Gabatarwa:
Amblyopia - ciwo ne wanda aka fi sani da raggon ido a hausa - wata cuta ce da ke kawo asara ko rashin hangen nesa dakyau ko kuma rashin gani da kyau wanda ke shafar ido ɗaya ko duka biyu, wannan cutar an fi samun ta ga yara ƙanana ko matasa.
Cutar amblyopia ko kuma cutar kasalar idanu ana danganta ta ne da rashin gani da kyau ko kuma samun babban bambanci a matakin hangen nesa ko hangen kusa tsakanin idanu biyu.
Yawanci cutar tana somawa ne kafin shekaru shida (6) kuma bai cika shafar hangen gefe ba. Gilashin ido ko amfani da tabarau da ake yi a asibiti ba zai iya gyara ƙarancin hangen nesa da amblyopia ke haifar wa ba idan ba a yi saurin gane wannan cuta a cikin muhimmin lokaci ba.
Abubuwan da ke kawo cutar raggon ido
1. Rashin samun cikakkiyar jarrabawar ido don gano yanayin ganin yaron da ya kai watanni shida (6) zuwa shekaru uku (3) da haihuwa.
2. Amfani da tabarau na asibiti wanda ba chanchanta da idanun mutum ba.
3. Tarihin wannan cutar a cikin zuriya ko iyali.
4. Haihuwar jarirai kamin su cika mizanin watanni tara (9).
5. Jarirai da aka haifa da wata naƙasa
6. Rawar idanu wanda ake kira strabismus (ido É—aya ko duka biyu su kama juyawa a ciki ko a waje).
6. Rashin gani na ido É—aya.
7. Haihuwar jarirai da cutar cataract.
8. Kurakuran gani masu shafar retina (refractive errors).
Alamomin raggon ido
Alamun raggon ido sun haÉ—a da fifita amfani da ido É—aya (ido mai lafiya) ko kuma fifita ganin abinda ke sashe É—aya (sashen ido mai lafiya). Idan kuma ya shafi dukkan idanu toh marar lafiya zai dinga gani bishi-bishi a dukkan idanu. Alamun ba koyaushe suke bayyana ba kai tsaye ba.
Yadda ake gane cutar raggon ido a asibiti.
Saurin gane cutar tun da wuri yana ƙara bada damar samun cikakkiyar farfaɗo wa ko kuma warkewa daga cutar.
Ƙungiyar likitocin optometric ta Amurka ta ba da shawarar cewa yara su yi cikakken jarrabawar gani tun suna yan wata shida (6) da kuma sake yi a lokacin da suka kai shekaru uku (3).
Wannan cutar ta kasalar idanu bata warkewa da wuri idan ba a gano cutar ba har zuwa lokacin da jariri ya kai matashi ko balagagge. Magani a wannan lokaci yana É—aukar tsawon lokaci kuma sau da yawa ba shi da tasiri.
Yadda ake maganin cutar raggon ido
Magani ga malalacin ido ya haÉ—a da amfani da gilashin tabarau na asibiti da kuma koyar da yaro yadda zai yi amfani da raggon idon. Haka kuma, yaron da ya karkata zuwa amfani da ido É—aya (ido mai lafiya) ana koyar da shi yadda zai iya amfani da idanun duka biyu. Har takan iya sa a rufe ido mai lafiya da wata yar leda domin yaron ya fara amfani da ido marar lafiya, wanda yawan amfani zai sa malalacin idon ya farfaÉ—o daga cutar.
Riga-kafi
Kamar yadda mukayi bayani a baya, gano wannan cutar da wuri shi ne abu mai matuƙar amfani a wajen kare ta. Ana gano wannan cutar da wuri ta hanyar yiwa ƙananan yara cikakken jarrabawar ido ta watanni shida (6) da kuma ta shekara uku (3).
0 Comments