Ad Code

Ticker

6/recent/ticker-posts

Wane ne zai iya yin fassarar ayoyin Alkur'ani? Bayanin Sheikh Imam Al-Nawawi

Gabatarwa:

Haramun ne ga wani ya fassara Alqur'ani ba tare da ilimi ba, da kuma cancantar yin magana a kan ma'anoninsa ba. Hadisai da suka yi magana a kan haka suna da yawa, ya dace malamai ne kawai za su bayyana fassarar ayoyin Alqur'ani, kuma anyi ijma'i akan hakan. 

Wanda ya cancanta ya bayyana ma'anonin Alqur'ani, shi ne wanda ya tattara dukkan kayan aikin da ake buƙata domin fassara ma'anonin littafin Allah [Alqur'ani]. Wannan shi ne mutumin da ya samu ingantaccen ilimin tafsiri ta hanyar karatu sau da ƙafa a wurin malaman tafsiri, wannan shi ne zai iya bayyana ma'anonin Alqur'ani, musamman abubuwan da suke bayyane a gare shi, hakika zai iya bayyana su. Haka kuma idan wani abu ne da ake samu ta hanyar tunani mai zaman kansa [ijtihadi] toh zai iya yin ijtihadi. Amma idan wani abu ne wanda ba a samu ta hanyar tunani mai zaman kansa, sai ta hanyar watsa [tunanin magabata], baya halatta mutum ya sadar da wannan sai ta hanyar ingantattun ƙwararrun masana. 

Shi kuma wanda bai cancanta yayi fassara ba saboda rashin samun cikakken ingantacccen ilimin yin haka, haramun ne a gare shi ya ba da fassara da kansa ko yayi ijtihadi. Sai dai yana iya watsa fassara da bayanai daga ƙwararrun masana.


 Amfani da ra'ayi ba tare da hujja ba

 Masu bayyana ra'ayoyinsu ba tare da ingantacciyar hujja ba ana iya karkasa su kamar haka:

 (1). Wanda ya yi amfani da aya don tabbatar da ingancin mazhabarsa ta musamman da kuma karfafa tunaninsa, duk da cewa a cikin zuciyarsa ya san cewa ayar bata tabbatar da ra'ayinsa, amma duk da haka ya dage yana neman kawai ya yi nasara a kan abokin muhawararsa.

 (2). Wanda ya yi nufin yin kira zuwa ga alheri, amma ya yi amfani da aya don tabbatar da matsayinsa ba tare da ma'anar [ayar] ta bayyana a gare shi da gaske ba.

 (3). Wanda ya fassara jimlolin larabci na [Alqur'ani] ba tare da sanin ma'anarsu ba kamar yadda ƙwararrun malaman tafsiri suka fassara ba, alhali jimlolin Al'qurani wasu abu ne da ba za a iya ɗauka ta hanyar ƙwararrun malaman larabci da tawili kaɗai ba.

 Ilimin Larabci kaɗai baya wadatarwa ga mai fassara Alkur'ani

 Sanin ilmin larabci kaɗai baya wadatarwa ga mai fassara littafin Allah, maimakon haka, dole ne a san duk abin da ƙwararrun malaman tafsiri suka faɗa game da [wani nassin Alƙur'ani], domin malaman tafsiri suna iya yin ijma'i akan cewa ma'anar wata aya, ba fassarar zahirin abinda take nufi da larabci ba ne. Haka nan idan wata jimla ta Alkur'ani tana da ma’anoni daban-daban kuma an san cewa ɗaya daga cikin waɗannan ma'anonin ake nufi, malamai masana tafsiri za su taru suyi ijma'i akan wace ma'ana ce ake amfani da ita domin fassara ayar.

 Duk abin da ya gabata yana nuna mana bayar da bayani ta hanyar ra'ayi ko kuma yin fassarar ayoyin Alƙur'ani da molon kai ba abu ne da ya halatta ba, kuma wannan haramun ne. Allah shi ne Mafi sani.

Muhawara ko jayayya ba tare da hujja ba

 Haramun ne a yi jayayya da muhawara a kan ayoyin Alkur’ani ba tare da hakki ba, kamar  mutumin da yake da wata fassara akan wata aya, duk da cewa yasan akwai yiwuwar ayar ta tafi sabanin ra’ayinsa, kuma tana da raunin yiwuwar haduwa da shi, amma duk da haka ya kasance akan ra'ayinsa.  Hasali ma, shi [ya dage] a kan yin muhawara duk da cewa ya bayyana a gare shi cewa abin ya saba wa ra’ayinsa.  (Amma idan hakan bai bayyana a gare shi ba, to an yi masa uzuri).

Ya tabbata cewa Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya ce: “Yin jayayya a kan Alqur’ani kafirci ne.” [2] Al-Khaṭṭābī ya ce: “Abin da ake nufi da jayayya a nan shi ne ‘shakka’.  Ra'ayoyin wasu kuma sun bayyana cewa 'ƙalubalanta' ko kuma yin jayayya akan ayoyin da suka yi magana a kan kaddara da makamantansu.

 Tambaya Akan Hikimar Aya

 Wani wanda yake so ya yi tambaya—me ya sa, alal misali, wata aya ta gabaci wata ko kuma dacewa da aya a cikin wani takamaiman yanayi—ya halatta ya ce, “Mene ne hikimar wannan?”

Kammalawa

An cirato wannan bayani ne daga littafin Al-Tibyān fī Ādāb Ḥamalat al-Qurʾān.
Print this post

Post a Comment

0 Comments