Meke Kawo Jinkirin Jinin Haila Ko Rashin Ganin Jinin Al'ada


Rashin ganin jinin haila, ko kuma jinkirin jinin haila shi ake kira da "Amenorrhea" da harshen likitanci. A harshen masana kuwa, wannan kalmar tana nufin samun tsaiko, jinkiri ko daukewar jinin haila tsawon wata biyu ko fiye da haka. Masana sun raba jinkirin jinin haila zuwa kashi biyu kamar haka :

1. Primary Amenorrhea - Jinkirin haila kashi na farko 
2. Secondary Amenorrhea - Jinkirin haila kashi na biyu 

1. Primary Amenorrhea

Wannan shi ne jinkirin fara hailar mace ko rashin yin hailar mace har takai shekaru goma sha shidda zuwa sama ba ta fara ganin jinin haila ba.

2. Secondary Amenorrhea

Wannan shi ne É—aukewar jinin haila har na tsawon wata biyu ga macen da take yin hailarta normal a chan baya .

Abubuwan Dake Kawo Jinkirin Jinin Haila


Jinkirin jinin haila


Abubuwa da dama suna kawo jinkirin Haila, ga kadan daga ciki :

1. Pregnancy

Mafi yawan mata idan sun dauki ciki sun daina ganin hailarsu har sai wasu watanni bayan haihuwa, ko kuma idan cikin ya samu matsala. Samun ciki shi ne abu na farko da yafi kawo jinkirin jinin haila.

2. Lactation/Breastfeeding 

Idan mace ta haihu kuma tana shayar da jariri, to wannan yakan sa daukewar jinin haila. Bayan É—aukewar jinin biki, mata da yawa sukan shafe watanni basa yin haila idan su ke shayar da jariri, wannan ba matsala bane.

3. Infection 

Kamuwa da kwayoyin cuta, kamar cutar sanyin mata, cututtukan da ke yaÉ—uwa ta hanyar saduwa na kan gaba wajen kawo wa mata jinkirin jinin haila.

4. Family Planning Pills 

Shan wasu daga cikin ƙwayoyin tazarar haihuwa (a cikinsu akwai masu rikita jinin haila, akwai kuma waɗanda suke saita jinin aila)

5. Family planning injection 

Amfani da alluran bada tazarar haihuwa kamar irin su e.g Depo-provera, shi ma yana kawo rashin ganin jinin al'ada. Wata mace da tayi alluran ma ba zata ƙara ganin jinin al'ada ba har sai alluran ya ƙare aiki.

6. Ovarian cyst 

Samun kumburin a cikin kwan haihuwa na mace da ake cewa ovarian cyst shima yana iya rikicin jinin haila.

7. Stress 

Yawan yin aiki mai gajiyar wa ko kuma rashin kwanciyar hankali suna kawo jinkirin jinin haila. 

8. Regular Strenuous Exercise

Motsa jiki mai tada hankali kamar gudu zuwa waje mai nisa, ko kuma mata masu jimmin (gymnastics) suna samun rikicin jinin haila.

9. Extremely Low Body Weight. 

Rashin nauyin jiki wanda ya samu asali daga rashin isheshahen abinci mai lafiya na kawo canjin nau'in yin jinin haila.

10. Diseases.

Wasu cututtuka kamar su irin su cutar PCOS, cutar Asherman Syndrome na kawo É—aukewar jinin haila.

11. Problem with thyroid 

Matsalar gland din thyroid wanda yake samar da sinadaran hormones na thyroid shi ma yana kawo barkacewar jinin haila.

12. Medications

Wasu magunguna kamar irin su, magungunan ciwon damuwa, suna kawo jinkirin jinin haila.

Shin Jinkirin Jinin Haila Na Da Alaƙa Da Rashin Haihuwa?

Eh, lallai tabbas hakane yawan samun jinkiri da kuma rikicin jinin haila kan iya kawo rashin haihuwa ko jinkirin samun ciki, domin shi samun ciki yana buĆ™atar yanayin al’ada daidaitacce ba rikitacce ba.