Bayani game da ciwon ido na Apollo da yadda ake maganin sa (Pink eye - Conjunctivitis)

Gabatarwa:

Ciwon ido na Apollo wata cuta ce da ke addabar idanu a lokacin da wata Æ™wayar cuta ta shafi fatar conjunctiva. Wannan cutar ta Apollo tana da matuÆ™ar saurin yaÉ—uwa a al'umma saÉ“anin cututtukan fatar idanu da muka yi bayani a rubutun baya. Kamin mu fara bayanin ciwon  ido na Apollo wanda ake kira conjunctivitis da turanci, yana da kyau muyi fashin baÆ™i game da mene ne fatar conjunctiva.



Mene ne conjunctiva?

Conjunctiva wata fata ce siririya sosai tamkar leda transparent (watau za'a iya ganin abinda ke cikinta) wadda ta lulluɓe bangon fatar idanu na ciki da kuma dukkanin ƙwayar idanu in banda cornea (sashen ido dake da baƙi). Fatar conjunctiva fata ce mai ɗauke da ɗimbin al'ajabi, saboda duk da cewa ana iya ganin abinda ke cikinta da wajenta amma tana ɗauke da wasu jijiyoyin jini 'yan ƙanana waɗanda ba safai akan iya ganin su ba idan har fatar tana cikin ƙoshin lafiya. Waɗannan ƙananan jijiyoyin su ke da alhakin samar da jini zuwa ga tantanin halittun fatar conjunctiva.
KaÉ—an daga cikin amfanin fatar conjunctiva a idanu sun haÉ—a da;
1. Samar da wani sinadarin ruwa mai masƙi domin lausasa idanu
2. Taimakawa wajen samar da hawaye
3. Bada kariya ga idanu ta hanyar hana ƙwayoyin cuta shiga daga ciki kai tsaye.



Mene ne ciwon ido na Apollo?

Ciwon Apollo wani ciwo ne dake faruwa a lokacin da fatar conjunctiva ta shiga halin ƙaƙa-nikai sakamakon shigar wata ƙwayar cuta a cikin ta. Shigar ƙwayar cuta a cikin conjunctiva yakan sa fatar ta kumbura, ta fara ciwo kuma tayi jaa sannan ta kama fitar da kwantsa.
Idanu sukan yi jaa sosai a lokacin da mutum ya ke ciwon Apollo, wannan ya samu asali ne sakamakon kumburar jijiyoyin jini da ke cikin fatar conjunctiva. Jijiyoyin jinin fatar conjunctiva ba safai akan iya ganin su ba in dai har fatar tana cikin ƙoshin lafiya, amma idan ƙwayar cuta ta shafi fatar jijiyoyin sukan kumbura su fito fili sosai, wanda hakan ke sa jajayen idanu a cutar Apollo.




Me ke kawo ciwon ido na Apollo?

Kamar yadda muka yi bayani a baya cutar Apollo tana faruwa ne a lokacin da wani baƙon abu ko kuma ƙwayar cuta ta shiga fatar conjunctiva. Ƙwayoyin cutar da kan iya shiga fatar conjunctiva su haifar da ciwon Apollo sun haɗa da
1. Ƙwayoyin cutar bakteriya (Bacterial conjunctivitis)
  • Ƙwayar bakteriya Staphylococcus aureus
  • Ƙwayar bakteriya Streptococcus pneumoniae
  • Ƙwayar bakteriya Haemophilus influenzae
  • Ƙwayar bakteriya Moraxella catarrhalis
  • Ƙwayar bakteriya Moraxella lacunata
  • Ƙwayar bakteriya Neisseria gonorrhoeae
  • Ƙwayar bakteriya Chlamydia trachomatis
  • Da kuma Æ™wayar bakteriya Chlamydia pneumoniae
2. Ƙwayoyin cutar virus (Viral conjunctivitis)
  • Ƙwayoyin cutar virus na zuriyar Adenovirus (su ne suka fi yawan kawowa)
  • Ƙwayoyin cutar Herpes simplex virus
  • Ƙwayoyin cutar varicella zoster virus

3. Shigar wasu abubuwa a cikin idanu ( Allergic conjunctivitis)
Faɗawar wasu baƙin abubuwa a cikin idanu yakan iya haifar da ciwon ido, sai dai an fi danganta ciwon Apollo da ƙwayoyin cutar bakteriya ko virus. Haka kuma wannan ciwon da ya samo asali sanadiyyar faɗawar wasu baƙin abubuwa a cikin idanu baya yaɗuwa tsakanin mutane saɓanin ciwon Apollo wanda ya samu asali daga shigar wata ƙwayar cuta (bakteriya ko virus) a cikin idanu.
Baƙin abubuwan da kan iya shiga idanu har su haifar da ciwon ido sun haɗa da
  • Iska mai É—auke da Æ™ura.
  • HayaÆ™i
  • Ruwan sinadarai kamar acid ko alkali
  • Haki ko ciyawa
  • Ƙwari (Insects)
  • GurÉ“ataccin ruwa
  • Da dai sauransu



Alamomin ciwon ido na Apollo

1. Jajayen idanu
2. Fitar da wani ruwa mai É—auri daga idanu
3. Wahala wajen buÉ—e idanu idan mutum ya farka daga bacci
4. Ƙaiƙayin idanu
5. Yawan hawaye babu dalili
6. Rashin son haske
7. Gani bishi-bishi

A lura cewa, ba ciwon ido na Apollo kaÉ—ai kan iya kawo jajayen idanu ba, akwai cututtuka da dama dake kawo haka, saboda haka ya kamata mutum ya hanzarta ganin likita da zarar ya idanunsa sun canza kala.

Yadda cutar Apollo ke yaÉ—uwa tsakanin jama'a

A lura cewa akwai hanyoyi daban-daban da waɗannan ƙwayoyin cutar bakteriya da virus kan iya yaɗuwa a tsakanin mutane. Manyan hanyoyi yaɗuwar sun haɗa da:
  • TaÉ“a idanu da gurÉ“ataccin hannuwa
  • TaÉ“a hanci, kunnuwa ko baki da gurÉ“ataccin hannuwa
  • Wanke fuska da gurÉ“ataccin ruwa ko hannuwa
  • Gaisawa hannu da hannu da mai fama da cutar
  • Sumbatar baki da baki da mai fama da cutar
  • Ta hanyar jima'i
  • Ta hanyar haihuwa
  • Haka kuma akwai majiya ta musamman da ta tabbatar da yaÉ—uwar cutar Apollo ta hanyar iska.

Yadda ake maganin ciwon ido na Apollo.

Farko dai likita zai ɗauki muhimman bayanai game da ciwon idon da kuma yanda ya fara. Haka zalika, yana da kyau a tantance yadda ciwon ya samu asali saboda watarana akan samu ɓarkewar wannan ciwon a cikin al'umma da kuma yaɗuwar ta tamkar wutar daji. Ciwon ido wanda ya samo asali daga ƙwayar cutar bakteriya ko virus sune kan iya kawo ɓarkewar ciwon ido na Apollo a cikin al'umma.
Ba wasu gwaje-gwaje na musamman da ake yi domin tabbatar da ciwon idon na Apollo, amma idan ana buƙatar gane wace ƙwayar cuta ce keda alhakin kawo ciwon ana iya amfani da kwantsa (ruwa mai ɗauri wanda ke fita daga cikin idanu a lokacin da ciwon ya shafe su) sai aje ɗakin gwaje-gwaje na asibiti (laboratory) a auna domin gano ƙwayar cutar da ta kawo ciwon da kuma maganin da zai iya amfani wajen kashe ta.

Magungunan da ake amfani dasu domin warkewa daga cutar Apollo.

Zaɓin magungunan da ya kamata ayi amfani dasu wajen warkar da cutar Apollo ya danganta da musabbabin abinda ya kawo cutar. Ana amfani da magungunan antibiotics na ɗigawa a cikin idanu da kuma na sha a cutar Apollo wadda ƙwayar bakteriya ta kawo. Magungunan antibiotics da ake amfani dasu na ɗigawa a cikin idanu sun haɗa da;
  • Ofloxacin eye drops
  • Chloramphenicol eye drops
  • Gentamicin eye drops
  • Azithromycin eye drops
  • Bacitracin eye drops
  • Ciprofloxacin eye drops



Haka zalika bayan anyi amfani da magungunan ɗigawa a idanu za'a kuma iya yin amfani da magungunan antibiotics na sha domin kashe ƙwayoyin cutar bakteriya wadda ke cikin jini yadda ya kamata. Ana amfani da magungunan antibiotics masu faɗin aiki ko kuma maganin antibiotic wanda sakamakon gwaji ya tabbatar zai kashe ƙwayar bakteriya da ta kawo cutar.
Magungunan sha sun haÉ—a da
  • Ampiclox capsules
  • Augmentin caplet
  • Ciprofloxacin tablet
  • Levofloxacin tablet
  • Cefuroxime tablet
Idan har ciwon idon yasa idanu na ciwo sosai matuƙa, to ana so a bawa marar lafiya magungunan kashe ciwo ko na sha ko kuma na ɗigawa a idanu domin rage raɗaɗin ciwon ido, magungunan kashe ciwo da za'a iya amfani da su a idanu sun haɗa da
  • Diclofenac eye drops
  • Da kuma sauran maganganun kashe ciwo na sha.
Cutar Apollo wadda Æ™wayar virus ta kawo ba'a amfani da antibiotics ko antivirals. Har ila yau babu wani maganin É—igawa ko man shafawa da kai tsaye zai iya magance cutar Apollo wadda virus ya kawo. Kamar cutar mura na gama gari, kwayar cutar dole ne ta gudanar da aikinta, wanda zai iya É—aukar makonni biyu ko uku sannan ta warke da kanta. Amma duk da haka ana iya amfani da magungunan rage ciwo kamar Diclofenac eye drops domin rage raÉ—aÉ—in ciwon ido da kuma amfani da wasu anti-allergic eye drops (bayanin su zai zo jim kaÉ—an) domin rage wasu miyagun alamomin cutar. 

Shi kuma Allergic conjunctivitis, wanda babu alhakin wata ƙwayar cutar bakteriya ko virus a wajen samuwar sa, mafi akasari yana faruwa ne a lokacin da wasu baƙin abubuwa suka faɗa a idanu kamar yadda muka yi bayani a baya. Hanya ta farko ta maganin wannan ciwon ido ita ce fitar da abubuwan da suka faɗa a cikin idanu. Bayan an fitar, sai a samu ruwa mai sanyi kuma mai tsalki sosai (wanda bayada wasu ƙwayoyin cuta) sai a wanke idanu dashi. A asibiti ana amfani da sinadarin ruwan normal saline wajen wanke ido. Haka kuma akan iya yin gashi da ruwan sanyi. Akwai magungunan ɗigawa da za'a iya amfani dasu domin samun sauƙin miyagun alamomin allergic conjunctivitis, waɗannan magunguna sun haɗa da;
  • Anteallerge eye drops
  • Spersellerge eye drops
  • Kitotifen fumerate eye drops
  • Tears naturale eye drops
Haka zalika, shima akan iya yin amfani da magungunan kashe ciwo domin rage raÉ—aÉ—in ciwon idanu.

Yadda mutum zai kare kansa daga kamuwa da ciwon ido na Apollo.

Kamar yadda muka yi bayani a baya, cutar ciwon ido na Apollo wadda bakteriya da kuma virus suke kawowa tana da matuƙar saurin yaɗuwa tamkar wutar daji. Wannan shi yasa sau dayawa akan samu ɓarkewar cutar Apollo a cikin al'umma. Kiyaye waɗannan hanyoyi zai taimaka sosai wajen hana wannan cutar yaɗuwa ko a lokacin da aka samu ɓarkewar ta cikin al'umma.
1. Tsafta; wannan ya ƙunshi tsaftace jiki da kuma muhalli.
2. Kiyaye taɓa idanu da hannuwa
3. Yawan wanke hannuwa
4. Amfani da tabarau da kuma kula da tsaftace shi
5. Yin amfani da tabarau É—aya kacal kuma ba tare da arawa kowa ba
6. Rage shiga taron jama'a a lokacin da cutar ta É“arke.

Kammalawa

Cutar ciwon idon Apollo cuta ce dake samo asali a lokacin da fatar conjunctiva ta shiga halin ƙaƙanikayi sakamakon shigar ƙwayar cutar bakteriya ko virus ko wasu baƙin abubuwa a cikin ta. Cutar tana nuna alamomin da suka haɗa da jajayen idanu, kwantsa, ƙaiƙayi, yawan hawaye da dai sauran su. Haka kuma ana amfani da magungunan antibiotics na ɗigawa a idanu, anti-allergic eye drops da kuma magungunan rage raɗaɗin ciwo domin magance wannan cutar.

Idan kuna da tambaya sai kuyi a cikin akwatin sharhi dake Æ™asa, Insha Allah zamu karba ba tare da jinkiri ba. Haka kuma zaku iya shiga group dinmu na WhatsApp domin kasancewa damu damu a koda yaushe da kuma samun ingantattun bayanan mu a cikin sauki. Ku danna wannan domin shiga: Lafiyata Group 3. 

Post a Comment

0 Comments