Maganin Ciwon Ido: Cututtukan Fatar Idanu da Yadda ake Maganin su (Blepharitis, Chalazion, Stye or Hordeolum)

Gabatarwa:


Fatar idanu tana daga cikin fata marar kauri a jikin É—an adam. Fatar idanu duk da rashin kaurinta, tana É—auke da wasu abubuwa da suka Æ™unshi glands, karan gashi(hair follicles)  da kitse. Cututtukan fata r idanu su na daya daga ciki abubuwan da ke kawo ciwon ido.

Glands É—in da ake samu a fatar idanu ana kiran su meibomian glands, kuma sun kasu gida biyu, akwai glands da ke fitar da zufa (sweat glands) akwai kuma glands É—in da ke fitar da wani sinadari mai masÆ™i da ake kira sinadarin sebum. Amma kitsen da fatar idanu ke É—auke dashi bayada  yawa, wannan shi yasa fatar ta zama 'yar siririya.

Ƙwayar cututtuka sukan iya shafar wannan fatar da kuma glands ɗin da ke cikinta har su haifar da ƙuraje kamar yadda zamu gani a cikin wannan rubutu.



Ire-iren ƙurajen fatar idanu

1. Kumburin Blepharitis

Wannan kumburi ne da ke faruwa a lokacin da wata Æ™wayar cutar bakteriya ta shafi fatar idanu ko kuma a lokacin da glands É—in da ke fitar da zufa ko waÉ—anda ke fitar da sinadarin sebum suka toshe sakamakon shigar wata Æ™wayar cuta a cikin su. 

Blepharitis yakan sanya fatar idanu tayi kumburi da ciwo haka zalika idanu suyi jaa. Wannan shi ne mataki na farko a ciwon fatar idanu, wanda in ba'a ɗauki mataki da sauri ba yakan iya warkewa da kansa ko kuma ya chi gaba ya haifar da ƙurjin Stye (Hordeolum) ko ƙurjin Chalazion.



2. Ƙurjin Stye

Wani ƙaramin ƙurji ne da ke fitowa a bangon fatar idanu na ciki ko na waje. Wannan ƙurji ana kiran sa Stye ko kuma Hordeolum a turance.
Wannan Æ™urjin ya kasu gida biyu (2), akwai mai fitowa a bangon fatar idanu na ciki (Internal hordeolum) akwai kuma mai fitowa a bangon fatar idanu na waje (External hordeolum). 

Shi internal hordeolum yana faruwa ne a lokacin da dandazon ƙwayar bakteriya ya kawo toshewar glands masu fitar da sinadarin sebum a fatar idanu. Shi kuma External hordeolum yana faruwa ne a lokacin da dandazon ƙwayar bakteriya ya kawo toshewar gindin karan gashi (hair follicle).

Ƙurjin stye (hordeolum) yana somawa ne da kumburin blepharitis da kuma duk wasu alamomi da blepharitis yake nunawa irinsu ciwon ido, kumburi, Æ™aiÆ™ayi da jan idanu kamar yadda muka yi bayani a baya. 

Daga nan sai ya fitar da ƙurji mai azabar ciwo a bangon fatar idanu na ciki ko na waje. Ƙurjin yana iya yin wasu fararen ruwa masu kauri. Idan ba'ayi magani da sauri ba, ƙurjin Stye yakan iya warkewa da kansa ko kuma ya chi gaba zuwa ƙurjin Chalazion.




3. Ƙurjin Chalazion

Wannan Æ™urji yana somawa ne yayin da meibomian glands suka toshe ba tare da alhakin wata Æ™wayar cutar bakteriya ba. Haka kuma, Æ™urjin stye idan ya daÉ—e yakan iya komawa Æ™urjin chalazion. 

Chalazion yana fitowa a bangon fatar idanu na waje ko na ciki, watarana girman sa yakan mamaye bangon ciki da na waje. Chalazion yafi stye girma, haka kuma saɓanin stye chalazion bayada ciwo sosai.




A lura cewa, duk waÉ—annan Æ™uraje da muka ambata an fi samunsu a fatar idanu ta sama saboda fatar tafi yawan adadin meibomian glands. Amma duk da haka ana iya samun su a fatar idanu ta Æ™asa. 



Abubuwan da ke kawo ƙuraje a fatar idanu.

1. Rashin tsaftace idanu
2. Yawan pimples (ƙurajen fuska)
3. Infections (Wasu cututtuka)
4. Bushewar idanu
5. Dandruff (Kuraici)
6. Yawan cin maiƙo

Alamomin ƙuraje masu fitowa a fatar idanu

1. Ciwon ido: WaÉ—annan Æ™uraje masu fitowa a fatar idanu suna haifar da wasu alamomi a jikin mutum. Babbar alamar Æ™urjin stye ita ce ciwo a inda zai fito. Wannan Æ™urjin yana da matuÆ™ar ciwo sosai, wanda watarana shi ne abu na farko da zai fara jan hankalin marar lafiya zuwa neman magani duk da cewa kumburi da Æ™aiÆ™aiyi sukan riga ciwo a wani sa'ilin. 

Saɓanin kumburin blepharitis da ƙurjin stye shi ƙurjin chalazion bayada ciwo. Sauran alamomin da wadannan cututtukan ke nunawa sun haɗa da:

2. Kumburin idanu
3. Ƙaiƙayin idanu
4. Yawan hawaye
5. Idanu su zama jajaye
6. Yawan ƙyafta idanu
7. Rashin son haske
8. Rashin iya buÉ—e ido
9. Zazzaɓi ko zafin jiki.
10. Kwantsa

Yadda ake maganin ƙurajen fatar idanu.

Da farko dai likita zai ɗauki cikakken bayani akan yadda ƙurjin ya fara da yadda ya chi gaba. Mafi yawanci ba'a buƙatar wasu gwaje-gwaje na musamman kamin tabbatar da waɗannan ƙuraje. Likita zai duba marar lafiya akan gadon asibiti, kuma zai taɓa ƙurjin domin ƙara tabbatar da wane irin ƙurji marar lafiya yake dashi. Sannan likita zai baiwa marar lafiya hanyoyin magani kamar haka:

1. Gashi da ruwan zafi ko tuwon ƙasa

Anso idan É—aya daga cikin waÉ—annan Æ™uraje suka fitowa mutum ya samu ruwa masu É—imi da tsumma ya rinÆ™a sanya tsumman a cikin ruwan zafi sannan ya danna a inda Æ™urjin ya fito. 

Ko kuma mutum yayi tuwon ƙasa ya kama gasa ƙurjin dashi sannu a hankali. Anaso mutum yayi gashi kamar sau uku a rana. Wannan gashi da ruwan zafi ko tuwon ƙasa zai taimaka wajen buɗe ƙofofin glands din da suka toshe.

2. Amfani da magungunan antibiotics

Ana amfani da Æ™wayoyin maganin antibiotics domin kashe Æ™wayar bakteriya da ta kawo toshewar Æ™ofofin meibomian glands ko kuma karan gashi. Antibiotics É—in da ake son ayi amfani dasu sune antibiotics masu faÉ—in aiki kamar su; Augmentin tablet, ciprofloxacin tablet, cefuroxime, Ampiclox da dai sauransu. 

Haka kuma akwai antibiotics na É—igawa a idanu (eye drops) kamar irin su: Ofloxacin eye drop, Chloramphenicol eye drops, Gentamicin eye drops da dai sauransu.

3. Magungunan kashe ciwo

Kumburin blepharitis da kuma ƙurjin stye suna da matuƙar ciwo sosai, musamman ƙurjin stye. Domin rage wannan ciwon ana amfani da waɗannan magunguna kamar haka; Diclofenac tablet ko eye drops, Ceflonac tablet, Boscopan tablet, Cocodamol da dai sauransu.

4. Fasa ƙurji idan yayi ruwa

Ƙurjin stye ko ko chalazion sukan yi ruwa a cikinsu. Idan haka ta faru za'a iya ganin wani farin ruwa a saman ƙurjin. Wannan ruwan dole ne a fasa ƙurjin a matse shi har sai ƙurjin ya fitar da dukkan ruwan da ke cikin sa. Wannan ya zama wajibi idan anason ƙurjin yayi saurin warkewa. A lura cewa, ba ko wane ƙurji ake fasawa ba sai wanda aka tabbatar yanada fararen ruwa a cikin sa.

Ƙarin bayani; idan anason ƙurjin ya warke yadda ya kamata, to za'a yi amfani da duk waɗannan matakai da muka ambata a sama, watau za'a yi gashi da ruwan zafi ko tuwon ƙasa tare da amfani da magungunan ƙwayoyi na antibiotics da kuma na ɗigawa a idanu tare da amfani da magungunan kashe ciwo, haka kuma idan ƙurjin yana da ruwa a matse su.

4. Tiyata

Idan ƙurjin yaki ya ɓace ko ya warke har wani tsawon lokaci bayan duk an gama amfani da waɗannan matakai na sama toh za'a iya kaishi wajen likitoci masu ƙwarewa ta musamman a fannin idanu domin a cire shi ta hanyar aikin tiyata. Ƙurjin chalazion yafi yin haka.

Bayanin kammalawa

Idanu sassan jikin ɗan adam ne masu matuƙar muhimmanci wanda hakan ya wajabta kula da tsaftace su domin gujewa cututtukan da kan iya shafuwar su. Ƙurajen da ke fitowa a fatar idanu basu cika haifar da makanta ba sai dai suna damuwar mutane saboda ciwo da kuma dalilin ado (cosmesis).

Idan kuna da tambaya sai kuyi a cikin akwatin sharhi dake Æ™asa, Insha Allah zamu karba ba tare da jinkiri ba. Haka kuma zaku iya shiga group dinmu na WhatsApp domin kasancewa damu damu a koda yaushe da kuma samun ingantattun bayanan mu a cikin sauki. Ku danna wannan domin shiga: Lafiyata Group 3.