Meke Kawo Ciwon Baya Bayan Aikin Tiyatar Cire Jariri CS

Maganin ciwon baya


Caesarian section ko kuma "CS" a turance, aikin tiyata ne da ake yi domin cire jariri daga cikin mahaifa ta hanyar yanka cikin uwa da mahaifa kai tsaye a lokacin da jariri ya kai mizanin da zai iya rayuwa a cikin duniya waje da mahaifa.

Mafi akasari, ana yin aikin tiyatar CS ne idan aka samu tangarɗar nakuda ko kuma idan an lura mace ba ta iya haihuwa da kanta ko kuma bisa zaɓin mace wadda ba ta so tayi haihuwa ta gaban ta ko akan wasu dalilai.

Sai dai kuma, yawan ciwon baya bayan aikin tiyatar CS na daga cikin ƙorafe-ƙorafen da ke biyo bayan anyi aikin CS an kammala cikin nasara har mace ta fara warke.

Maganin ciwon baya

Daga cikin dalilan da ke kawo ciwon baya bayan aikin tiyatar CS shi ne idan an yi wa mace allurar kashe jiki a gadon bayan ta (spinal anesthesia). Irin wannan allurar kashe jiki ita ce ake yiwa mace domin kashe jin ciwo ko duk wani jin taɓi daga cibiya har zuwa ƙafafu.

Saɓanin allurar kashe jiki ta sha-ka-leme, idan anyi wa mace irin wannan allurar ba za ta samu gushewa

Daga cikin dalilan samun ciwon baya bayan aikin tiyatar CS na da alaƙa da yanka tsokokin bangon ciki da ake yi a lokacin tiyatar, waɗanda rukunin tsokoki ne da ke tallafa wa gadon baya ya zauna lami-lafiya.

Saboda haka, bayan aikin tiyatar CS, tsokokin bangon ciki suna samun Æ™aramin rauni, don haka tsarin taimakekeniya da ke tsakanin tsokokin gadon baya da tsokokin bangon ciki zai samu tangarÉ—a. 

Bugu da ƙari, riƙewa, ɗagawa ko goya abu mai nauyi na iya ƙara haɗarin samun ciwon gadon bayan da kuma yin barazana ga ɗinkin da aka yiwa bangon mahaifa bayan cire jariri.

Haka kuma mace na iya samun ciwon baya bayan an yi mata aikin tiyatar CS ta dalilin yadda take daukar jariri a hannun, ko yadda take shayarwa. Ba'a daukar jariri tare da bada dukkan nauyin sa akan ƙugun macen da aka yiwa aikin tiyatar CS. Wannan ma ya kan iya kawo ciwon gadon baya.

Yadda ake daukar jariri

Bincike ya nuna matan da aka yiwa aikin tiyatar cire jariri daga mahaifa kuma suka samu kulawar likitan fisiyo bayan warkewa daga tiyatar sun fi samun raguwar ciwon baya a kan waÉ—anda ba su samu kulawar likitan fisiyo ba.

Likitan fisiyo na taka muhimmiyar rawar gani bayan tiyatar ciro jariri ta hanyar ƙarfafa tsokokin bangon ciki, maganin ciwon baya, ciwon ƙugu, koyar da lafiyayyun hanyoyin riƙe jariri, ɗaga jariri sama, goya jariri domin kiyaye buɗewar tiyatar da kuma sauƙaƙa ko kiyaye ciwon baya.

Idan kina fama da ciwon baya bayan an miki aikin tiyatar cire jariri, tuntuɓi likitan fisiyo a yau domin fara bankwana da ciwon baya ba tare da dogaro da shan maganin rage ciwo kullum ba.

Nassoshi 

1. Physiotherapy Hausa
2. Obgyn Magazine 

Post a Comment

0 Comments