Yadda ake maganin yawun bacci da kuma abubuwan da ke kawo zubar yawu (Drooling in sleep)

Gabatarwa:

Maganin yawun bacci

Watakila, kun taÉ“a tashi  daga bacci mai zurfi kuka ga matashin kan ku (pillow) ya jiÆ™e da yawu ko makwancin ku, ko zanen da kuke rufa da shi ku kuma ku ga kwancin yawu a kumatun ku. 

Zubar da yawu a cikin bacci na iya zama da wahala da abin kunya, musamman ma idan kuna kwana kusa da wani da kuke ƙoƙarin birgewa ko kuma a lokacin da kuke yin gyangyaɗi a cikin jama'a kamar cikin motar kasuwa ko jirgin sama.

Zubar da yawu yayin bacci ba wani abin damuwa ba ne musamman idan jariri ne ya yi, amma idan babba ne, farkawa cikin ƙoramar yawu na iya zama abin ban takaici da kunya, musamman idan ba kai kaɗai kake yin bacci ba.

Dukkan mu mun taɓa zubar da yawu a kan makwancin mu a wani lokaci. Amma idan ka lura cewa zubar da yawun da kake yi ya zama mai yawa, cigaba da karanta wannan rubutu domin ka koyi yadda zaka daina kwararar yawu na dindindin.

Me yasa mutane ke zubar da yawu yayin barci?

Kafin ka koyi yadda zaka daina, bari mu fara fahimtar dalilin da yasa mutane ke zubar da yawu tun farko. Yayin barci, tsokokin fuska da tsarin haɗiye yawu suna shiga yanayin natsuwa gaba ɗaya. Wannan shi ne dalilin da yasa mutum ke ƙara samun kwanciyar hankali lokacin barci, saboda duka tsokokin sa suna samun natsuwa da hutawa.

Bugu da Æ™ari, wannan natsuwar tsokokin da ke faruwa yana hana haÉ—iye yawu a lokacin da mutum yake bacci, wanda zai sanya yawu taruwa a baki. Saboda haka, idan tsokokin fuska sun natsu, bakin ka yana iya buÉ—ewa kaÉ—an, kuma yawun da ya taru yana iya fara kwarara kan matashin kan da kake kwance a sama. 

Wannan shi ne dalilin da yasa jarirai da ƙananan yara ke zubar da yawu sau da yawa, saboda ba su iya sarrafa tsokokin fuskar su, ko suna farke ko sun yi barci.

Toh, idan babu wata illah ga jarirai, to ba matsala ga manya, ko? To, ba haka bane. Akwai lokacin da kwararar yawu idan tayi yawa, a jarirai da manya ta kan iya zama sakamakon wata matsala. Idan ta faru akai-akai kuma fiye da ƙima, yana iya zama alamar ciwon da ke tasowa ko wata matsala a jikin mutum.

Abubuwan da ke haifar da yawan zubar yawu yayin barci

Zubar da yawu yana faruwa ne idan jikin ka yana samar da yawun da ya fi Æ™ima ko baka iya rike yawun a bakinka, ko kuma idan kana fama da matsalar haÉ—iye yawu. Samar da yawun da ya fi Æ™ima ana kiransa da sialorrhea ko hypersalivation. 

Duk da yake zubar da yawu yayin barci abu ne na al'ada, wasu abubuwa na iya sanya ka zubar da yawu fiye da yadda aka saba.

1. Yadda kake kwanciyar ka yayin barci

Maganin yawun bacci

Matsayin da kake kwanciya yayin barci na iya tasiri kan yawan yawun da kake samu a kan matashin kai da safe. Idan ka kwanta rairam da gadon bayan ka, nauyin ƙasa yana sa yawun da ka samar ya tsaya a bakin ka ko ya gangaro zuwa makogwaro. Amma idan kana kwanciya da gefe ko a rub da ciki, nauyin kasa na iya jan yawun ya kwarara zuwa matashin kai, wanda hakan zai haifar da kaji kanka a cikin ƙoramar yawu.

Idan kai mai kwanciya ne da gefe ko a rub da ciki kuma kana barci da bakinka a bude, toh zaka fi kowa iya zubar da yawu a yayin barci. Kwanciya a gadon baya na iya taimakawa wajen rage zubar da yawu. Hakanan, zaka iya É—aukar matakai don yin numfashi ta hanci da rufe bakinka yayin barci, kamar amfani da tef don rufe baki.

2. Cutar mura da kuma saura allergy 

Idan kana fama da mura, ciwon makogwaro, ko kuma alamomin kamuwa da allergy na yanayi, waÉ—annan yanayi na iya kumbura jijiyoyin hancinka su kuma toshe hanyoyin iska na hanci, hakan yana tilasta maka yin numfashi ta baki wanda zai sa ka zubar da yawu fiye da yadda aka saba. Sauran cututtuka, kamar su mononucleosis, tonsillitis, da kuma cutar sinuses, suma suna iya haifar da yawan zubar da yawu yayin bacci.

3. Taunar haƙora yayin bacci (Bruxism)

Zubar da yawu yana yawan faruwa tare da taunar haƙora yayin barci, wato, cizawar haƙora bai gaira ba dalili yayin barci. Wannan na iya kasancewa sakamakon alaƙar taunar haƙora da yin numfashi ta baki, domin yawun na iya fita daga baki idan mutum yana barci da bakinsa a buɗe. Saboda haka a lokacin da mutum ya buɗe bakin sa domin tauna haƙora ko yin numfashi sai yawun ya fara kwarara.

4. Illolin Wasu Magunguna

Idan kana shan magunguna da aka rubuta maka kuma kana zubar da yawu da daddare, magungunan ka na iya zama dalilin wannan kwararar yawun. Yawan samar da yawu da zubar da yawu na daga cikin illolin wasu magunguna, ciki har da wasu magungunan kashe Æ™wayoyin cutar bakteriya (antibiotics), magungunan antipsychotic, da magungunan da ake amfani da su wajen magance cutar Alzheimer. 

Idan an lissafa zubar da yawu a matsayin É—aya daga cikin illolin magungunan ka, kar ka daina shan maganin. Maimakon haka, ka fara tuntubar likitanka game da damuwarka, sannan ka tambaye shi ko zai iya canja maka wani maganin da ba zai haifar da yawan zubar da yawu ba

5. Wasu Cututtuka

Masu fama da matsalolin lafiya, kamar waɗanda suka taba kamuwa da cutar shanyewar ɓangare ko waɗanda ke fama da multiple sclerosis, ko masu fama da cutar obstrucive sleep apnea, ko yara masu fama da cutar epiglottitis ko pharyngotonsillitis duk su na zubar da yawu fiye da ƙima. Amma idan kwararar yawunka ba ta da nasaba da rashin lafiya, ga wasu hanyoyi da zaka rage zubar da yawu a lokacin bacci

Yadda zaka daina zubar da yawu yayin barci

1. Canza yadda kake kwanciya 

Wannan na iya zama mafi saukin dabara idan ka saba kwanciya a rub da ciki ko a gefe, watau a yanayin da nauyin ƙasa yake iya jan yawun bakin ka zuwa makwancin ka. Idan kana kwanciya kan gefe ko a rub da ciki, kana da damar zubar da yawu yayin bacci. Saboda haka, canja kwanciya zuwa kwanciya rairam a gadon baya zai hana yawun fita daga bakinka.

Maganin yawun bacci

2. Yin amfani da na'urar hana kwararar yawu 

Akwai na'urori na musamman da ke hana zubar da yawu, kuma suna da matukar tasiri. TuntuÉ“i likitan hakori domin samun madaidaicin na’ura da za ta taimaka maka.

3. Magance alamomin mura da allergy 

Idan kana zubar da yawu da daddare kuma kana da alamomin mura ko allergy (yawan atishawa, yoyon hanci da tari), to hakan na iya zama dalilin zubar yawun. Magance mura da allergies zai iya buɗe hanyoyin hancin ka kuma ya ba ka damar yin numfashi ta hanci maimakon baki. Idan kana iya yin numfashi ta hanci yayin barci maimakon baki, zaka iya fuskantar ƙarancin zubar da yawu.

4. Duba ko kana da cutar hucin barci (Sleep Apnea) 

Cutar hucin barci tana shafar numfashi yayin barci. Idan kana zubar da yawu kuma kana tashi da bakinka bushe, ka tuntuɓi likita don ganowa.

5. Duba magungunan da kake sha

Wasu magunguna, kamar na maganin hawan jini ko damuwa, suna iya haifar da yawan yawun baki. Ka tambayi likitanka idan hakan na daga cikin illolin magungunan ka.

6. Ka É—aga kan ka a wajen kwanciya 

Maganin yawun bacci

Kwanciya da kai a sama zai taimaka wajen rage kwararar yawu. Amfani da matashin kai (pillow ) mai tsawo zai iya taimaka maka.

7. Tsaftace hancin ka 

Idan hancin ka ya toshe, hakan na iya tilasta maka yin numfashi ta baki, wanda ke haifar da kwararar yawu a makwancin ka. Tsaftace hancin ka kafin kwanciya da kuma amfani da magungunan wanke hanci na taimakawa.

Post a Comment

0 Comments