan garkuwar jiki, garkuwar jikin su ta kan kasa gane wasu ƙwayoyin halittun jikinsu, sai ta ayyana su a matsayin baƙi daga bisani sai ta nemi kai musu hari da hallaka su. A wannan gaɓar zamu iya cewa kenan, masu cututtukan garkuwar jiki, garkuwar jikin su tana cutar da wani ɓangaren jikin su ne da kanta sakamakon rashin iya bambanta ƙwayoyin halittun jikinsu da baƙin ƙwayoyin halittu.
Cutar Garkuwar Jiki Ta Lupus
Faɗa tsakanin sojojin garkuwar jiki da kuma ƙwayoyin halittun ɓangaren da take ƙoƙarin hallaka wa, shi yake haifar da kumburin ɓangaren da kuma sauran alamomin cutar Lupus.
Garkuwar jikin masu cutar Lupus ta kan iya tura sojojin ta domin kai hari ga;
- Zuciya
- Fata
- Ƙwaƙwalwa
- Huhu
- Ƙoda da kuma
- Gaɓɓai
WaÉ—annan bangarorin jiki su ne cutar Lupus tafi kai hari a jikin dan Adam, amma cutar Lupus tana iya shafuwar ko'ina a sassan jiki.
Alamomin Cutar Lupus
1. A lokacin da sojojin garkuwar jiki suke kai har ga fata, zaku iya ganin mai fama da cutar Lupus ya fara fitar da wasu ƙuraje, ko kuma fatar sa ta yi kamar an ƙona, ko wasu tambura sun fito a jikin fatar. Haka kuma mutum zai iya samun yawan zubar gashin jiki ko gashin kai.
Haka kuma akwai wani tambarin ƙuraje da ke fitowa masu cutar Lupus a fuska, wanda zaku ga ƙuraje sunyi kalan ja ko baƙi a hanci da kuma kumatun mai ɗauke da wannan cutar. Ana kiran wannan tambari da Malar rashes a turance, kuma tambarin wani babban jigo ne wajen gane masu ɗauke da cutar Lupus.
2. Idan cutar Lupus take kai hari a ƙwaƙwalwa zaku iya ganin mutum na yawan ciwon kai, yawan sambatu, yawan mantuwa, mutuwar rabin jiki, watarana ma har da fisge-fisge ko kuma farfadiya.
3. A lokacin da cutar Lupus take kai hari a gaɓɓai, zaku ga mutum na yawan samun ciwo da kumburin wasu gaɓoɓi ko ma dukkan gaɓoɓi wanda ya ƙi ci yaƙi cinyewa.
4. A lokacin da cutar take kai hari a zuciya takan iya sa mutum ya kamu da ciwon zuciya ko kuma ruwa ya taru a zuciya kafin daga baya zuciyar ta gaza ta fara nuna alamomin gazawar zuciya kamar kumburin ƙafa, tari da wahalar nunfashi.
5. Haka huhu, ruwa sukan iya taruwa a huhu su hana mutum numfashi. Haka kuma mutum zai iya samun ciwon kirji, tari da kuma yawan yin cutar Pneumonia.
6. Idan sojojin garkuwar jiki suna kai hari a ƙoda mutum zai fara bayyanar da wasu alamomi na gazawar koda.
A lura cewa masu cutar garkuwar jiki ta Lupus suna samun wadannan alamomi ne lokaci bayan lokaci. Haka kuma a kowane lokaci cutar tana iya kai hari a ɓangare na daban a jikin mutum. Misali idan mutum ya samu alamomin ƙwaƙwalwa yanzu toh wani lokaci yana iya samun alamomin zuciya ko na ƙoda ko ma ya same su duka a tare.
Yadda Ake Kamuwa Da Cutar Garkuwar Jiki Ta Lupus
Duk da cewa cutar ba ta yaɗuwa a tsakanin jama'a, amma cutar za'a iya gadon ta. Dalili kuwa shi ne, idan mutum iyayensa na dauke da wadannan matsaloli na ƙwayoyin halitta masu kawo cutar Lupus, toh akwai yiwuwar ya gado wadannan ƙwayoyin halittun daga iyayensa.
Bugu da kari, bincike ya nuna cewa mata sun fi maza zama kan haÉ—arin kamuwa da cutar Lupus. Haka kuma cutar tafi bayyana ne a lokacin da mace ta fara kai mizanin balaga har zuwa shekaru 45.
Yadda Ake Maganin Cutar Garkuwar Jiki Ta Lupus
Cutar garkuwar jiki ta Lupus cuta ce wadda ba ta warkewa ga baki daya. Sai dai cutar ta kwanta daga baya kuma ta sake tashi. Magungunan da za'a yi amfani da su a wajen magance cutar Lupus sun ƙunshi, magunguna masu ragewa garkuwar jiki ƙarfi a lokacin da cutar ta motsa, sannan sauran magungunan sun danganta ne daga ɓangaren jikin da cutar ta kai hari.
Kammalawa
Idan akwai mai tambaya ya ajiye mana ita a cikin akwatin sharhi da ke kasa, ko kuma ya danna alamar WhatsApp da ke ƙasa a hannun hagu domin samun mu a WhatsApp.
0 Comments