Bayani Game Da Cutar Maƙoƙon Wuya Na Thyroid

Cutar Maƙoƙon na thyroid
Assalamu alaikum warahmatullah Dr. Dan Allah ina son kayimin ƙarin bayani a kan goiter (Maƙoƙo) ya fito min kuma yana yimin ciwo. Nayi tambaya a group ba a bani amsa ba. Muna godiya d irin abubuwan da ake mana Allah ya saka da alkhairi.

Amsa

MaÆ™oÆ™on wuya shi ne ake kira da "goiter" ko kuma "thyromegaly" a likitanci. MaÆ™oÆ™o wani kumburi ne da ke fitowa a cikin jakar sinadarin thyroid (thyroid gland) wanda yake kasancewa a Æ™asan wuya. Ba lallai bane maÆ™oÆ™o ya zamo ciwon daji (cancer), amma  har ko yaushe, fitowar maÆ™oÆ™o alamar matsalar jakar sinadarin thyroid ne.

Abubuwan Da Ke Kawo MaÆ™oÆ™on Wuya 

Abubuwan da suke iya haifar da makoko sune: 

1. Ƙarancin sinadarin iodin a cikin jini (iodine deficiency)

Wannan shi ne mafi yawa cikin dalilan samuwar makoko a duk faɗin duniya. Iodin yana da matuƙar muhimmanci wajen samar da sinadarin hormone na thyroid, kuma rashin iodine zai iya sanya jakar thyroid ta kumbura don ƙoƙarin cike wannan giɓin, wannan kumburin shi zai haifar da maƙoƙon wuya.

2. Graves’ Disease

Wannan cuta ce ta garkuwar jiki (autoimmune disorders) wacce take sanya jakar thyroid ta samar da sinadarin iodine fiye da ƙima (hyperthyroidism), kuma hakan yana haifar da kumburewar jakar thyroid da kuma samun maƙoƙo.

3. Hashimoto's Thyroiditis

Wannan itama wata cuta ce ta garkuwar jiki (autoimmune disorder) inda garkuwar jiki take kai hari ga jakar sinadarin thyroid, kuma hakan yana sanya jakar ta kasa samar da sinadaran hormone na thyroid yadda ake buÆ™ata (hypothyroidism).  Wannan yana iya haifar da kumburin maÆ™oÆ™o.

4. Tsirowar Ƙari a Cikin Jakar Thyroid (Thyroid Nodules)

Wannan ƙari, wani kumburi ko kurji ne da yake fitowa a cikin jakar sinadarin thyroid, wanda yake haifar da kumburin maƙoƙo.

5. Ciwon Daji na Thyroid (Thyroid Cancer)

Ko da yake baya faruwa sosai, amma ciwon cancer yana iya haifar da kumburin jakar thyroid idan ya shafi tsarin halittar jakar. Haka kuma, sauran cututtukan da muka ambata a sama idan suka haifar da maƙoƙo, toh yakan iya rikiɗewa ya zama maƙoƙon cancer thyroid.

6. Juna Biyu (Pregnancy)

Canje-canjen zubar ruwan sinadaran estrogen da progesterone da sauran su, yayin da mace ta ɗauki ciki, yana iya haifar mata da kumburin maƙoƙo na wucin gadi (temporary goiter) saboda jikinta yana buƙatar karuwar sinadarin thyroid.

7. Kumburi (Inflammation)

Kumburin jakar sinadarin thyroid (thyroiditis) yana iya haifar da kumburin makoko.

Yadda ake maganin cutar maÆ™oÆ™on wuya na thyroid 

1. Karin Iodin a Cikin Abinci (Iodine Supplementation)

Idan maƙoƙo ya samo asali ne daga rashin isasshen iodin a cikin jini, toh, kara yawan cin abincin da yake ɗauke da sinadarin iodin ko shan magungunan ƙarin iodin yana iya rage kumburin maƙoƙon.

2. Yin Amfani Da Magunguna (Medications)

Idan maÆ™oÆ™o ya samo asali ne daga Æ™arancin sinadarin thyroid (hypothyroidism), toh, shan maganin Æ™arin sinadaran thyroid hormones, kamar  levothyroxine zai iya rage kumburin.

Idan kuwa maƙoƙon ya samo asali ne daga yawan sinadarin thyroid fiye da ƙima a cikin jini (hyperthyroidism), toh, shan magungunan da ke rage yawan sinadaran thyroid ɗin (antithyroid medications) zai iya rage kumburin maƙoƙon.

3. Maganin Maƙoƙo ta Hanyar Hasken Radiation (Iodine Radioactive Therapy)

Ana amfani da wannan dabarar ta hasken radiation na musamman don rage girman jakar thyroid ɗin da ta zama maƙoƙo a lokutan hyperthyroidism.

4. Aikin Tiyata (Surgery)

A wasu lokutan, idan maƙoƙo yayi girma sosai har yakai yana kawo matsala wajen numfashi ko haɗiye abinci, ko wajen fitar da furuci ko kuma idan ana zargin maƙoƙon ya rikiɗe ya zama ciwon daji, toh, ana iya cire wani bangare ko dukkan jakar sinadarin thyroid din (thyroidectomy).

5. Kulawa Ta Akai-Akai (Regular Observation) 

Idan maÆ™oÆ™on ba ya haifar da wata matsala, toh,  likita yana iya bayar da shawarar a cigaba da lura da yanayin sa ba tare da yin magani nan-take ba.

Kammalawa

A takaice, ya kamata kije asibiti domin ayi bincike a tabbatar da abin da ya haddasa miki wannan maƙoƙon, da kuma matakin da yake ciki a jikinki a halin yanzu, domin a san irin maganin da za'a yi miki.

WalLahu A'lam

No comments: