Gabatarwa:
Maza da yawa sukan ga azzakarin su yana karkacewa a wani gefe, watau yana lankwashewa, idan azzakarin ya mike a lokacin da sha'awar su ta yin jima'i ta motsa, ko a lokacin yin fitsari. Wannan karkacewar ko lankwashewar azzakari ita ce ake kira "penile curvature" a turance. A likitance kuwa ana kiranta "penile angulation".
Shin Za'a Iya Gane Azzakarin Da Ya Karkace A Lokacin Da Bai Miƙe Ba
Amsar wannan tambayar ita ce, eh za'a iya, kuma a'a ba za'a iya ba. Eh, mai yiwuwa ne mutum ya iya gane cewa yana da karkataccen azzakari ko da kuwa azzakarin sa bai miƙe ba. Ma'ana, zai iya ganin azzakarin sa a karkarce a lokacin da ake zaune lafiya.
Abubuwan da suke haddasa hakan su ne banbance-banbance wajen halittar azzakari a tsakanin maza (variations in penile anatomy among men). Wannan yana nufin anfi ganin karkacewar azzakari ne idan ya zamo azzakarin yana da tsawo (lengthy penis), ko tsokokinsa su na da laushi sosai (highly elastic penile tissues), ko jijiyoyin sa wasu su na da tsawo, wasu basu da tsawon (suspensory ligaments variation), ko tsokokin sa wasu su na da girma wasu basu da girma, sa'annan rabuwarsu ta banbanta (size and distribution of erectile tissues).
Idan ance a'a kuwa yana nufin ana iya kasa ganin karkacewar saboda ba mai yawa bace (minimal degree of curvature), ko tsarin tsokoki da jijiyoyin azzakari (tissues and ligaments properties) baya nuna karkacewar sai idan azzakarin ya miƙe, ko rashin tsauri (penile flaccidity) a lokacin da azzakari bai mike ba wanda hakan yana sanya a kasa gane karkacewar sa.
Ire-iren Karkacewar Azzakari
Karkacewar azzakari ta rabu zuwa manyan rukunnai guda biyu:
1. Karkacewar azzakari wanda ba matsalar rashin lafiya ta haddasa shi ba (physiological penile curvature), kuma shine ake kira karkacewar azzakari na al'ada (normal penile curvature).
2. Karkacewar azzakari wanda matsalar rashin lafiya ta haddasa shi (pathological penile curvature), kuma shine ake kira karkacewar azzakari wanda ba na al'ada ba (abnormal penile curvature).
Karkacewar Azzakari Na Al'ada (Physiological Penile Curvature)
Wannan nau’in karkacewar yana zuwa ne a matsayin al'ada (normal) ga maza da yawa. A wannan yanayin, karkacewar tana da sauÆ™i, ma'ana ba ta da yawa, kuma bata kawo ciwo ko wata matsala yayin jima’i ko fitsari. Muhimman siffofin karkacewar sune:
- a. Lanƙwasar ko karkacewar tana da sauƙi (mild curvature).
- b. Ana haihuwar mutum da ita ne (it is present at birth), kuma tana bayyana lokacin balaga (it develops at puberty).
- c. Ba ta kara yin tsanani a lokacin da mutum ya kara nisan shekaru (it does not worsen with increasing age).
- d. Ba ta haifar da jin ciwo ko wata matsala a lokacin miƙewar azzakari (it does not cause pain or erectile dysfunction).
- e. Bata buƙatar yin amfani da magani domin daidaita ta (it does not require medical treatment). Amma idan mutum baya buƙatar ganin karkacewar, toh, zai iya zuwa asibiti domin ayi masa aikin tiyatar daidaita azzakarin. Tabb, me ya kaika!
Karkacewar Azzakari Na Rashin Lafiya (Pathological Penile Curvature)
Wannan nau’in karkacewar azzakarin yana faruwa ne idan lanÆ™wasar ko karkacewar tana da tsanani ko ta faru sakamakon wasu matsalolin rashin lafiya, yawanci cutar Peyronie ce take haifar dashi. Yana iya bayyana da sauri (suddenly) ko a hankali (gradually), sannan yana haifar da jin ciwo, ko matsalar rashin mikewar azzakari yadda ya kamata, ko kuma wahalar yin jima'i.
Rashin Lafiyar Da Ke Haifar Da Karkacewar Azzakari
1. Cutar Peyronie
Wannan cuta na faruwa ne sakamakon samuwar wani nau’in tabo (fibrous scar tissue) a cikin fata mai kauri wadda take rufe da gabobin jini na azzakari (tunica albuginea).
Tabon yana iya haifar da lanƙwasa mai tsanani yayin miƙewar azzakarin, wanda hakan zai iya jawo jin ciwo ko kuma siffar azzakarin ya zamo ba kyawun gani (deformed looking). Idan hakan ya faru, toh, yana iya tsananta idan aka daɗe, ko kuma lanƙwasar ta ƙara tsanani. A wasu lokuta kuwa, tabon yana iya warkewa da kansa. Amma a wasu lokuta sai anyi amfani da magunguna ko ayi tiyata domin warkar da shi.
2. Karkacewar azzakari saboda rauni (traumatic penile curvature)
Wannan yana faruwa ne sakamakon samun rauni ko jin ciwo a azzakari, galibi a lokacin jima’i. Raunin yana iya haifar da lahani a fata ko tsokar azzakari, wanda zai iya kawo samuwar tabo da lankwashewar azzakari da ba ta al'ada ba.
3. Karkataccen azzakari na haihuwa (congenital penile curvature)
Wannan yanayi ne wanda ake haihuwar mutum da shi, galibi saboda rashin daidaito a haÉ“akar halittun tsokokin azzakarin (corpora cavernosa). Ba kamar cutar Peyronie ba, wannan ba ta da alaÆ™a da samuwar tabo. wasu lokutan, idan lankwashewar tayi tsanani sosai, to, akwai buÆ™atar ayi tiyata domin gyarawa idan tana jawo matsalar yin jima’i.
Tasirin Karkataccen Ga Jin DaÉ—in Jima'i Da Kuma Samun Ciki
Karkataccen azzakari, mai sauƙi ko tsanani, yana da tasiri daban-daban a kan gamsuwar mace yayin jima'i da kuma iya samun juna biyu, gwargwadon yadda karkacewar take da tsanani ko alamun dake tattare da ita, kamar haka:
1. Tasiri kan Gamsuwar Jima'i ga Mace
Idan karkatar ta na da sauƙi ko kuma ta al'ada ce, to, ba za ta hana mace samun gamsuwar jima'i ba. Hasalima, wasu matan su na iya samun ƙarin gamsuwar, domin lanƙwasar tana iya taɓa wasu wurare a cikin farji, musamman wurin G-spot.
Ita kuwa karkacewa mai tsanani wacce take da alaka da rashin lafiyar azzakari ta cutar Peyronie, tana iya kawo wahala yayin jima'i, wanda zai iya jawo rashin jin daÉ—i ko ciwo ga ma'auratan su dukkansu.
2. Tasiri Wajen Samun Juna Biyu
Karkacewa mai sauƙi ko ta al'ada ba ta da tasirin hana mace samun juna biyu. Muddin yin inzali da samar da ruwan maniyyi ba su sami matsala ba, toh, samun juna biyu shi ma ba zai sami matsala ba Insha Allah. Wannan yana nufin siffa ko karkatar azzakari ba ta hana samun juna biyu, matuƙar za'a iya yin jima'i yadda ya kamata ba tare da wata matsala ba.
Kenan karkata mai tsanani, musamman idan ta hana samun yin jima'i yadda ya kamata, tana iya tasiri kai tsaye ga haihuwa. Idan ba'a iya samun shigar maniyyi cikin farji ba saboda matsalar karkatar, toh, hakan zai iya rage damar samun ciki. A irin wannan yanayin, dole ne a nemi maganin rage ko kuma daidaita karkacewar azzakarin.
A takaice, yayin da karkata mai sauƙi ba ta haifar da matsala ga jin daɗin mace ko haihuwa, karkata mai tsanani tana iya kawo rashin jin daɗi yayin jima'i da kuma rage damar samun ciki idan ta hana jima'i yadda ya kamata.
Usman Shehu Hassan
0 Comments