Doro ko ƙusumbi lalurorin ƙashin baya ne da za'a iya magance su tun da wuri.
Doro lalurar ƙashin baya ce da ke sauya surar ƙashin bayan, wanda idan ba a magance ta ba za ta iya zama ƙusumbi idan abu yayi nisa.
Yadda doro ke sauya surar jiki, haka yake sauya gurbin wuya, kafaɗu da kuma kai a jiki. Maza da mata, yara da manya, a kowane shekaru ana iya samun doro ko ƙusumbi.
Doro na faruwa ne yayin da ƙashin baya da ke fuskantar ƙirji ya lankwasa ta baya fiye da ƙim. Hakan shi ke haifar da doro tare da sauyawar daidaituwar tsayuwar jiki.
Bayan bayyanar doro wanda ke iya sanya mutum cikin baƙin ciki da damuwa kan sauyin surar jiki, ƙarin matsalolin da kan iya biyowa baya sun haɗa da: ciwon wuya, ciwon kafaɗu da wahalar numfashi.
Matsalolin da ke karawa mutum haÉ—arin samun doro sun haÉ—a da:
- Salon zama, tsayuwa, tafiya, ko kuma ayyukan sana'o'i dake buƙatar yawan tsuguno ko lankwasa wuya da ƙashin baya.
- Masana sun tabbatar da cewa yawan amfani da wayar salula ko duk wata na'ura mai ƙwaƙwalwa a zaune na tsawon lokaci yana taimakawa wajen samun lalurar doro.
- Tawayar ƙashin baya da ake haihuwar mutum da ita.
- Rauni ko rashin kwarin tsokokin baya da ke riƙe da kashin baya.
- Lalurar zaizayewar ƙashin baya (spondylosis).
- Lalurar sanƙarewar kashin baya.
- Lahani ko rauni ga ƙashin baya kamar haɗarin mota, faɗuwa daga itaciya akan ƙashin baya, bugu da dai sauransu.
Idan ba a shawo kan lalurar doro da sauri ba toh tana iya zarcewa zuwa lalurar ƙusumbi.
Likitan fisiyo na taimakawa mai doro ko ƙusumbi wajen shawo kan lalurar tun da wuri domin dawo da lanƙwasar ƙashin bayan zuwa daidai.
Idan lalurar doro ta zama ƙusumbi, tiyata na iya zama dole domin gyara ƙashin bayan.
Idan kana da doro kuma kana damuwa kan surar jikin ka, ko kuma akwai ƙorafin ciwon wuya ko ciwon kafaɗa, tuntuɓi likitan fisiyo domin neman agajin gaggawa.
0 Comments