Amfanin Namijin Goro Ga Lafiyar Mace Da Namiji

Amfanin namijin goro ga lafiyar maza


Don Allah Dr menene amfanin namijin goro a cikin jikin mace, kuma mene ne illarsa?

Amsa 

Namijin goro shi ne “bitter kola” da harshen turanci ko kuma “garcinia kola” a harshen kimiyya da fasaha. Yana ƙunshe da sinadaran caffeine, vitamin C, iron, potassium, calcium, protein, carbohydrate, da fats. 

A kan wannan dalilin ne masu maganin gargajiya su ke yin amfani da tsiron sa domin warkar da matsalolin gudawa (diarrhea), cutar huhu (bronchitis), cututtukan hanta (liver diseases), ciwon sanyi (gonorrhea), cututtukan kumburi (inflammatory diseases) da sauransu.

Amma duk da wannan amfanin namijin goro, jikin wasu mutane yana bijire masa (allergy) don haka yana iya haifar mu su da illah, kamar ɗaukewar barci (insomnia), hawan jini (hypertension), tashin zuciya (nausea), rawar jiki (tremors), da dai sauran su.

Bai kamata mace ta ci namijin goro ba a lokacin da take yin jinin haila saboda caffeine ɗin da yake cikin sa zai iya tsananta mata laulayin al’adar. Wani bincike kuma ya nuna cewa idan mace taci namijin goro a lokacin da ta kusa saka ƙwai na haihuwa (ovulation), toh, maiko da kuma dacin da yake cikin namijin goron zai iya hanata saka kwai.

Amma ga mace mai ciki wanda ya fara ƙwari, cin namijin goro kaɗan yana taimakawa wajen rage yawan tashin zuciya da ƙwarnafi, sa’annan yana gyara mahaifa. Ita kuma mace mai shayarwa, sinadarin ɗaci da yake cikin namijin goro zai iya ƙara mata ruwan nono. Amma a rika ci kadan ba da yawa ba. 

Amfanin namijin goro ga maza shi ne yana haɓaka yawan sinadarin testosterone a jiki, kaɗan daga cikin ayyukan testosterone su ne ƙara ƙarfin sha’awar saduwar aure, ƙara yawan ƙwayoyin maniyyi, ƙarfin mazakuta, da karfin ƙasusuwa. 

Sai dai cin namijin goro fiye da ƙima zai iya sanya caffeine ɗin da yake cikin sa ya ta’azzara ciwon hawan jini da kuma ciwon ido na glaucoma. Wasu mutane sukan haɗa namijin goro da mintin Tom Tom a matsayin maganin gargajiya na tari. Wasu kuma suna haɗa namijin goro da zuma domin irin wannan dalilin.

A lura cewa, amfanin da muka lissafa a sama ana samun su idan ana chin namijin goro akan ƙima, masana sun ba da shawarar kar a wuce ƙwara biyu a yini. Amma idan ana chin namijin goro fiye da ƙima, akwai hatsarin lafiya dayawa da yakan iya ɗora mutum akai. Munyi bayanin wasu a cikin wannan rubutun Harmful Effects of Bitter Kola To Health.

WalLahu A’lam.

No comments: